Tsallake zuwa abun ciki

circa 6 BC – AD 30

The Life of Jesus

The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.

3,779 ayoyi · 4 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Mattiyu 26:16kusan 33 M.

    Daga wannan lokaci, Yahuda ya yi ta neman zarafin da zai miƙa shi.

  2. Mattiyu 26:17kusan 33 M.

    A rana ta fari ta Bikin Burodi Marar Yisti, sai almajiran suka zo wurin Yesu suka yi tambaya suka ce, “Ina kake so mu je mu shirya maka wurin da za ka ci Bikin Ƙetarewa?”

  3. Mattiyu 26:18kusan 33 M.

    Ya amsa ya ce, “Ku shiga gari wurin wāne, ku ce masa, ‘Malam ya ce, lokacina ya yi kusa. Zan ci Bikin Ƙetarewa tare da almajiraina a gidanka.’ ”

  4. Mattiyu 26:19kusan 33 M.

    Saboda haka almajiran suka yi yadda Yesu ya umarce su, suka kuwa shirya Bikin Ƙetarewa.

  5. Mattiyu 26:20kusan 33 M.

    Da yamma ta yi, sai Yesu ya zauna don cin abinci tare da Sha Biyun.

  6. Mattiyu 26:21kusan 33 M.

    Yayinda suke cin abinci, sai ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.”

  7. Mattiyu 26:22kusan 33 M.

    Suka yi baƙin ciki ƙwarai, suka fara ce masa da ɗaya-ɗaya, “Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.”

  8. Mattiyu 26:23kusan 33 M.

    Yesu ya amsa ya ce, “Wanda ya sa hannunsa a kwano tare da ni ne, zai bashe ni.

  9. Mattiyu 26:24kusan 33 M.

    Ɗan Mutum zai tafi kamar yadda aka rubuta game da shi. Amma kaiton mutumin da zai bashe Ɗan Mutum! Da ma ba a haifi mutumin nan ba, da ya fi masa.”

  10. Mattiyu 26:25kusan 33 M.

    Sa’an nan Yahuda, wanda zai bashe shi ya ce, “Tabbatacce ba ni ba ne, ko, Rabbi?” Yesu ya amsa ya ce, “I, kai ma ka fada.”

  11. Mattiyu 26:26kusan 33 M.

    Yayinda suke cikin cin abinci, Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya ya kuma kakkarya, ya ba wa almajiransa yana cewa, “Ku karɓa ku ci; wannan jikina ne.”

  12. Mattiyu 26:27kusan 33 M.

    Sa’an nan ya ɗauki kwaf, ya yi godiya, ya kuma ba su, yana cewa, “Ku shassha daga cikinsa, dukanku.

  13. Mattiyu 26:28kusan 33 M.

    Wannan jinina ne na sabon alkawari, wanda aka zubar saboda mutane da yawa, don gafarar zunubai.

  14. Mattiyu 26:29kusan 33 M.

    Ina gaya muku, ba zan ƙara shan ruwan inabin nan ba har sai ranar da zan sha shi sabo tare da ku a mulkin Ubana.”

  15. Mattiyu 26:30kusan 33 M.

    Da suka rera waƙa, sai suka fita, suka tafi Dutsen Zaitun.

  16. Mattiyu 26:31kusan 33 M.

    Sai Yesu ya ce musu, “A wannan dare, dukanku za ku ja da baya saboda ni, gama a rubuce yake cewa, “ ‘Zan bugi makiyayin, tumakin garken kuwa za su fasu.’

  17. Mattiyu 26:32kusan 33 M.

    Amma bayan na tashi, zan sha gabanku zuwa Galili.”

  18. Mattiyu 26:33kusan 33 M.

    Bitrus ya amsa ya ce, “Ko da duka sun ja da baya saboda kai, ba zan taɓa ja da baya ba.”

  19. Mattiyu 26:34kusan 33 M.

    Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya maka, a daren nan, kafin zakara yă yi cara, za ka yi mūsun sanina sau uku.”

  20. Mattiyu 26:35kusan 33 M.

    Bitrus ya furta, “Ko da ma zan mutu ne tare da kai, ba zan taɓa yin mūsun saninka ba.” Dukan sauran almajiran ma suka faɗa haka.

  21. Mattiyu 26:36kusan 33 M.

    Sa’an nan Yesu ya tafi da almajiransa zuwa wani wurin da ake kira Getsemane, ya ce musu, “Ku zauna nan, in je can in yi addu’a.”

  22. Mattiyu 26:37kusan 33 M.

    Ya ɗauki Bitrus da ’ya’ya biyun nan na Zebedi tare da shi, sai ya fara baƙin ciki, ya kuma damu.

  23. Mattiyu 26:38kusan 33 M.

    Sai ya ce musu, “Raina yana cike da baƙin ciki har kamar zan mutu. Ku dakata a nan, ku kuma yi tsaro tare da ni.”

  24. Mattiyu 26:39kusan 33 M.

    Da ya yi gaba kaɗan, sai ya fāɗi a ƙasa, ya yi addu’a ya ce, “Ubana, in mai yiwuwa ne, a ɗauke mini wannan kwaf. Amma ba nufina ba, sai naka.”

  25. Mattiyu 26:40kusan 33 M.

    Sa’an nan ya komo wurin almajiransa, ya tarar suna barci. Ya tambayi Bitrus ya ce, “Ashe, ba za ku iya yin tsaro tare da ni ko na sa’a guda ba?