- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1010–970 BC
The Reign of David
David unites the tribes, conquers Jerusalem, and establishes Israel's golden age—even through deep personal failure.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 1 Tarihi 23:32kusan 1015 K.H.
A haka kuwa Lawiyawa suka yi ayyukansu don Tentin Sujada, don Wuri Mai Tsarki da kuma a ƙarƙashin ’yan’uwansu zuriyar Haruna, saboda hidimar haikalin Ubangiji.
- 1 Tarihi 24:1kusan 1015 K.H.
Waɗannan su ne sassan ’ya’yan Haruna maza. ’Ya’yan Haruna maza su ne Nadab, Abihu, Eleyazar da Itamar.
- 1 Tarihi 24:2kusan 1015 K.H.
Amma Nadab da Abihu sun mutu kafin mahaifinsu, ba su kuma haifi ’ya’ya maza ba; saboda haka Eleyazar da Itamar suka yi hidimar firistoci.
- 1 Tarihi 24:3kusan 1015 K.H.
Tare da taimakon Zadok zuriyar Eleyazar da Ahimelek wani zuriyar Itamar. Dawuda ya karkasa su zuwa ɓangarori don aikinsu bisa ga hidima.
- 1 Tarihi 24:4kusan 1015 K.H.
Akwai ɗumbun shugabanni a cikin zuriyar Eleyazar fiye da zuriyar Itamar, aka kuma karkasa su haka, kawuna goma sha shida daga zuriyar Eleyazar da kuma kawuna iyalai takwas daga zuriyar Itamar.
- 1 Tarihi 24:5kusan 1015 K.H.
Aka karkasa su babu sonkai ta wurin jifa ƙuri’a, gama akwai manyan ma’aikatan wuri mai tsarki da manyan ma’aikatan Allah a cikin zuriyar Eleyazar da Itamar.
- 1 Tarihi 24:6kusan 1015 K.H.
Shemahiya ɗan Netanel, wani Balawe ne marubuci, ya rubuta sunayensu a gaban sarki da kuma a gaban manyan ma’aikata. Zadok firist, Ahimelek ɗan Abiyatar da kuma kawunan iyalan firistoci da na Lawiyawa, iyali guda daga Eleyazar, guda kuma daga Itamar.
- 1 Tarihi 24:7kusan 1015 K.H.
Ƙuri’a ta farko ta faɗa a kan Yehoyarib, na biyu a kan Yedahiya,
- 1 Tarihi 24:8kusan 1015 K.H.
na uku a kan Harim, na huɗu a kan Seyorim,
- 1 Tarihi 24:9kusan 1015 K.H.
na biyar a kan Malkiya, na shida a kan Miyamin,
- 1 Tarihi 24:10kusan 1015 K.H.
na bakwai a kan Hakkoz, na takwas a kan Abiya,
- 1 Tarihi 24:11kusan 1015 K.H.
na tara a kan Yeshuwa, na goma a kan Shekaniya,
- 1 Tarihi 24:12kusan 1015 K.H.
na goma sha ɗaya a kan Eliyashib, na goma sha biyu a kan Yakim,
- 1 Tarihi 24:13kusan 1015 K.H.
na goma sha uku a kan Huffa, na goma sha huɗu a kan Yeshebeyab,
- 1 Tarihi 24:14kusan 1015 K.H.
na goma sha biyar a kan Bilga, na goma sha shida a kan Immer,
- 1 Tarihi 24:15kusan 1015 K.H.
na goma sha shida a kan Hezir, na goma sha takwas a kan Haffizzez,
- 1 Tarihi 24:16kusan 1015 K.H.
na goma sha tara a kan Fetahahiya, na ashirin a kan Ezekiyel,
- 1 Tarihi 24:17kusan 1015 K.H.
na ashirin da ɗaya wa Yakin, na ashirin da biyu a kan Gamul,
- 1 Tarihi 24:18kusan 1015 K.H.
na ashirin da uku wa Delahiya da kuma na ashirin da huɗu a kan Ma’aziya.
- 1 Tarihi 24:19kusan 1015 K.H.
Ga tsarin aikinsu na hidima sa’ad da suka shiga haikalin Ubangiji, bisa ga ƙa’idar da kakansu Haruna ya kafa, yadda Ubangiji, Allah na Isra’ila ya umarce shi.
- 1 Tarihi 24:20kusan 1015 K.H.
Game da sauran zuriyar Lawi kuwa, Daga ’ya’yan Amram maza. Shubayel; daga ’ya’yan Shubayel maza. Yedehiya.
- 1 Tarihi 24:21kusan 1015 K.H.
Game da Rehabiya kuwa, daga ’ya’yansa maza. Isshiya shi ne na fari.
- 1 Tarihi 24:22kusan 1015 K.H.
Daga mutanen Izhar, Shelomot; daga ’ya’yan Shelomot maza, Yahat.
- 1 Tarihi 24:23kusan 1015 K.H.
’Ya’yan Hebron maza su ne, Yeriya na fari, Amariya na biyu, Yahaziyel na uku da Yekameyam na huɗu.
- 1 Tarihi 24:24kusan 1015 K.H.
Ɗan Uzziyel shi ne, Mika; daga ’ya’yan Mika maza, Shamir.