Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Alliance and Society with the Enemies of God: Forbidden

17 ayoyi · 51 fannoni

Ayoyi game da Forbidden

  1. Kada ku ƙulla yarjejjeniya da su, ko da allolinsu.

  2. Ku kula, kada ku yi yarjejjeniya da waɗanda suke zaune a ƙasar da za ku tafi, in ba haka ba, za su zama muku tarko.

  3. Sa’ad da kuma Ubangiji Allahnku ya ba da su gare ku, kuka kuma ci su da yaƙi, sai ku hallaka su ƙaƙaf. Kada ku yi yarjejjeniya da su, kada kuma ku nuna musu jinƙai.

  4. Kada ku yi auratayya da su. Kada ku ba da ’ya’yanku mata wa ’ya’yansu maza, ko ku ɗauko ’ya’yansu mata wa ’ya’yanku maza.

  5. In ɗan’uwanka, ko ɗanka, ko ’yarka, ko matar da kake ƙauna, ko abokinka na kusa, a ɓoye ya ruɗe ka, yana cewa, “Mu je mu yi wa waɗansu alloli sujada” (allolin da ko kai, ko kakanninka ba su sani ba,

  6. kada ka yarda da shi, kada ma ka saurare shi. Kada ka ji tausayinsa. Kada ka haƙura da shi, ko ka tsare shi.

  7. “Ku yi ƙarfin hali, ku yi hankali, ku yi biyayya da dukan abin da aka rubuta a cikin Littafin Dokoki na Musa, ba tare da kun juya hagu ko dama ba.

  8. Kada ku haɗa kai da mutanen nan da suke zama cikinku; ba ruwanku da sunayen allolinsu, kada ku rantse da su. Kada kuwa ku bauta musu ko kuwa ku rusuna musu.

  9. ku kuma kada ku shiga wata yarjejjeniya da mazaunan ƙasan nan, sai dai za ku rurrushe bagadansu.’ Duk da haka ba ku yi biyayya mini ba. Me ya sa kuka yi haka?

  10. Saboda haka kada ku aurar musu da ’yan matanku, kada kuma ku auro wa ’ya’yanku maza ’yan matansu. Kada ku yi wata yarjejjeniya ta abokantaka da su. Idan kun yi biyayya za ku yi ƙarfi, ku kuma ci albarkar ƙasar, har ku bar wa ’ya’yanku gādo na har abada.’

  11. Ɗana, in masu zunubi sun jarabce ka, kada ka yarda.

  12. ɗana, kada ka tafi tare da su, kada ka taka ƙafarka a hanyarsu;

  13. Kada ku haɗa kai da marasa bi. Gama me ya haɗa adalci da mugunta? Ko kuwa me ya haɗa haske da duhu?

  14. Wace daidaituwa ce tsakanin Kiristi da Iblis? Me ya haɗa mai bi da marar bi?

  15. Wane alkawari ne tsakanin haikalin Allah da na gumaka? Gama mu haikalin Allah mai rai ne. Kamar yadda Allah ya ce, “Zan zauna tare da su, in yi tafiya a cikinsu, zan zama Allahnsu, su kuma za su zama mutanena.”

  16. Saboda haka, “Sai ku fito daga cikinsu, ku keɓe kanku, in ji Ubangiji. Kada ku taɓa wani abu marar tsabta, zan kuma karɓe ku.”

  17. Ku yi nesa da ayyukan duhun da mutane suke yi, a maimakon haka, ku tona su.