Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Alliance and Society with the Enemies of God

229 ayoyi · 51 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ban da haka, a waɗannan kwanakin na ga mutanen Yahuda waɗanda suka auri mata daga Ashdod, Ammon da Mowab.

  2. Rabin ’ya’yansu suna yaren Ashdod ko kuwa wani yare na waɗansu mutane, ba su kuwa san yadda za su yi Yahudanci ba.

  3. Na tsawata musu na kuma kira la’ana a kansu. Na bugi waɗansu mutane na kuma ja gashin kansu. Na sa suka yi rantsuwa da sunan Allah na ce, “Kada ku ba da ’ya’yanku mata aure ga ’ya’yansu maza, ba kuwa za ku auri ’ya’yansu mata wa ’ya’yanku maza ko wa kanku ba.

  4. Ba don aure-aure irin waɗannan ne Solomon sarkin Isra’ila ya yi zunubi ba? A cikin yawancin al’ummai babu sarki kamar sa. Allahnsa ya ƙaunace shi, Allah kuma ya mai da shi sarki a kan dukan Isra’ila, amma duk da haka baren mata suka rinjaye shi ga zunubi.

  5. Yanzu za mu ji cewa ku ma kuna yin duk wannan mugunta kuna zama marasa aminci ga Allahnmu ta wurin auren baren mata?”

  6. Mai farin ciki ne mutumin da ba ya aiki da shawarar mugaye ko yă yi abin da masu zunubi suke yi ko yă zauna tare da masu yin ba’a.

  7. Ku tafi daga gare ni, dukanku masu aikata mugunta, gama Ubangiji ya ji kukata.

  8. wanda yake ƙin mugun mutum amma yakan girmama masu tsoron Ubangiji, yakan cika alkawarinsa ko da ma ya zafe shi,

  9. Ba na zama tare da masu ruɗu, ko in yi tarayya da masu riya;

  10. na ƙi jinin taron masu aikata mugunta na ƙi in zauna tare da mugaye.

  11. Na ƙi waɗanda suke manne wa gumakan banza; na dogara ga Ubangiji.

  12. Sa’ad da kuka ga ɓarawo, kukan haɗa kai da shi; kukan haɗa kai da mazinata.

  13. Ina tsakiyar zakoki; ina kwance a cikin namun jeji masu cin mutane, mutanen da haƙoransu masu ne da kuma kibiyoyi, waɗanda harshensu suna da kaifi kamar takobi.

  14. Mutane masu mugun zuciya za su nesa da ni; ba abin da zai haɗa ni da mugunta.

  15. Duk wanda ya yi ɓatanci wa maƙwabcinsa a ɓoye shi za a kashe; duk mai renin wayo da mai girman kai, ba zan jure masa ba.

  16. Idanuna za su kasance a kan amintattu a cikin ƙasar, don su zauna tare da ni; tafiyarsa ba ta da zargi zai yi mini hidima.

  17. Babu mai ruɗun da zai zauna a gidana; babu mai ƙaryan da zai tsaya a gabana.

  18. suka tsokane Ubangiji ya yi fushi ta wurin mugayen ayyukansu, sai annoba ta ɓarke a cikinsu.

  19. Suka yi wa gumakansu sujada, waɗanda suka zama tarko gare su.

  20. Suka miƙa ’ya’yansu maza hadaya ’yan matansu kuma ga aljanu.

  21. Suka zub da jini marar laifi, jinin ’ya’yansu maza da mata, waɗanda suka miƙa hadaya ga gumakan Kan’ana, ƙasar kuwa ta ƙazantu ta wurin jininsu.

  22. Saboda haka Ubangiji ya yi fushi da mutanensa ya ji ƙyamar gādonsa.

  23. Ya miƙa su ga al’ummai, maƙiyansu kuma suka yi mulki a kansu.

  24. Abokan gābansu suka danne su suka sa su a ƙarƙashin ikonsu.

  25. Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta, don in kiyaye umarnan Allahna!