Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Afflicted Saints

122 ayoyi · 31 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Amma na dogara a kan ƙaunarka marar ƙarewa; zuciyata tana farin ciki a cikin cetonka.

  2. Zan rera ga Ubangiji gama ya yi mini alheri.

  3. Gama a lokacin wahala, zai kiyaye ni lafiya a wurin zamansa; zai ɓoye ni cikin inuwar tabanakul nasa ya kuma sa ni can a bisa dutse.

  4. Sa’an nan kaina zai ɗaukaka a bisa abokan gābana waɗanda suka kewaye ni; a tabanakul nasa zan miƙa hadaya da sowa ta farin ciki; zan rera in kuma yi kiɗi ga Ubangiji.

  5. Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni, kada ka kore bawanka daga gare ka cikin fushi; kai ne ka kasance mai taimakona. Kada ka ƙi ni ko ka yashe ni, Ya Allah Mai cetona.

  6. Na nemi Ubangiji, ya kuwa amsa mini; ya cece ni daga dukan tsoro.

  7. Adali zai iya kasance da wahala da yawa, amma Ubangiji yakan cece shi daga dukansu;

  8. yakan tsare dukan ƙasusuwansa, ba ko ɗayansu da zai karye.

  9. Na yi shiru; ba zan buɗe bakina ba, gama kai ne wanda ka aikata wannan.

  10. Allah yana cikinta, ba za tă fāɗi ba; Allah zai taimake ta da safe.

  11. Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu; Allah na Yaƙub ne kagararmu. Sela

  12. ku kira gare ni a ranar wahala; zan cece ku, za ku kuwa girmama ni.”

  13. Amma ga mugaye, Allah ya ce, “Wace dama ce kuke da ita na haddace dokokina ko na yin maganar alkawarina a leɓunanku?

  14. Kun ƙi umarnina kuka kuma zubar da kalmomina a bayanku

  15. Ka lissafta makokina; ka jera hawayena a littafinka, ba a rubuce suke a cikin littafinka ba?

  16. Ta haka abokan gābana za su juya da baya sa’ad da na nemi taimako. Ta haka zan san cewa Allah yana tare da ni.

  17. Ga Allah, wanda nake yabon maganarsa, ga Ubangiji, wanda nake yabon maganarsa,

  18. Sun shimfiɗa raga don su kama ƙafafuna, damuwa ta sha ƙarfina. Sun haƙa rami a hanyata, amma su kansu suka fāɗa a cikinta. Sela

  19. Zuciyata tana nan daram, ya Allah, zuciyata tana nan daram; zan rera in kuma yi kaɗe-kaɗe.

  20. Zan zo haikalinka da hadayun ƙonawa zan kuwa cika alkawurana gare ka,

  21. alkawuran da leɓunana suka yi alkawari bakina kuma ya faɗa sa’ad da nake cikin wahala.

  22. Zan miƙa kitsen dabbobi gare ka da kuma baye-baye na raguna; zan miƙa bijimai da awaki. Sela

  23. Ko da yake ka sa na ga wahaloli, masu yawa da kuma masu ɗaci, za ka sāke mayar mini da rai; daga zurfafan duniya za ka sāke tā da ni.

  24. Za ka ƙara girmana ka sāke ta’azantar da ni.

  25. Zan yabe ka da garaya saboda amincinka, ya Allah; zan rera yabo gare ka da molo, Ya Mai Tsarki na Isra’ila.