Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Alliance and Society with the Enemies of God: Blessedness of forsaking
Ayoyi game da Blessedness of forsaking
Saboda haka kada ku aurar musu da ’yan matanku, kada kuma ku auro wa ’ya’yanku maza ’yan matansu. Kada ku yi wata yarjejjeniya ta abokantaka da su. Idan kun yi biyayya za ku yi ƙarfi, ku kuma ci albarkar ƙasar, har ku bar wa ’ya’yanku gādo na har abada.’
Ku bar hanyoyinku marasa hankali za ku kuwa rayu; yi tafiya a hanyar fahimi.
Saboda haka, “Sai ku fito daga cikinsu, ku keɓe kanku, in ji Ubangiji. Kada ku taɓa wani abu marar tsabta, zan kuma karɓe ku.”
Kuma, “Zan zama Uba a gare ku, ku kuma za ku zama ’ya’yana, maza da mata, in ji Ubangiji Maɗaukaki.”