- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Church (2)
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
Duba, Ubangiji Mai Iko Duka yana zuwa da iko, hannunsa kuma yana yin mulki dominsa. Duba, ladarsa tana tare da shi, sakamakonsa kuma na rakiyarsa.
Yakan lura da garkensa kamar makiyayi. Yakan tattara tumaki wuri ɗaya yă riƙe su kurkusa da ƙirjinsa; a hankali kuma yakan bi da masu ba da mama.
To, fa, ga abin da Ubangiji yana cewa, shi da ya halicce ka, ya Yaƙub, shi da ya siffanta ka, ya Isra’ila, “Kada ka ji tsoro, gama na fanshe ka; na kira ka da suna; kai nawa ne.
Sa’ad da kuka bi ta ruwaye, zan kasance tare da ku; sa’ad da kuka bi ta koguna, ba za su kwashe ku ba. Sa’ad da kuke tafiyata cikin wuta, ba za tă ƙone ku ba; harsunan wutar ba za su ƙone ku ba.
Gama ni ne Ubangiji, Allahnku, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, Mai Cetonku; na bayar da Masar don fansa, Kush da Seba a maimakonku.
Da yake ku masu daraja da kuma girma ne a idona, saboda kuma ina ƙaunarku, zan ba da mutane a maimakonku, al’umma kuma domin ranku.
Kada ku ji tsoro, gama ina tare da ku; zan kawo yaranku daga gabas in kuma tattara ku daga yamma.
Zan ce wa arewa, ‘Ku miƙa su!’ Ga kudu kuma, ‘Kada ku riƙe su.’ Kawo ’ya’yana maza daga nesa ’ya’yana mata kuma daga iyakar duniya,
kowa da ake kira da sunana, wanda aka halitta saboda ɗaukakata, wanda na siffanta na kuma yi.”
Amma Sihiyona ta ce, “Ubangiji ya yashe ni, Ubangiji ya manta da ni.”
“Yana yiwuwa mahaifiya ta manta da jariri a ƙirjinta ta kuma kāsa nuna tausayi ga yaron da ta haifa? Mai yiwuwa ta manta, amma ba zan taɓa manta da ke ba!
Duba, na zāna ki a tafin hannuwana; katangarki kullum suna a gabana.
’Ya’yanki maza su komo da gaggawa, waɗanda suka lalatar da ke kuwa za su bar ki.
Ki farka, ki farka, ya Sihiyona, ki sanya wa kanki ƙarfi. Ki sa rigarki na daraja, Ya Urushalima, birni mai tsarki. Marasa kaciya da maƙazanta ba za su shi cikinki ba.
Ki kakkaɓe ƙurarki; ki tashi, ki zauna a kursiyinki, ya Urushalima. Ki ’yantar da kanki daga sarƙoƙi a wuyanki, Ke kamammiyar Diyar Sihiyona.
Me ya fi wannan kyau a kan duwatsu a ga ƙafafu na masu kawo labari mai daɗi waɗanda suke shelar salama, waɗanda suke kawo labari mai daɗi, waɗanda suke shelar ceto, waɗanda suke ce wa Sihiyona, “Allahnki yana mulki!”
Ki kasa kunne! Masu tsaronki sun tā da muryoyinsu; tare sun yi sowa ta farin ciki. Sa’ad da Ubangiji ya komo Sihiyona, za su gan shi da idanunsu.
Ku ɓarke cikin waƙoƙin farin ciki gaba ɗaya, kangonki na Urushalima, gama Ubangiji ya ta’azantar da mutanensa, ya fanshi Urushalima.
Ubangiji zai nuna hannunsa mai tsarki a fili a idanun dukan al’ummai, da kuma dukan iyakokin duniya za su gani ceton Allahnmu.
Ku fita, ku fita daga can! Kada ku taɓa wani abu marar tsarki! Ku fita daga cikinta ku zama da tsarki, ku da kuke ɗaukan kayan aikin Ubangiji.
Amma ba za ku fita a gaggauce ba ko ku tafi da gudu; gama Ubangiji zai ja gabanku, Allah na Isra’ila zai kasance mai tsaron bayanku.
“Ki tashi, ki haskaka, gama haskenki ya zo, ɗaukakar Ubangiji ya taso a kanki.
Duba, duhu ya rufe duniya duhu mai kauri kuma yana bisa mutane, amma Ubangiji ya taso a kanki ɗaukakarsa kuma ya bayyana a bisanki.
Al’ummai za su zo wurin haskenki, sarakuna kuma zuwa asubahin sabon yininki.
“Ki ɗaga idanunki ki duba kewaye da ke. Duka sun tattaru suka kuma zo wurinki; ’ya’yanki maza daga nesa, ana kuma ɗaukan ’ya’yanki mata a hannu.