Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Church (2): Love for

18 ayoyi · 7 fannoni

Ayoyi game da Love for

  1. Bari Ubangiji ya albarkace ka daga Sihiyona dukan kwanakin ranka; bari ka ga wadatar Urushalima,

  2. bari kuma ka rayu ka ga ’ya’ya ’ya’yanka. Salama tă kasance tare da Isra’ila.

  3. A bakin kogunan Babilon muka zauna muka yi kuka sa’ad da muka tuna da Sihiyona.

  4. A can a kan rassan itatuwa muka rataye garayunmu,

  5. gama a can masu kamunmu suka sa mu yi waƙoƙi, masu ba mu azaba suka nema waƙoƙin farin ciki; suka ce, “Ku rera mana ɗaya daga cikin waƙoƙin Sihiyona!”

  6. Yaya za mu rera waƙoƙin Ubangiji a baƙuwar ƙasa?

  7. In na manta da ke, ya Urushalima, bari hannuna na dama manta da iyawarsa.

  8. Bari harshena yă manne wa rufin bakina in ban tuna da ke ba, in ban so Urushalima farin cikin mafi girma ba.

  9. Na sa matsara a kan katangarki, ya Urushalima; ba za su taɓa yin shiru ba, dare da rana. Ku da kuke kira bisa sunan Ubangiji, kada ku ba kanku hutu,

  10. kuma kada ku ba shi hutu sai ya kafa Urushalima ya kuma mai da ita yabon duniya.

  11. Kamar yadda uwa takan ta’azantar da ɗanta haka zan ta’azantar da ku; za ku kuma ta’azantu a Urushalima.”

  12. Sa’ad da kuka ga wannan, zuciyarku za tă yi farin ciki za ku kuma haɓaka kamar ciyawa; za a sanar da hannun Ubangiji ga bayinsa, amma za a nuna wa maƙiyansa fushinsa.

  13. Ku waɗanda kuka tsere wa takobi, ku gudu kada ku tsaya! Ku tuna da Ubangiji a ƙasa mai nesa, ku kuma yi ta tunani a kan Urushalima.”

  14. “Mun sha kunya saboda zargin da ake yi mana kunya ta rufe mu, domin baƙi sun shiga tsarkakan wurare na gidan Ubangiji.”

  15. Hawaye na kwararowa daga idanuna domin an hallaka mutanena.

  16. Idanuna za su ci gaba da kwararowa da hawaye, ba hutawa.

  17. Har sai in Ubangiji ya duba daga sama ya gani.

  18. Abin da nake gani yana kawo mini baƙin ciki domin dukan matan birnina.