Tsallake zuwa abun ciki

circa 1010–970 BC

The Reign of David

David unites the tribes, conquers Jerusalem, and establishes Israel's golden age—even through deep personal failure.

1,230 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. 1 Tarihi 24:25kusan 1015 K.H.

    Ɗan’uwan Mika shi ne, Isshiya; daga ’ya’yan Isshiya maza, Zakariya.

  2. 1 Tarihi 24:26kusan 1015 K.H.

    ’Ya’yan Merari su ne, Mali da Mushi. Ɗan Ya’aziya shi ne, Beno.

  3. 1 Tarihi 24:27kusan 1015 K.H.

    ’Ya’yan Merari su ne, daga Ya’aziya, Beno, Shoham, Zakkur da Ibri.

  4. 1 Tarihi 24:28kusan 1015 K.H.

    Daga Mali, Eleyazar, wanda ba shi da ’ya’ya maza.

  5. 1 Tarihi 24:29kusan 1015 K.H.

    Daga Kish, ɗan Kish shi ne, Yerameyel.

  6. 1 Tarihi 24:30kusan 1015 K.H.

    Kuma ’ya’yan Mushi maza su ne, Mali, Eder da Yerimot. Waɗannan su ne Lawiyawa bisa ga iyalansu.

  7. 1 Tarihi 24:31kusan 1015 K.H.

    Suka kuma jifa ƙuri’a, kamar dai yadda ’yan’uwansu zuriyar Haruna suka yi, a gaban Sarki Dawuda da gaban Zadok, Ahimelek, da kuma a gaban kawunan iyalan firistoci da na Lawiyawa. Aka yi da iyalan wa daidai da iyalan ƙane.

  8. 1 Tarihi 25:1kusan 1015 K.H.

    Dawuda tare da shugabannin mayaƙa, suka keɓe waɗansu daga ’ya’yan Asaf, Heman da Yedutun don hidimar yin annabci, suna amfani da garayu, molaye da ganguna. Ga jerin mutanen da suka yi wannan hidima.

  9. 1 Tarihi 25:2kusan 1015 K.H.

    Daga ’ya’yan Asaf, Zakkur, Yusuf, Netaniya da Asarela. ’Ya’yan Asaf sun kasance a ƙarƙashin kulawar Asaf, wanda ya yi annabci a ƙarƙashin kulawar sarki.

  10. 1 Tarihi 25:3kusan 1015 K.H.

    Game da Yedutun kuwa, daga ’ya’yansa maza. Gedaliya, Zeri, Yeshahiya, Shimeyi, Hashabiya da Mattitiya, su shida ne duka, a ƙarƙashin kulawar mahaifinsu Yedutun, wanda ya yi annabci, yana amfani da garaya a yin godiya da yabon Ubangiji.

  11. 1 Tarihi 25:4kusan 1015 K.H.

    Game da Heman kuwa, daga ’ya’yansa maza. Bukkiya, Mattaniya, Uzziyel, Shebuwel, Yerimot; Hananiya, Hanani, Eliyata, Giddalti, Romamti-Ezer, Yoshbekasha, Malloti, Hotir da Mahaziyot.

  12. 1 Tarihi 25:5kusan 1015 K.H.

    Dukan waɗannan ’ya’yan Heman ne mai duba na sarki. An ba shi su ta wurin alkawarin Allah don yă ɗaukaka shi. Allah ya ba Heman ’ya’ya maza goma sha huɗu da ’ya’ya mata uku.

  13. 1 Tarihi 25:6kusan 1015 K.H.

    Dukan waɗannan mutane suna a ƙarƙashin kulawar mahaifansu don kaɗe-kaɗe da bushe-bushe a cikin haikalin Ubangiji, da ganguna, molaye da garayu, don hidima a gidan Allah. Asaf, Yedutun da Heman suna ƙarƙashin kulawar sarki.

  14. 1 Tarihi 25:7kusan 1015 K.H.

    Da su da danginsu, dukansu su 288 ne kuma horarru da ƙwararru ne a kaɗe-kaɗe da bushe-bushe domin Ubangiji.

  15. 1 Tarihi 25:8kusan 1015 K.H.

    Baba ko yaro, malami ko ɗalibi, duk suka jefa ƙuri’a saboda ayyukan da za su yi.

  16. 1 Tarihi 25:9kusan 1015 K.H.

    Ƙuri’a ta fari, wadda take don Asaf, ta fāɗo a kan Yusuf, ’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta biyu a kan Gedaliya, danginsa da ’ya’yansa maza, 12

  17. 1 Tarihi 25:10kusan 1015 K.H.

    ta uku a kan Zakkur, ’ya’yansa da danginsa, 12

  18. 1 Tarihi 25:11kusan 1015 K.H.

    ta huɗu a kan Izri, ’ya’yansa maza da danginsa, 12

  19. 1 Tarihi 25:12kusan 1015 K.H.

    ta biyar a kan Netaniya, ’ya’yansa maza da danginsa, 12

  20. 1 Tarihi 25:13kusan 1015 K.H.

    ta shida a kan Bukkiya, ’ya’yansa maza da danginsa, 12

  21. 1 Tarihi 25:14kusan 1015 K.H.

    ta bakwai a kan Yesarela, ’ya’yansa maza da danginsa, 12

  22. 1 Tarihi 25:15kusan 1015 K.H.

    ta takwas a kan Yeshahiya, ’ya’yansa maza da danginsa, 12

  23. 1 Tarihi 25:16kusan 1015 K.H.

    ta tara a kan Mattaniya, ’ya’yansa maza da danginsa, 12

  24. 1 Tarihi 25:17kusan 1015 K.H.

    ta goma a kan Shimeyi, ’ya’yansa maza da danginsa, 12

  25. 1 Tarihi 25:18kusan 1015 K.H.

    ta goma sha ɗaya a kan Azarel, ’ya’yansa maza da danginsa, 12