Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Alliance and Society with the Enemies of God

229 ayoyi · 51 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Kaitona da nake zama a Meshek, da nake zama a ciki tentunan Kedar!

  2. Da daɗewa na zauna a cikin waɗanda suke ƙin salama.

  3. Da kawai za ka kashe mugaye, ya Allah! Ku rabu da ni, ku masu kisankai!

  4. Ɗana, in masu zunubi sun jarabce ka, kada ka yarda.

  5. In suka ce, “Zo mu tafi; mu yi kwanton ɓauna, mu nemi wani mu kashe, mu fāɗa wa marasa laifi;

  6. mu haɗiye su da rai gaba ɗaya kamar kabari, kamar waɗanda suke gangarawa zuwa rami;

  7. za mu sami dukiya masu daraja iri-iri, mu kuma cika gidajenmu da ganima;

  8. ka haɗa kai da mu, za mu kuwa raba abin da muka sato”

  9. ɗana, kada ka tafi tare da su, kada ka taka ƙafarka a hanyarsu;

  10. Gama hikima za tă shiga cikin zuciyarka, sani kuma zai faranta maka rai.

  11. Tsinkaya za tă tsare ka, ganewa kuma za tă yi maka jagora.

  12. Hikima za tă cece ka daga hanyoyin mugayen mutane, daga kalmomin mutane masu ɓatanci,

  13. waɗanda suke barin miƙaƙƙun hanyoyi don su yi tafiya a hanyoyi masu duhu,

  14. waɗanda suke jin daɗin yin abin da ba shi da kyau suna kuma farin ciki a mugayen ɓatanci,

  15. waɗanda hanyoyinsu karkatattu ne waɗanda kuma suke cuku-cuku a hanyoyinsu.

  16. Zai kiyaye ku kuma daga mazinaciya, daga mace mai lalata, mai ƙoƙarin kama ka da daɗin bakinta,

  17. wadda ta bar mijin ƙuruciyarta ta kuma ƙyale alkawarin da ta yi a gaban Allah.

  18. Gama gidanta yana kai ga mutuwa hanyarta kuma ga ruhohin matattu.

  19. Duk wanda ya ziyarce ta ba ya ƙara komowa ba zai ƙara komowa ga hanyar rai.

  20. Don haka dole ku yi tafiya a hanyoyin mutanen kirki ku kuma yi ta bi hanyoyin adalai.

  21. Kada ka sa ƙafa a kan hanyar mugaye kada ka bi gurbin mugaye.

  22. Ka guji mugunta, kada ka yi tafiya a kanta; juya daga gare ta ka yi tafiyarka.

  23. Ku bar hanyoyinku marasa hankali za ku kuwa rayu; yi tafiya a hanyar fahimi.

  24. Duk wanda ya nome gonarsa zai sami abinci a yalwace, amma shi da yake naushin iska marar azanci ne.

  25. Ka guji wawa, gama ba za ka sami sani a leɓunansa ba.