- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa AD 95
The Revelation
John's vision on Patmos unveils the cosmic victory of the Lamb over evil and the final restoration of all creation.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ru’uya ta Yohanna 9:8kusan 96 M.
Gashin kansu ya yi kamar gashin kan mata, haƙoransu kuma sun yi kamar haƙoran zakoki.
- Ru’uya ta Yohanna 9:9kusan 96 M.
Suna da sulkuna kamar sulkunan ƙarfe, ƙarar fikafikansu kuma ta yi kamar motsin dawakai da kekunan yaƙi masu yawa da suke rugawa zuwa yaƙi.
- Ru’uya ta Yohanna 9:10kusan 96 M.
Suna da wutsiyoyi da ƙari kamar kunamai, kuma a wutsiyoyinsu suna da iko su ba wa mutane azaba na wata biyar.
- Ru’uya ta Yohanna 9:11kusan 96 M.
Suna da sarkin da yake mulki a bisansu wanda yake mala’ikan Abis, wanda sunansa a harshen Yahudawa shi ne Abaddon, da harshen Hellenawa kuwa shi ne, Afolliyon.
- Ru’uya ta Yohanna 9:12kusan 96 M.
Bala’i na fari ya wuce, sauran bala’i biyu suna nan zuwa.
- Ru’uya ta Yohanna 9:13kusan 96 M.
Mala’ika na shida ya busa ƙahonsa, sai na ji murya tana fitowa daga ƙahonin bagaden zinariya da suke a gaban Allah.
- Ru’uya ta Yohanna 9:14kusan 96 M.
Ta ce wa mala’ika na shida da yake da ƙahon, “Ka saki mala’iku huɗun nan da suke a daure a babban kogin Yuferites.”
- Ru’uya ta Yohanna 9:15kusan 96 M.
Mala’iku huɗun nan kuwa da aka shirya musamman don wannan sa’a da kuma don wannan rana da wata da kuma shekara aka sake su domin su kashe kashi ɗaya bisa uku na ’yan Adam.
- Ru’uya ta Yohanna 9:16kusan 96 M.
Yawan rundunan masu hawan dawakan nan mutum miliyon ɗari biyu ne. Na ji adadinsu.
- Ru’uya ta Yohanna 9:17kusan 96 M.
Dawakai da masu hawansu da na gani cikin wahayina sun yi kamar. Sulkunansu ja wur ne, baƙin shuɗi, da kuma rawaya kamar farar wuta. Kawunan dawakan sun yi kamar kawunan zakoki, daga bakunansu kuwa wuta, hayaƙi, da farar wuta suna fitowa.
- Ru’uya ta Yohanna 9:18kusan 96 M.
Aka kashe kashi ɗaya bisa uku na ’yan Adam da annobai uku na wuta, hayaƙi da farar wuta da suka fito daga bakunansu.
- Ru’uya ta Yohanna 9:19kusan 96 M.
Ƙarfin dawakan nan kuwa yana a bakunansu da wutsiyoyinsu; gama wutsiyoyinsu suna kama da macizai masu kawuna, da wutsiyoyin ne kuma suke yi wa mutane rauni.
- Ru’uya ta Yohanna 9:20kusan 96 M.
Sauran ’yan Adam da ba a kashe ta wajen waɗannan annobai ba kuwa har wa yau ba su tuba daga aikin hannuwansu ba; ba su daina bauta wa aljanu, da gumakan zinariya, azurfa, tagulla, dutse da na itace, gumakan da ba sa iya gani ko ji ko tafiya ba.
- Ru’uya ta Yohanna 9:21kusan 96 M.
Ba su kuma tuba daga kisankansu, sihirinsu, fasikancinsu ko kuma daga sace-sacensu ba.
- Ru’uya ta Yohanna 10:1kusan 96 M.
Sai na ga wani babban mala’ika yana saukowa daga sama. An lulluɓe shi da girgije, bakan gizo kuma yana kansa; fuskarsa tana kama da rana, ƙafafunsa kuma suna kama da ginshiƙan wuta.
- Ru’uya ta Yohanna 10:2kusan 96 M.
Yana riƙe da ɗan ƙaramin naɗaɗɗen littafi, wanda yake a buɗe a hannunsa. Ya kafa ƙafarsa ta dama a kan teku ƙafarsa ta hagu kuma a kan ƙasa,
- Ru’uya ta Yohanna 10:3kusan 96 M.
ya kuma yi ihu da ƙarfi kamar rurin zaki. Da ya yi ihun, sai muryoyin tsawan nan bakwai suka yi magana.
- Ru’uya ta Yohanna 10:4kusan 96 M.
Sa’ad da tsawan nan bakwai kuwa suka yi magana, ina dab da rubutawa; amma na ji wata murya daga sama ta ce, “Rufe abin da tsawan nan bakwai suka faɗa kada ka rubuta.”
- Ru’uya ta Yohanna 10:5kusan 96 M.
Sai mala’ikan da na gani na tsaye a teku da ƙasa ya ɗaga hannunsa na dama sama.
- Ru’uya ta Yohanna 10:6kusan 96 M.
Ya kuma yi rantsuwa da wannan wanda yake raye har abada abadin, wanda ya halicci sammai da dukan abin da yake cikinsu, duniya da dukan abin da yake cikinta, da kuma teku da dukan abin da yake cikinsa, ya kuma ce, “Babu sauran jinkiri!
- Ru’uya ta Yohanna 10:7kusan 96 M.
Amma a ranakun da mala’ika na bakwai na dab da busa ƙahonsa, za a cika asirin Allah, kamar yadda ya sanar wa bayinsa annabawa.”
- Ru’uya ta Yohanna 10:8kusan 96 M.
Sai muryar da na ji daga sama ta sāke magana da ni ta ce, “Tafi, ka karɓi naɗaɗɗen littafin da yake a buɗe a hannun mala’ikan da yake tsaye bisa teku da ƙasa.”
- Ru’uya ta Yohanna 10:9kusan 96 M.
Sai na je wajen mala’ikan na ce masa yă ba ni ƙaramin naɗaɗɗen littafin. Ya ce mini, “Karɓa ka ci. Zai sa cikinka yă yi tsami, amma ‘a bakinka zai zama da zaƙi kamar zuma.’ ”
- Ru’uya ta Yohanna 10:10kusan 96 M.
Na karɓi ƙaramin naɗaɗɗen littafin daga hannun mala’ikan na kuma ci. Ya yi zaƙi kamar zuma a bakina, amma sa’ad da na cinye, cikina ya yi tsami.
- Ru’uya ta Yohanna 10:11kusan 96 M.
Sa’an nan aka ce mini, “Dole ne ka sāke yin annabci game da mutane masu yawa, al’ummai, harsuna da kuma sarakuna.”