Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Alliance and Society with the Enemies of God: Exhortations to shun all inducements to
Ayoyi game da Exhortations to shun all inducements to
Ɗana, in masu zunubi sun jarabce ka, kada ka yarda.
In suka ce, “Zo mu tafi; mu yi kwanton ɓauna, mu nemi wani mu kashe, mu fāɗa wa marasa laifi;
mu haɗiye su da rai gaba ɗaya kamar kabari, kamar waɗanda suke gangarawa zuwa rami;
za mu sami dukiya masu daraja iri-iri, mu kuma cika gidajenmu da ganima;
ka haɗa kai da mu, za mu kuwa raba abin da muka sato”
ɗana, kada ka tafi tare da su, kada ka taka ƙafarka a hanyarsu;
Kada ka sa ƙafa a kan hanyar mugaye kada ka bi gurbin mugaye.
Ka guji mugunta, kada ka yi tafiya a kanta; juya daga gare ta ka yi tafiyarka.
Saboda haka, abokaina ƙaunatattu, da yake kun riga kun san wannan, sai ku zauna a faɗake don kada a ɗauke hankalinku ta wurin kuskuren marasa bin dokan nan har ku fāɗi daga matsayinku.