Tsallake zuwa abun ciki

circa 1010–970 BC

The Reign of David

David unites the tribes, conquers Jerusalem, and establishes Israel's golden age—even through deep personal failure.

1,230 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. 1 Tarihi 23:7kusan 1015 K.H.

    Na Gershonawa, Ladan da Shimeyi.

  2. 1 Tarihi 23:8kusan 1015 K.H.

    ’Ya’yan Ladan maza su ne, Yehiyel na farko, Zetam da Yowel, su uku ne duka.

  3. 1 Tarihi 23:9kusan 1015 K.H.

    ’Ya’yan Shimeyi maza su ne, Shelomot, Haziyel da Haran, su uku ne duka. Waɗannan su ne kawunan iyalan Ladan.

  4. 1 Tarihi 23:10kusan 1015 K.H.

    ’Ya’yan Shimeyi maza kuwa su ne, Yahat, Zina, Yewush da Beriya. Waɗannan su ne ’ya’yan Shimeyi maza, su huɗu ne duka.

  5. 1 Tarihi 23:11kusan 1015 K.H.

    Yahat shi ne na fari, Ziza kuma na biyu, amma Yewush da Beriya ba su haifi ’ya’ya maza da yawa ba; saboda haka aka ƙidaya su kamar iyali ɗaya a wurin rabon aiki.

  6. 1 Tarihi 23:12kusan 1015 K.H.

    ’Ya’yan Kohat maza su ne, Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel, su huɗu ne duka.

  7. 1 Tarihi 23:13kusan 1015 K.H.

    ’Ya’yan Amram maza su ne, Haruna da Musa. Haruna shi ne aka keɓe, shi da zuriyarsa har abada, don su tsarkake kayayyakin mafi tsarki, su miƙa hadayu a gaban Ubangiji, su yi hidima a gabansa su kuma furta albarku a cikin sunansa har abada.

  8. 1 Tarihi 23:14kusan 1015 K.H.

    An ƙidaya aka kuma haɗa ’ya’yan Musa maza mutumin Allah a sashen kabilar Lawi.

  9. 1 Tarihi 23:15kusan 1015 K.H.

    ’Ya’yan Musa maza su ne, Gershom da Eliyezer.

  10. 1 Tarihi 23:16kusan 1015 K.H.

    Zuriyar Gershom su ne, Shebuwel ne ɗan fari.

  11. 1 Tarihi 23:17kusan 1015 K.H.

    Zuriyar Eliyezer su ne, Rehabiya ne ɗan fari. Eliyezer ba shi da waɗansu ’ya’ya maza, amma ’ya’yan Rehabiya maza sun yi yawa.

  12. 1 Tarihi 23:18kusan 1015 K.H.

    ’Ya’yan Izhar maza su ne, Shelomit ne ɗan fari.

  13. 1 Tarihi 23:19kusan 1015 K.H.

    ’Ya’yan Hebron maza su ne, Yeriya na fari, Amariya na biyu, Yahaziyel na uku da Yekameyam na huɗu.

  14. 1 Tarihi 23:20kusan 1015 K.H.

    ’Ya’yan Uzziyel maza su ne, Mika na fari da Isshiya na biyu.

  15. 1 Tarihi 23:21kusan 1015 K.H.

    ’Ya’yan Merari maza su ne, Mali da Mushi. ’Ya’yan Mali maza su ne, Eleyazar da Kish.

  16. 1 Tarihi 23:22kusan 1015 K.H.

    Eleyazar ya mutu ba ’ya’yan maza, yana da ’ya’ya mata ne kawai. ’Yan’uwansu, ’ya’yan Kish maza, suka aure su.

  17. 1 Tarihi 23:23kusan 1015 K.H.

    ’Ya’yan Mushi maza su ne, Mali, Eder da Yeremot, su uku ne duka.

  18. 1 Tarihi 23:24kusan 1015 K.H.

    Waɗannan ne zuriyar Lawi bisa ga iyalansu, kawunan iyalai kamar yadda aka rubuta su a ƙarƙashin sunayensu aka kuma ƙirga kowa, wato, masu aikin da suke ’yan shekara ashirin da haihuwa ko fiye waɗanda suka yi hidima a cikin haikalin Ubangiji.

  19. 1 Tarihi 23:25kusan 1015 K.H.

    Gama Dawuda ya ce, “Tun da Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya ba da hutu ga mutanensa, ya kuma zo ya zauna a Urushalima har abada,

  20. 1 Tarihi 23:26kusan 1015 K.H.

    Lawiyawa ba sa ƙara bukata su ɗauki tabanakul ko kuwa waɗansu kayayyakin da ake amfani da su a hidima.”

  21. 1 Tarihi 23:27kusan 1015 K.H.

    Bisa ga umarnin ƙarshe na Dawuda, za a ƙidaya Lawiyawa daga ’yan shekara ashirin ko fiye.

  22. 1 Tarihi 23:28kusan 1015 K.H.

    Aikin Lawiyawa shi ne su taimaki zuriyar Haruna a hidimar haikalin Ubangiji; su lura da filaye da kuma ɗakunan da suke gefe, su tsarkake dukan kayayyaki masu tsarki, su kuma yi waɗansu ayyuka a gidan Allah.

  23. 1 Tarihi 23:29kusan 1015 K.H.

    Su ne za su lura da burodin da aka ajiye a tebur, lallausan gari don hadaya ta gari, waina marar yisti, toyawa da kwaɓawa, da kuma dukan awon yawa da kuma girman abubuwa.

  24. 1 Tarihi 23:30kusan 1015 K.H.

    Su ne kuma za su tsaya kowace safiya su yi godiya, su kuma yabi Ubangiji. Za su kuma yi haka da yamma

  25. 1 Tarihi 23:31kusan 1015 K.H.

    da kuma a duk sa’ad da aka miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji a Asabbatai da bukukkuwan Sabon Wata da kuma a ƙayyadaddun bukukkuwa, za su yi hidima a gaban Ubangiji kullum bisa ga yawan da aka tsara da kuma a hanyar da aka tsara musu.