Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Children

257 ayoyi · 102 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Amma Yesu ya ce, “Wani ya taɓa ni, na san cewa iko ya fita daga wurina.”

  2. Sai macen, da ta ga ba halin ɓoyewa, sai ta fita, jikinta na rawa, ta fāɗi a gabansa. A gaban dukan mutanen, ta faɗi dalilin da ya sa ta taɓa shi, da yadda ta warke nan take.

  3. Sai Yesu ya ce mata, “Diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya.”

  4. Yayinda Yesu na cikin magana har yanzu, sai ga wani daga gidan Yayirus, mai mulkin majami’ar ya ce, “Kada ka ƙara damun malam, diyarka ta rasu.”

  5. Da Yesu ya ji wannan, sai ya ce wa Yayirus, “Kada ka ji tsoro, ka gaskata, za a kuma warkar da ita.”

  6. Da ya iso gidan Yayirus, sai ya hana kowa yă bi shi cikin ɗakin, sai dai Bitrus, da Yohanna, da Yaƙub, da kuma mahaifin da mahaifiyar.

  7. Ana cikin haka, dukan mutanen kuma sai kuka da makoki suke ta yi, domin yarinyar. Sai Yesu ya ce, “Ka daina yin kuka, ba tă mutu ba, tana barci ne.”

  8. Sai suka yi masa dariya, da yake sun san cewa, ta mutu.

  9. Amma Yesu ya kama ta a hannu ya ce, “Diyata, tashi.”

  10. Ruhunta ya dawo, kuma ta tashi, nan take. Yesu ya ce musu, su ba ta wani abu tă ci.

  11. Iyayenta suka yi mamaki, amma ya ba su umarni kada su faɗa wa kowa abin da ya faru.

  12. Sai wani mutum daga cikin taron ya yi kira da ƙarfi ya ce, “Malam, ina roƙonka, ka dubi ɗan nan nawa, gama shi ne kaɗai nake da shi.

  13. Wani ruhu yakan kama shi, sai ya yi ihu farar ɗaya. Yakan sa shi farfaɗiya, har bakinsa ya yi kumfa. Da ƙyar yake barinsa, yana kuwa kan hallakar da shi.

  14. Na roƙi almajiranka su fitar da shi, amma ba su iya ba.”

  15. Yesu ya amsa ya ce, “Ya karkataccen zamani marar bangaskiya, har yaushe ne zan kasance tare da ku, ina kuma haƙuri da ku? Kawo yaronka nan.”

  16. Yaron yana kan zuwa ke nan, sai aljanin ya buga shi ƙasa, cikin farfaɗiya. Amma Yesu ya kwaɓe mugun ruhun, ya warkar da yaron, sai ya miƙa shi ga mahaifinsa.

  17. Wata gardama ta tashi a tsakanin almajiran, a kan ko wane ne a cikinsu zai zama mafi girma

  18. Da yake Yesu ya san tunaninsu, sai ya ɗauki wani ƙaramin yaro, ya sa ya tsaya kusa da shi.

  19. Sai ya ce musu, “Duk wanda ya karɓi wannan ƙaramin yaron a cikin sunana, ni ya karɓa, kuma duk wanda ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ne. Gama mafi ƙanƙanta duka a cikinku, shi ne kuma mafi girma.”

  20. Mutane suna kawo jarirai wurin Yesu don yă taɓa su. Da almajiransa suka ga haka, sai suka kwaɓe su.

  21. Amma Yesu ya kira yaran a wurinsa ya ce, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina. Kada ku hana su, gama mulkin Allah na irin waɗannan ne.

  22. Sai ya sāke ziyarci Kana ta Galili inda ya juya ruwa ya zama ruwan inabi. Akwai wani ma’aikacin hukuma a can wanda ɗansa yake kwance da rashin lafiya a Kafarnahum.

  23. Da mutumin nan ya ji cewa Yesu ya isa Galili daga Yahudiya, sai ya je wurinsa ya roƙe shi yă zo yă warkar da ɗansa da yake bakin mutuwa.

  24. Yesu ya ce masa, “Ku mutane, in ba kun ga alamu da abubuwan banmamaki ba, ba yadda za a yi ku ba da gaskiya.”

  25. Ma’aikacin hukuman ya ce, “Ranka yă daɗe, ka zo kafin ɗana yă mutu.”