- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa AD 95
The Revelation
John's vision on Patmos unveils the cosmic victory of the Lamb over evil and the final restoration of all creation.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ru’uya ta Yohanna 6:5kusan 96 M.
Sa’ad da Ɗan Ragon ya buɗe hatimi na uku, sai na ji halitta mai rai na uku ya ce, “Zo!” Na duba, can a gabana kuwa ga wani baƙin doki! Mai hawansa yana riƙe da abubuwan awo guda biyu a hannunsa.
- Ru’uya ta Yohanna 6:6kusan 96 M.
Sai na ji wani abu mai ƙara kamar wata murya a tsakiyar halittu huɗun nan masu rai tana cewa, “Kwatan alkama don albashin aikin yini, da kuma kwata uku na sha’ir don albashin yini guda, kada kuwa ka ɓata man da ruwan inabi!”
- Ru’uya ta Yohanna 6:7kusan 96 M.
Sa’ad da Ɗan Ragon ya buɗe hatimi na huɗu, sai na ji muryar halitta mai rai na huɗu ya ce, “Zo!”
- Ru’uya ta Yohanna 6:8kusan 96 M.
Na duba, can a gabana kuwa ga ƙodaɗɗen doki! An ba wa mai hawansa suna Mutuwa, Hades kuwa yana biye da shi. Aka ba su iko a kan kashi ɗaya bisa huɗu na duniya don su yi kisa da takobi, yunwa da annoba, har ma da namomin jeji na duniya.
- Ru’uya ta Yohanna 6:9kusan 96 M.
Sa’ad da ya buɗe hatimi na biyar, sai na ga a ƙarƙashin bagaden rayukan waɗanda aka kashe saboda maganar Allah da kuma shaidar da suka yi.
- Ru’uya ta Yohanna 6:10kusan 96 M.
Suka yi kira da babbar murya suka ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, Mai Tsarki da kuma Mai Gaskiya, sai yaushe za ka shari’anta mazaunan duniya ka kuma ɗauki mana fansar jininmu?”
- Ru’uya ta Yohanna 6:11kusan 96 M.
Sai aka ba wa kowannensu farin riga, aka kuma faɗa musu su ɗan jira kaɗan sai an cika adadin abokansu masu hidima da kuma ’yan’uwansu waɗanda za a kashe kamar yadda su ma aka kashe su.
- Ru’uya ta Yohanna 6:12kusan 96 M.
Ina kallo yayinda ya buɗe hatimi na shida. Sai aka yi babban girgizar ƙasa. Rana ta zama baƙa kamar gwado na gashin akuya, wata kuma gaba ɗaya ya zama ja wur kamar jini,
- Ru’uya ta Yohanna 6:13kusan 96 M.
taurarin sararin sama suka fāffāɗi a ƙasa, kamar yadda ɗanyun ’ya’yan ɓaure suke fāɗuwa daga itacen ɓaure sa’ad da iska mai ƙarfi ta jijjiga shi.
- Ru’uya ta Yohanna 6:14kusan 96 M.
Sararin sama kuwa ya janye kamar naɗaɗɗen littafi, ya yi ta naɗewa, aka kuma kawar da kowane dutse da kowane tsibiri daga wurinsa.
- Ru’uya ta Yohanna 6:15kusan 96 M.
Sa’an nan sarakunan duniya, hakimai, jarumawa, masu arziki, masu ƙarfi, da kowane bawa da kuma kowane ’yantacce ya ɓoye a cikin koguna da kuma cikin duwatsun tsaunuka.
- Ru’uya ta Yohanna 6:16kusan 96 M.
Suka kira duwatsu da tsaunuka suna cewa, “Ku fāɗi a kanmu ku kuma ɓoye mu daga fuskar wannan mai zama a kan kursiyi da kuma daga fushin Ɗan Ragon nan!
- Ru’uya ta Yohanna 6:17kusan 96 M.
Gama babbar ranar fushinsu ta zo, wa kuwa zai iya tsayawa?”
- Ru’uya ta Yohanna 7:1kusan 96 M.
Bayan wannan, na ga mala’iku huɗu, a tsaye a kusurwoyi huɗu na duniya, suna tsare iskoki huɗu na duniya, domin su hana wani iska hurawa a bisan ƙasa ko a bisan teku ko a bisa wani itace.
- Ru’uya ta Yohanna 7:2kusan 96 M.
Sai na ga wani mala’ika yana zuwa daga gabas, yana da hatimin Allah mai rai. Ya yi kira da babbar murya wa mala’ikun nan huɗu da aka ba su iko su cuci ƙasa da teku ya ce,
- Ru’uya ta Yohanna 7:3kusan 96 M.
“Kada ku cuci ƙasa ko teku ko kuma itatuwa sai bayan mun sa hatimi a goshin dukan bayin Allahnmu.”
- Ru’uya ta Yohanna 7:4kusan 96 M.
Sai na ji yawan waɗanda aka sa musu hatimi. Su 144,000 daga dukan kabilan Isra’ila.
- Ru’uya ta Yohanna 7:5kusan 96 M.
Daga kabilar Yahuda mutum 12,000 ne aka sa musu hatimin, daga kabilar Ruben mutum 12,000, daga kabilar Gad mutum 12,000,
- Ru’uya ta Yohanna 7:6kusan 96 M.
daga kabilar Asher mutum 12,000, daga kabilar Naftali mutum 12,000, daga kabilar Manasse mutum 12,000,
- Ru’uya ta Yohanna 7:7kusan 96 M.
daga kabilar Simeyon mutum 12,000, daga kabilar Lawi mutum 12,000, daga kabilar Issakar mutum 12,000,
- Ru’uya ta Yohanna 7:8kusan 96 M.
daga kabilar Zebulun mutum 12,000, daga kabilar Yusuf mutum 12,000, daga kabilar Benyamin mutum 12,000.
- Ru’uya ta Yohanna 7:9kusan 96 M.
Bayan wannan sai na duba, can a gabana kuwa ga wani taro mai girma, wanda ba mai iya ƙirgawa, daga kowace al’umma, kabila, mutane da kuma harshe, suna tsaye a gaban kursiyin da kuma gaban Ɗan Ragon nan. Suna saye da fararen tufafi suna kuma riƙe da rassan dabino a hannuwansu.
- Ru’uya ta Yohanna 7:10kusan 96 M.
Suka tā da murya da ƙarfi suna cewa, “Ceto na Allahnmu ne, wanda yake zaune a bisan kursiyi, da kuma na Ɗan Ragon.”
- Ru’uya ta Yohanna 7:11kusan 96 M.
Dukan mala’iku suna tsaye kewaye da kursiyin da kuma kewaye da dattawan tare da halittu huɗun nan masu rai. Suka fāɗi da fuskokinsu ƙasa a gaban kursiyin suka kuma yi wa Allah sujada,
- Ru’uya ta Yohanna 7:12kusan 96 M.
suna cewa, “Amin! Yabo da ɗaukaka, da hikima da godiya da girma da iko da ƙarfi sun tabbata ga Allahnmu har abada abadin. Amin!”