Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Alliance and Society with the Enemies of God: Are ensnaring

5 ayoyi · 51 fannoni

Ayoyi game da Are ensnaring

  1. Kada ku bari su zauna a cikin ƙasarku, in har kuka bar su, za su ɓata ku da zunubinsu na bautar allolinsu, har zai yă zama muku tarko.”

  2. gama sun ɗauke ku a matsayin abokan gāba, sa’ad da suka ruɗe ku a kan al’amuran Feyor da ’yar’uwarsu Kozbi ’yar shugaban Midiyawa, macen da aka kashe a annoba ta dalili Feyor.”

  3. to, sai ku lura, kada ku jarrabtu ku kwaikwaye su bayan da an riga an shafe su daga gabanku, kada ku tambayi kome game da allolinsu, kuna cewa, “Yaya waɗannan al’ummai suke bauta wa allolinsu? Mu ma za mu yi kamar yadda suka yi.”

  4. In ɗan’uwanka, ko ɗanka, ko ’yarka, ko matar da kake ƙauna, ko abokinka na kusa, a ɓoye ya ruɗe ka, yana cewa, “Mu je mu yi wa waɗansu alloli sujada” (allolin da ko kai, ko kakanninka ba su sani ba,

  5. Suka yi wa gumakansu sujada, waɗanda suka zama tarko gare su.