Tsallake zuwa abun ciki

circa 6 BC – AD 30

The Life of Jesus

The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.

3,779 ayoyi · 4 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Markus 15:44kusan 33 M.

    Bilatus ya yi mamaki da ya ji cewa Yesu ya riga ya mutu. Sai ya kira jarumin ya tambaye shi ko Yesu ya riga ya mutu.

  2. Markus 15:45kusan 33 M.

    Da ya ji ta bakin jarumin cewa haka ne, sai ya ba wa Yusuf jikin.

  3. Markus 15:46kusan 33 M.

    Sai Yusuf ya kawo zanen lilin, ya saukar da jikin, ya nannaɗe shi da lilin ɗin, sa’an nan ya sa shi a kabarin da aka fafe a cikin dutse. Sai ya gungura wani dutse ya rufe bakin kabarin.

  4. Markus 15:47kusan 33 M.

    Maryamu Magdalin da Maryamu uwar Yusuf sun ga inda aka kwantar da shi.

  5. Markus 16:1kusan 33 M.

    Da Asabbaci ya wuce, sai Maryamu Magdalin, Maryamu mahaifiyar Yaƙub, da kuma Salome suka sayi kayan ƙanshi domin su je su shafa wa jikin Yesu.

  6. Markus 16:2kusan 33 M.

    A ranar farko ta mako, da sassafe, bayan fitowar rana, suna kan hanyarsu zuwa kabarin ke nan,

  7. Markus 16:3kusan 33 M.

    sai suka tambaye juna suka ce, “Wane ne zai gungura mana dutsen daga bakin kabarin?”

  8. Markus 16:4kusan 33 M.

    Amma da suka ɗaga kai, sai suka ga cewa, an riga an gungura dutsen. Dutsen kuwa babba ne.

  9. Markus 16:5kusan 33 M.

    Da suna shiga cikin kabarin, sai suka ga wani saurayi sanye da farar riga, yana zaune a hannun dama, sai suka firgita.

  10. Markus 16:6kusan 33 M.

    Ya ce, “Kada ku firgita. Kuna neman Yesu Banazare wanda aka gicciye ne. Ya tashi! Ba ya nan. Ku dubi inda aka kwantar da shi.

  11. Markus 16:7kusan 33 M.

    Amma ku tafi ku gaya wa almajiransa da kuma Bitrus cewa, ‘Ya sha gabanku zuwa Galili. Can za ku gan shi, kamar yadda ya faɗa muku.’ ”

  12. Markus 16:8kusan 33 M.

    Da rawan jiki da kuma ruɗewa, matan suka fita a guje daga kabarin. Ba su kuwa gaya wa kowa ba, don suna tsoro.

  13. Markus 16:9kusan 33 M.

    Da Yesu ya tashi daga matattu da safe, a ranar farko ta mako, ya fara bayyana ga Maryamu Magdalin, wadda ya fitar da aljanu bakwai daga cikinta.

  14. Markus 16:10kusan 33 M.

    Ta je ta gaya wa waɗanda dā suke tare da shi, waɗanda kuma suke makoki da kuka.

  15. Markus 16:11kusan 33 M.

    Da suka ji cewa Yesu yana da rai, har ma ta gan shi, ba su gaskata ba.

  16. Markus 16:12kusan 33 M.

    Daga baya Yesu ya bayyana a wani kamanni dabam ga biyunsu, yayinda suke tafiya ƙauye.

  17. Markus 16:13kusan 33 M.

    Waɗannan kuwa suka koma suka shaida wa sauran, amma su ma ba su gaskata ba.

  18. Markus 16:14kusan 33 M.

    Bayan haka, Yesu ya bayyana ga Sha Ɗayan, yayinda suke cin abinci. Ya tsawata musu a kan rashin bangaskiyarsu, da yadda suka ƙi gaskata waɗanda suka gan shi bayan ya tashi.

  19. Markus 16:15kusan 33 M.

    Ya ce, musu, “Ku tafi cikin dukan duniya, ku yi wa’azin bishara ga dukan halitta.

  20. Markus 16:16kusan 33 M.

    Duk wanda ya gaskata, aka kuma yi masa baftisma, zai sami ceto. Amma duk wanda bai gaskata ba kuwa, zai hallaka.

  21. Markus 16:17kusan 33 M.

    Waɗannan alamu za su kasance tare da waɗanda suka gaskata. A cikin sunana za su fitar da aljanu, za su yi magana da sababbin harsuna.

  22. Markus 16:18kusan 33 M.

    Za su ɗauki macizai da hannuwansu. In kuwa suka sha mugun dafi, ba zai cuce su ba ko kaɗan. Za su ɗibiya hannuwansu a kan marasa lafiya, su kuwa warke.”

  23. Markus 16:19kusan 33 M.

    Bayan Ubangiji Yesu ya yi musu magana, sai aka ɗauke shi zuwa sama, ya kuma zauna a hannun dama na Allah.

  24. Markus 16:20kusan 33 M.

    Sai almajiran suka fita, suka yi wa’azi ko’ina. Ubangiji kuwa ya yi aiki tare da su, ya tabbatar da maganarsa ta wurin alamu da suke biye da maganar.

  25. Luka 1:1kusan 5 K.H.

    Mutane da yawa sun ɗau niyyar rubuta labarin abubuwan da aka cika a cikinmu,