Tsallake zuwa abun ciki

circa 6 BC – AD 30

The Life of Jesus

The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.

3,779 ayoyi · 4 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Mattiyu 27:41kusan 33 M.

    Haka ma, manyan firistoci da malaman dokoki da kuma dattawa, suka yi ta yin masa ba’a, suna cewa,

  2. Mattiyu 27:42kusan 33 M.

    “Ya ceci waɗansu, amma ya kāsa ceton kansa! In shi ne Sarkin Isra’ila! To, yă sauko daga kan gicciyen nan, mu kuwa mu gaskata shi.

  3. Mattiyu 27:43kusan 33 M.

    Ya dogara ga Allah. Bari Allah yă cece shi yanzu, in yana sonsa, domin ya ce, ‘Ni Ɗan Allah ne.’ ”

  4. Mattiyu 27:44kusan 33 M.

    Haka ma, ’yan fashin da aka gicciye tare da shi, suka zazzage shi.

  5. Mattiyu 27:45kusan 33 M.

    Daga sa’a ta shida, har zuwa sa’a ta tara, duhu ya rufe ƙasa duka.

  6. Mattiyu 27:46kusan 33 M.

    Wajen sa’a ta tara, Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi,lama sabaktani?” (Wato, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”).

  7. Mattiyu 27:47kusan 33 M.

    Sa’ad da waɗanda suke tsattsaye a wurin suka ji haka, sai suka ce, “Yana kiran Iliya.”

  8. Mattiyu 27:48kusan 33 M.

    Nan da nan, ɗaya daga cikinsu ya ruga, ya sami soso, ya jiƙa shi da ruwan tsami, ya sa a sanda, ya miƙa wa Yesu, yă sha.

  9. Mattiyu 27:49kusan 33 M.

    Sauran kuwa suka ce, “Ƙyale shi mu ga, ko Iliya zai zo yă cece shi.”

  10. Mattiyu 27:50kusan 33 M.

    Da Yesu ya sāke ɗaga murya da ƙarfi, sai ya saki ruhunsa.

  11. Mattiyu 27:51kusan 33 M.

    A daidai wannan lokaci, sai labulen haikali ya tsage gida biyu, daga sama har ƙasa. Ƙasa ta jijjiga, duwatsu kuma suka farfashe.

  12. Mattiyu 27:52kusan 33 M.

    Kaburbura suka bubbuɗe, jikunan tsarkaka da yawa kuwa cikin waɗanda da suka mutu, suka tashi.

  13. Mattiyu 27:53kusan 33 M.

    Suka firfito daga kaburbura, sa’an nan bayan tashin Yesu daga matattu, suka shiga birni mai tsarki, suka bayyana ga mutane da yawa.

  14. Mattiyu 27:54kusan 33 M.

    Da jarumin nan tare da waɗanda suke tsaron Yesu, suka ga girgizar ƙasa, da kuma abin da ya faru, sai tsoro ya kama su, suka kuma ce, “Gaskiya, wannan Ɗan Allah ne!”

  15. Mattiyu 27:55kusan 33 M.

    Akwai mata da yawa a can, suna kallo daga nesa. Sun bi Yesu tun daga Galili, suna masa hidima.

  16. Mattiyu 27:56kusan 33 M.

    A cikinsu, akwai Maryamu Magdalin, da Maryamu uwar Yaƙub da Yoses, da kuma uwar ’ya’yan Zebedi.

  17. Mattiyu 27:57kusan 33 M.

    Da yamma ta yi, sai ga wani mutum mai arziki daga Arimateya, sunansa Yusuf, wanda shi da kansa almajirin Yesu ne.

  18. Mattiyu 27:58kusan 33 M.

    Ya je wurin Bilatus, ya roƙe shi yă ba shi jikin Yesu. Sai Bilatus ya umarta a ba shi.

  19. Mattiyu 27:59kusan 33 M.

    Yusuf ya ɗauki jikin ya nannaɗe shi da zanen lilin mai tsabta.

  20. Mattiyu 27:60kusan 33 M.

    Sa’an nan ya sa shi a sabon kabarinsa, wanda ya haƙa a dutse. Bayan ya gungura wani babban dutse ya rufe bakin kabarin, sai ya tafi abinsa.

  21. Mattiyu 27:61kusan 33 M.

    Maryamu Magdalin da ɗayan Maryamun, suna zaune a wurin, ɗaura da kabarin.

  22. Mattiyu 27:62kusan 33 M.

    Kashegari, wato, bayan Ranar Shirye-shirye, sai manyan firistoci da Farisiyawa, suka je wurin Bilatus.

  23. Mattiyu 27:63kusan 33 M.

    Suka ce, “Ranka yă daɗe, mun tuna, mai ruɗin nan tun yana da rai ya ce, ‘Bayan kwana uku, zan tashi daga matattu.’

  24. Mattiyu 27:64kusan 33 M.

    Saboda haka, ka ba da umarni, a tsare kabarin sai rana ta uku ɗin. In ba haka ba, almajiransa za su iya zuwa su sace jikin, sa’an nan su faɗa wa mutane cewa, an tashe shi daga matattu. Ruɗin ƙarshen nan fa, sai yă fi na farkon muni.”

  25. Mattiyu 27:65kusan 33 M.

    Sai Bilatus ya ce, “Shi ke nan, ku ɗebi soja, ku je ku tsare kabarin iya ƙoƙarinku.”