circa 6 BC – AD 30
The Life of Jesus
The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Markus 14:66kusan 33 M.
Yayinda Bitrus yake ƙasa a filin gidan, sai wata yarinya, baiwa, ɗaya daga cikin ma’aikatan babban firist, ta zo can.
- Markus 14:67kusan 33 M.
Da ta ga Bitrus yana jin ɗumi, sai ta dube shi da kyau. Ta ce, “Kai ma kana tare da Yesu, Banazare.”
- Markus 14:68kusan 33 M.
Amma ya yi mūsu ya ce, “Ban san abin da kike magana ba, balle ma in fahimce ki.” Sai ya fita zuwa zaure.
- Markus 14:69kusan 33 M.
Da baiwar ta gan shi a can, sai ta sāke gaya wa waɗanda suke tsattsaye a wurin, ta ce, “Wannan mutum yana ɗaya daga cikinsu.”
- Markus 14:70kusan 33 M.
Sai ya sāke yin musu. Bayan ɗan lokaci kaɗan, sai waɗanda suke tsattsaye kusa suka ce wa Bitrus, “Lalle, kana ɗaya daga cikinsu, gama kai mutumin Galili ne.”
- Markus 14:71kusan 33 M.
Sai ya fara la’antar kansa, yana rantsuwa musu, yana cewa, “Ban san wannan mutumin da kuke magana a kai ba.”
- Markus 14:72kusan 33 M.
Nan da nan zakara ya yi cara sau na biyu. Sai Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya yi masa cewa, “Kafin zakara yă yi cara sau biyu,za ka yi mūsun sanina sau uku.” Sai ya fashe da kuka.
- Markus 15:1kusan 33 M.
Da sassafe, sai manyan firistoci da dattawa, da malaman dokoki, da dukan Majalisa, suka yanke shawara. Suka daure Yesu, suka kai shi, suka miƙa shi ga Bilatus.
- Markus 15:2kusan 33 M.
Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya amsa ya ce, “I, haka yake, kamar yadda ka faɗa.”
- Markus 15:3kusan 33 M.
Manyan firistoci suka zarge shi a kan abubuwa da yawa.
- Markus 15:4kusan 33 M.
Don haka Bilatus ya sāke tambayarsa ya ce, “Ba za ka amsa ba? Dubi abubuwa da yawa da suke zarginka da su.”
- Markus 15:5kusan 33 M.
Amma har yanzu, Yesu bai ba da amsa ba, Bilatus ya yi mamaki.
- Markus 15:6kusan 33 M.
Yanzu fa, al’ada ce a lokacin Bikin, a saki ɗan kurkuku guda wanda mutane suka roƙa.
- Markus 15:7kusan 33 M.
Wani mutumin da ake kira Barabbas, yana a kurkuku, tare da waɗansu ’yan tawaye da suka yi kisankai a lokacin wani hargitsi.
- Markus 15:8kusan 33 M.
Taron suka matso, suka ce roƙi Bilatus yă yi musu abin da ya saba yi.
- Markus 15:9kusan 33 M.
Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Kuna so in sakar muku Sarkin Yahudawa?”
- Markus 15:10kusan 33 M.
Don ya san saboda sonkai ne manyan firistoci suka ba da Yesu a gare shi.
- Markus 15:11kusan 33 M.
Amma manyan firistoci suka zuga taron su sa a saki Barabbas, a maimakon Yesu.
- Markus 15:12kusan 33 M.
Bilatus ya tambaye su ya ce, “To, me zan yi da wanda kuke ce da shi, sarkin Yahudawa?”
- Markus 15:13kusan 33 M.
Suka yi ihu, suka ce, “A gicciye shi!”
- Markus 15:14kusan 33 M.
Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Don me? Wane laifi ya yi?” Amma suka ƙara yin ihu suna cewa, “A gicciye shi!”
- Markus 15:15kusan 33 M.
Don son yă faranta wa taron rai, sai Bilatus ya sakar musu Barabbas. Ya sa aka yi wa Yesu bulala, sa’an nan ya ba da shi a gicciye.
- Markus 15:16kusan 33 M.
Sojojin suka tafi da Yesu cikin fadar gwamna (wato, Firetoriyum), suka kira dukan kamfanin sojoji wuri ɗaya.
- Markus 15:17kusan 33 M.
Suka sa masa wata riga mai ruwan shunayya, suka kuma tuƙa rawanin ƙaya suka sa masa.
- Markus 15:18kusan 33 M.
Sai suka fara ce masa, “Ranka yă daɗe sarkin Yahudawa!”