Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Afflicted Saints: Should acknowledge the justice of their chastisements

7 ayoyi · 31 fannoni

Ayoyi game da Should acknowledge the justice of their chastisements

  1. Cikin dukan abubuwan da suka faru da mu, ka kasance mai adalci; ka yi aminci, yayinda mu kuwa muka aikata mugu.

  2. Ya amsa ya ce, “Kina magana kamar wawiya. Alheri kaɗai za mu dinga samu daga Allah ban da wahala?” A cikin wannan duka Ayuba bai yi zunubi ba cikin maganarsa.

  3. Kakan taimaki waɗanda suke murnan yin abin da yake daidai, waɗanda sukan tuna da hanyoyinka. Amma sa’ad da muka ci gaba da yin zunubi, kakan yi fushi. Ta yaya za mu sami ceto ke nan?

  4. Dukanmu mun zama kamar wanda yake marar tsabta, kuma dukan ayyukanmu masu adalci sun zama kamar ƙazaman tsummoki; duk mun zama kamar busasshen ganye, kamar iska haka zunubanmu sukan share mu.

  5. Babu wanda yake kira bisa sunanka ko ya yi ƙoƙarin riƙe ka; gama ka ɓoye fuskarka daga gare mu ka kuma sa muka lalace saboda zunubanmu.

  6. Don mene ne wani mai rai zai yi gunaguni sa’ad da aka ba shi horo domin zunubansa?

  7. Domin na yi masa zunubi, zan fuskanci fushin Ubangiji, har sai ya dubi batuna ya kuma tabbatar da ’yancina. Zai kawo ni zuwa wurin haske; zan ga adalcinsa.