Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Alliance and Society with the Enemies of God: Persons in authority should denounce
Ayoyi game da Persons in authority should denounce
A cikin kwana uku duk mutanen Yahuda da na Benyamin suka taru a Urushalima. A ranar ashirin ga watan tara, dukan mutanen suka zauna a dandali a gaban gidan Allah cike da ɓacin rai saboda abin da ya faru da kuma ruwan da aka yi.
Sai Ezra firist ya miƙe tsaye ya yi musu magana ya ce, “Kun yi rashin aminci; kun aure mata baƙi, ta haka kuka ƙara kan zunubin Isra’ila.
Yanzu sai ku furta zunubanku ga Ubangiji, Allahn kakanninku, ku kuma yi nufinsa. Ku raba kanku da mutanen da suke kewaye da ku, ku kuma rabu da baƙin mata.”
Ban da haka, a waɗannan kwanakin na ga mutanen Yahuda waɗanda suka auri mata daga Ashdod, Ammon da Mowab.
Rabin ’ya’yansu suna yaren Ashdod ko kuwa wani yare na waɗansu mutane, ba su kuwa san yadda za su yi Yahudanci ba.
Na tsawata musu na kuma kira la’ana a kansu. Na bugi waɗansu mutane na kuma ja gashin kansu. Na sa suka yi rantsuwa da sunan Allah na ce, “Kada ku ba da ’ya’yanku mata aure ga ’ya’yansu maza, ba kuwa za ku auri ’ya’yansu mata wa ’ya’yanku maza ko wa kanku ba.
Ba don aure-aure irin waɗannan ne Solomon sarkin Isra’ila ya yi zunubi ba? A cikin yawancin al’ummai babu sarki kamar sa. Allahnsa ya ƙaunace shi, Allah kuma ya mai da shi sarki a kan dukan Isra’ila, amma duk da haka baren mata suka rinjaye shi ga zunubi.
Yanzu za mu ji cewa ku ma kuna yin duk wannan mugunta kuna zama marasa aminci ga Allahnmu ta wurin auren baren mata?”