Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da All Christians Should Be As Missionaries

198 ayoyi · 66 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sai ta ce wa uwargijiyarta, “Da dai shugabana zai ga annabin da yake Samariya, da annabin zai warkar da shi daga kuturtarsa.”

  2. Na riga na tara dukan kayayyakin da na tanada saboda haikalin Allahna, zinariya saboda dukan ayyukan zinariya, azurfa saboda ayyukan azurfa, tagulla saboda ayyukan tagulla, ƙarfe saboda ayyukan ƙarfe da kuma katako saboda ayyukan katako, da onis don ado, turkuwoyis, duwatsu masu launi dabam-dabam, da kuma dukan duwatsu masu kyau da mabul, dukan waɗannan suna nan jingim.

  3. Ban da haka ma, cikin sa zuciyata ga haikalin Allahna, yanzu na ba da ma’ajina na zinariya da azurfa saboda haikalin Allahna, fiye da kome na tanada saboda wannan haikali,

  4. Mutane suka yi farin ciki ganin yadda shugabanninsu suke bayarwa da yardar rai, gama sun bayar hannu sake da kuma dukan zuciya ga Ubangiji. Dawuda sarki shi ma ya yi farin ciki ƙwarai.

  5. “Amma wane ni, kuma wace ce jama’ata da za mu iya ba ka a yalwace kamar haka? Kome daga gare ka suka fito, kuma mun ba ka abin da kawai ya fito daga hannunka ne.

  6. Ya Ubangiji Allahnmu, game da dukan wannan yalwar da ka tanada saboda ginin haikali saboda Sunanka Mai Tsarki, sun fito daga hannunka ne, kuma dukan naka ne.

  7. Sai shugabannin zuriyar Yahuda da na Benyamin, da firistoci da Lawiyawa, duk wanda Allah ya taɓa zuciyarsa, suka shirya don su je su gina haikalin Ubangiji a Urushalima.

  8. Daga leɓunan yara da jarirai ka kafa yabo domin su sa abokan gābanka da masu ɗaukan fansa su yi shiru.

  9. Abu guda na roƙi Ubangiji, wannan shi ne na nema, cewa in zauna a gidan Ubangiji dukan kwanakin raina, in dubi kyan Ubangiji in kuma neme shi a cikin haikalinsa.

  10. Ku gwada ku gani cewa Ubangiji yana da kyau; mai albarka ne mutumin da yake neman mafaka a gare shi.

  11. Ku zo, ’ya’yana, ku saurare ni; zan koya muku tsoron Ubangiji.

  12. Bakin mutum mai adalci yakan yi magana da hikima, harshensa kuwa yakan yi maganar abin da yake daidai.

  13. Ta haka zan koyar wa masu laifi hanyoyinka, masu zunubi kuma za su komo gare ka.

  14. Ku zo ku saurara, dukanku waɗanda suke tsoron Allah; bari in faɗa muku abin da ya yi mini.

  15. Tun ina yaro, ya Allah, ka koya mini har wa yau ina furta ayyukanka masu banmamaki.

  16. Ko sa’ad da na tsufa da furfura, kada ka yashe ni, ya Allah, sai na furta ikonka ga tsara mai zuwa, ƙarfinka ga dukan waɗanda suke zuwa.

  17. Harshena zai ba da labarin ayyukanka masu adalci dukan yini, gama waɗanda suka so su cutar da ni sun sha kunya suka kuma rikice.

  18. Zan yi tunani a kan dukan ayyukanka in lura da dukan manyan abubuwan da ka aikata.

  19. Ya kafa ƙa’idodi wa Yaƙub ya kuma kafa doka a cikin Isra’ila, wadda ya umarce kakanni-kakanninmu su koya wa ’ya’yansu,

  20. don tsara na biye su san su, har da ’ya’yan da ba a riga an haifa ba, su kuma su faɗa wa ’ya’yansu.

  21. Ta haka za su dogara ga Allah ba kuwa za su manta da ayyukansa ba amma za su kiyaye umarnansa.

  22. Ba za su zama kamar kakanni kakanninsu ba, masu taurinkai da kuma tsara masu tayarwa, waɗanda zukatansu ba su yi biyayya ga Allah ba, waɗanda zukatansu ba su yi aminci ga Allah ba.

  23. Ya rarraba kyautansa ga matalauta, adalcinsa zai dawwama har abada; za a ɗaga ƙahonsa sama da bangirma.

  24. Ya Ubangiji, da gaske ni bawanka ne; ni bawanka ne, ɗan baiwarka; ka ’yantar da ni daga sarƙoƙi.

  25. Zan yi hadayar godiya gare ka in kuma kira bisa sunan Ubangiji.