Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Alliance and Society with the Enemies of God: Lead to idolatry
Ayoyi game da Lead to idolatry
“Ku kula, kada ku yi yarjejjeniya da mazaunan wannan ƙasa, don kada sa’ad da suke yi wa allolinsu sujada, suna miƙa musu hadaya, su gayyace ku, ku ci hadayar da suka miƙa wa allolinsu.
Kada ku auro wa ’ya’yanku maza ’yan matansu, waɗanda suke yi wa alloli sujada, har su sa ’ya’yanku su bi allolinsu.
Lokacin da Isra’ila suke a sansani a Shittim, sai maza suka fara yin lalata da matan Mowabawa,
waɗanda suka gayyace su zuwa wajen hadayu na allolinsu. Mutane suka ci suka kuma yi wa waɗannan alloli sujada.
Ta haka Isra’ila suka sa kai a bautar gumaka Ba’al-Feyor. Ubangiji kuwa ya husata da su.
Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka kama dukan shugabannin mutanen nan, ka kashe su, ka kuma bar su a tsakar rana a gaban Ubangiji, don Ubangiji yă huce daga fushin da nake yi da Isra’ila.”
Saboda haka Musa ya ce wa alƙalan Isra’ila, “Dole kowannenku yă kashe mutanen nan da suka haɗa kai cikin bautar Ba’al-Feyor.”
Sa’an nan wani mutumin Isra’ila ya kawo wata Bamidiyana a iyalinsa a idon Musa da dukan taron jama’ar Isra’ila, yayinda suke kuka a ƙofar Tentin Sujada.
Da Finehas ɗan Eleyazar, ɗan Haruna, firist, ya ga haka, sai ya bar taron, ya ɗauki māshi
ya bi mutumin Isra’ilan nan cikin tenti, ya soke dukansu biyu, māshin ya ratsa jikin mutumin Isra’ilan har zuwa jikin macen. Sa’an nan aka tsai da annoban nan a kan Isra’ilawa.
Gama za su juye ’ya’yanku maza daga bina, su bauta waɗansu alloli, fushin Ubangiji kuma zai ƙuna a kanku da sauri, zai kuma hallaka ku.
Isra’ilawa suka zauna tare da Kan’aniyawa da Hittiyawa, Amoriyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da kuma Yebusiyawa.
Suka auri ’ya’yansu mata, su ma suka bar ’ya’yansu maza suka auri ’ya’yansu mata, suka kuma yi wa gumakansu sujada.
Isra’ilawa suka aikata mugunta a gaban Ubangiji; suka manta da Ubangiji Allahnsu suka kuma bauta wa Ba’al da Ashera.
Duk da haka, ina da wannan game da kai. Kana haƙuri da matan nan Yezebel, wadda take kira kanta annabiya. Ta wurin koyarwarta tana ɓad da bayina ga yin fasikanci suka kuma ci abincin da aka miƙa wa gumaka.