Skip to content

Ashdod

18 verses · 2 known names

An kuma san shi da: Ashdothites

31.8000, 34.6300 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Ashdod

  1. Ba a bar waɗansu Anakawa a harabar Isra’ila ba; sai dai a Gaza, Gat da Ashdod ne aka samu waɗanda suka ragu da rai.

  2. Daga Kogin Shihor a gabashin Masar zuwa sashen Ekron a arewa, dukan wannan ƙasa ana lissafta ta a cikin ƙasar Kan’aniyawa, ko da yake tana a sashen da sarakuna biyar na Filistiyawa na Gaza, Ashdod, Ashkeloniyawa, Gat da Ekron; na Awwiyawa.

  3. yammancin Ekron da dukan garuruwa da ƙauyukan da suke kusa da Ashdod.

  4. Ashdod da garuruwa da kuma ƙauyukan da suke kewaye da ita, Gaza da garuruwanta da ƙauyukanta har zuwa Rafin Masar da kuma Bahar Rum.

  5. Bayan Filistiyawa sun ƙwace akwatin alkawarin Allah, sai suka ɗauke shi daga Ebenezer suka kai shi Ashdod.

  6. Kashegari da safe da mutanen Ashdod suka farka sai ga Dagon ya fāɗi a gaban akwatin alkawarin Ubangiji. Sai suka ɗauki Dagon suka ajiye a wurin zamansa.

  7. Saboda haka firistocin Dagon da waɗanda suke sujada a haikalin Dagon ba sa taka bakin ƙofar Dagon a Ashdod har wa yau.

  8. Hannun Ubangiji kuwa ya yi nauyi a bisa Ashdod da kewayenta. Ya kawo hallaka ga dukansu, ya kuma buga su da marurai.

  9. Da mutanen Ashdod suka ga abin da yake faruwa, sai suka ce, “Lalle Akwatin Alkawarin Allah na Isra’ila ba zai kasance da mu ba, domin hannunsa yana da nauyi a kanmu da bisan Dagon allahnmu.”

  10. Waɗannan su ne siffofi marurai na zinariya waɗanda Filistiyawa suka aika domin miƙa hadaya don laifi ga Ubangiji, ɗaya domin Ashdod, ɗaya domin Gaza, ɗaya domin Ashkelon, ɗaya domin Gat, ɗaya kuma domin Ekron.

  11. Ya yi yaƙi da Filistiyawa ya kuma rushe katangar Gat, Yabne da kuma Ashdod. Sa’an nan ya sāke gina garuruwa kusa da Ashdod da sauran wurare a cikin Filistiyawa.

  12. Ban da haka, a waɗannan kwanakin na ga mutanen Yahuda waɗanda suka auri mata daga Ashdod, Ammon da Mowab.

  13. Rabin ’ya’yansu suna yaren Ashdod ko kuwa wani yare na waɗansu mutane, ba su kuwa san yadda za su yi Yahudanci ba.

  14. A shekarar da babban shugaban yaƙin da Sargon sarkin Assuriya ya aika, ya zo Ashdod ya kuma fāɗa mata ya kuma ci ta da yaƙi,

  15. da dukan baƙin da suke can; dukan sarakunan Uz; dukan sarakunan Filistiyawa (waɗannan na Ashkelon, Gaza, Ekron da mutanen da aka bari a Ashdod);

  16. Zan hallaka sarkin Ashdod da kuma mai riƙe da sandar mulki na Ashkelon. Zan hukunta Ekron, har sai dukan Filistiyawa sun mutu,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

  17. Ku yi shela ga kagarun Ashdod da kuma ga kagarun Masar. “Ku tara kanku a tuddan Samariya; ku ga rashin jituwar da take a cikinta, da kuma zaluncin da ake yi a cikin mutanenta.”

  18. Baƙi za su mallaki Ashdod, kuma zan kawar da girman kan Filistiyawa.