circa 6 BC – AD 30
The Life of Jesus
The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Mattiyu 26:66kusan 33 M.
Me kuka gani?” Suka amsa, suka ce, “Ya cancanci mutuwa.”
- Mattiyu 26:67kusan 33 M.
Sai suka tottofa masa miyau a fuskarsa, suka kuma bubbuge shi da hannuwansu. Waɗansu kuma suka mammare shi
- Mattiyu 26:68kusan 33 M.
suka ce, “Yi mana annabci, Kiristi. Wa ya buge ka?”
- Mattiyu 26:69kusan 33 M.
To, Bitrus yana nan zaune a filin, sai wata yarinya baiwa, ta zo wurinsa. Ta ce, “Kai ma kana tare da Yesu mutumin Galili.”
- Mattiyu 26:70kusan 33 M.
Amma ya yi mūsu a gabansu duka. Ya ce, “Ban san abin da kike magana ba.”
- Mattiyu 26:71kusan 33 M.
Sa’an nan ya fito zuwa hanyar shiga, inda wata yarinya kuma ta gan shi, ta ce wa mutanen da suke can, “Wannan mutum ma yana tare da Yesu Banazare.”
- Mattiyu 26:72kusan 33 M.
Ya sāke mūsu har da rantsuwa, yana cewa, “Ban ma san mutumin nan ba!”
- Mattiyu 26:73kusan 33 M.
Bayan ɗan lokaci, sai na tsattsaye a wurin, suka hauro wurin Bitrus, suka ce, “Tabbatacce, kai ɗayansu ne, don harshen maganarka, ya tone ka.”
- Mattiyu 26:74kusan 33 M.
Sai ya fara la’antar kansa, yana ta rantsuwa yana ce musu, “Ban ma san mutumin nan ba!” Nan da take, sai zakara ya yi cara.
- Mattiyu 26:75kusan 33 M.
Sai Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya yi cewa, “Kafin zakara yă yi cara, za ka yi mūsun sani na sau uku.” Sai ya fita waje, ya yi ta kuka.
- Mattiyu 27:1kusan 33 M.
Da wayewar gari, sai dukan manyan firistoci da dattawan mutane suka yanke shawara su kashe Yesu.
- Mattiyu 27:2kusan 33 M.
Suka daure shi, suka tafi da shi, suka ba da shi ga gwamna Bilatus.
- Mattiyu 27:3kusan 33 M.
Sa’ad da Yahuda, wanda ya bashe Yesu, ya ga an yanke wa Yesu hukuncin kisa, sai ya yi “da na sani.” Ya je mayar wa manyan firistoci da dattawan kuɗin azurfa talatin ɗin.
- Mattiyu 27:4kusan 33 M.
Ya ce, “Na yi zunubi da na ci amanar marar laifi.” Suka ce masa, “Ina ruwanmu da wannan? Wannan dai ruwanka ne.”
- Mattiyu 27:5kusan 33 M.
Sai Yahuda ya zubar da kuɗin a cikin haikalin ya tafi. Sa’an nan ya je ya rataye kansa.
- Mattiyu 27:6kusan 33 M.
Manyan firistoci suka ɗauki kuɗin, suka ce, “Doka ta hana a sa kuɗin a cikin ma’aji, da yake kuɗin jini ne.”
- Mattiyu 27:7kusan 33 M.
Saboda haka, sai suka yanke shawara su yi amfani da kuɗin suka sayi filin mai yin tukwane, saboda binne baƙi.
- Mattiyu 27:8kusan 33 M.
Shi ya sa ake kiran filin, Filin Jini har yă zuwa yau.
- Mattiyu 27:9kusan 33 M.
Sai abin da aka faɗa ta bakin annabi Irmiya ya cika cewa, “Suka ɗauki azurfa talatin, kuɗin da mutanen Isra’ila suka sa a kansa,
- Mattiyu 27:10kusan 33 M.
suka kuma yi amfani da su, suka sayi filin mai yin tukwane, kamar yadda Ubangiji ya umarce ni.”
- Mattiyu 27:11kusan 33 M.
Ana cikin haka, Yesu kuwa yana tsaye a gaban gwamna, sai gwamnan ya tambaye shi, “Kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya ce, “I, haka ne, kamar yadda ka faɗa.”
- Mattiyu 27:12kusan 33 M.
Da manyan firistoci da dattawa suka zarge shi, bai ba da amsa ba.
- Mattiyu 27:13kusan 33 M.
Sai Bilatus ya tambaye shi ya ce, “Ba ka jin shaidar da suke kawowa a kanka?”
- Mattiyu 27:14kusan 33 M.
Amma Yesu bai ce uffam game da ko ɗaya daga cikin zargin da suka yi masa ba. Har gwamna ya yi mamaki ƙwarai.
- Mattiyu 27:15kusan 33 M.
A wannan irin Biki, gwamna yana da wata al’ada, ta sakin ɗan kurkuku guda wanda taron suka zaɓa.