circa 6 BC – AD 30
The Life of Jesus
The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Mattiyu 27:16kusan 33 M.
To, a wannan lokaci kuwa suna da wani shahararren ɗan kurkuku da ake kira Barabbas.
- Mattiyu 27:17kusan 33 M.
Saboda haka da taron suka taru, sai Bilatus ya tambaye su ya ce, “Wane ne a cikinsu kuke so in sakar muku. Barabbas ko Yesu wanda ake kira Kiristi?”
- Mattiyu 27:18kusan 33 M.
Don ya san saboda sonkai ne suka ba da Yesu a gare shi.
- Mattiyu 27:19kusan 33 M.
Yayinda Bilatus yake zaune a kan kujerar shari’a, sai matarsa ta aika masa da wannan saƙo cewa, “Kada ka sa hannunka a kan marar laifin nan, domin na sha wahala ƙwarai, a cikin mafarki yau game da shi.”
- Mattiyu 27:20kusan 33 M.
Amma manyan firistoci da dattawa suka shawo kan taron, su ce, a ba su Barabbas, amma a kashe Yesu.
- Mattiyu 27:21kusan 33 M.
Gwamna ya yi tambaya ya ce, “Wane ne cikin biyun nan, kuke so in sakar muku?” Suka ce, “Barabbas.”
- Mattiyu 27:22kusan 33 M.
Bilatus ya yi tambaya, “To, me zan yi da Yesu wanda ake kira Kiristi?” Duka suka ce, “A gicciye shi!”
- Mattiyu 27:23kusan 33 M.
Bilatus ya ce, “Don me? Wane laifi ya yi?” Amma suka ƙara tā da ihu, suna cewa, “A gicciye shi!”
- Mattiyu 27:24kusan 33 M.
Da Bilatus ya ga cewa ba ya kaiwa ko’ina, sai ma hargitsi ne yake so yă tashi, sai ya ɗibi ruwa, ya wanke hannuwansa a gaban taron ya ce, “Ni kam, ba ruwana da alhakin jinin mutumin nan. Wannan ruwanku ne!”
- Mattiyu 27:25kusan 33 M.
Sai dukan mutane suka amsa, suka ce, “Bari alhakin jininsa yă zauna a kanmu da ’ya’yanmu!”
- Mattiyu 27:26kusan 33 M.
Sai ya sakar musu Barabbas. Amma ya sa aka yi wa Yesu bulala, sa’an nan ya ba da shi a gicciye.
- Mattiyu 27:27kusan 33 M.
Sai sojojin gwamna suka ɗauki Yesu suka kai shi Fadar mai mulki, sa’an nan suka tara dukan kamfanin sojoji kewaye da shi.
- Mattiyu 27:28kusan 33 M.
Suka tuɓe shi, suka yafa masa wata jar riga.
- Mattiyu 27:29kusan 33 M.
Suka kuma tuƙa wani rawanin ƙaya, suka sa masa a kā. Suka sa sanda a hannun damansa. Suka durƙusa a gabansa, suka yi masa ba’a, suna cewa, “Ranka yă daɗe sarkin Yahudawa!”
- Mattiyu 27:30kusan 33 M.
Suka tattofa masa miyau, suka karɓe sandan, suka yi ta ƙwala masa shi a kai.
- Mattiyu 27:31kusan 33 M.
Bayan sun yi masa ba’a, sai suka tuɓe masa rigar, suka sa masa nasa tufafin. Sai suka tafi da shi, domin su gicciye shi.
- Mattiyu 27:32kusan 33 M.
Suna fitowa ke nan, sai suka sadu da wani mutumin Sairin, mai suna Siman. Sai suka tilasta shi ya ɗauki gicciyen.
- Mattiyu 27:33kusan 33 M.
Sai suka iso wani wurin da ake kira Golgota (wanda yake nufin Wurin Ƙoƙon Kai).
- Mattiyu 27:34kusan 33 M.
A can, suka ba shi ruwan inabi gauraye da wani abu mai ɗaci yă sha. Amma da ya ɗanɗana, sai ya ƙi sha.
- Mattiyu 27:35kusan 33 M.
Bayan da suka gicciye shi, sai suka raba tufafinsa a tsakaninsu ta wurin jefa ƙuri’a.
- Mattiyu 27:36kusan 33 M.
Sa’an nan suka zauna suna tsaronsa.
- Mattiyu 27:37kusan 33 M.
Bisa da kansa kuwa, an kafa rubutun zargin da aka yi masa, da ya ce, Wannan shi ne Yesu Sarkin Yahudawa.
- Mattiyu 27:38kusan 33 M.
An gicciye ’yan fashi biyu tare da shi, ɗaya a damansa, ɗaya kuma a hagunsa.
- Mattiyu 27:39kusan 33 M.
Masu wucewa, suka zazzage shi, suna kaɗa kai,
- Mattiyu 27:40kusan 33 M.
suna cewa, “Kai da za ka rushe haikali, ka kuma gina shi cikin kwana uku, ceci kanka mana! In kai Ɗan Allah ne, ka sauka daga gicciyen!”