Tsallake zuwa abun ciki

circa 6 BC – AD 30

The Life of Jesus

The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.

3,779 ayoyi · 4 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Mattiyu 25:37kusan 33 M.

    “Sa’an nan masu adalci za su amsa masa, su ce, ‘Ubangiji, yaushe muka gan ka da yunwa muka ciyar da kai, ko da ƙishirwa muka ba ka abin sha?

  2. Mattiyu 25:38kusan 33 M.

    Yaushe kuma muka gan ka baƙo muka karɓe ka, ko cikin bukatar tufafi muka yi maka sutura?

  3. Mattiyu 25:39kusan 33 M.

    Yaushe kuma muka gan ka cikin rashin lafiya ko a kurkuku muka ziyarce ka?’

  4. Mattiyu 25:40kusan 33 M.

    “Sarkin zai amsa ya ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka yi wa ɗaya daga cikin waɗannan ’yan’uwana mafi ƙanƙanta, ni kuka yi wa.’

  5. Mattiyu 25:41kusan 33 M.

    “Sa’an nan zai ce wa waɗanda suke a hagunsa, ‘Ku rabu da ni, la’anannu, zuwa cikin madawwamiyar wutar da aka shirya don Iblis da mala’ikunsa.

  6. Mattiyu 25:42kusan 33 M.

    Gama da nake jin yunwa, ba ku ba ni abinci ba, da nake jin ƙishirwa, ba ku ba ni abin sha ba,

  7. Mattiyu 25:43kusan 33 M.

    da na yi baƙunci, ba ku karɓe ni ba, da nake bukatar tufafi, ba ku yi mini sutura ba, da na yi rashin lafiya kuma ina a kurkuku, ba ku lura da ni ba.’

  8. Mattiyu 25:44kusan 33 M.

    “Su ma za su amsa, su ce, ‘Ubangiji, yaushe muka gan ka cikin yunwa ko ƙishirwa ko baƙo ko cikin bukatar tufafi ko cikin rashin lafiya ko cikin kurkuku, ba mu taimake ka ba?’

  9. Mattiyu 25:45kusan 33 M.

    “Zai amsa, yă ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da ba ku yi wa ɗaya daga cikin waɗannan mafi ƙanƙanta ba, ba ku yi mini ba ke nan.’

  10. Mattiyu 25:46kusan 33 M.

    “Sa’an nan za su tafi cikin madawwamiyar hukunci, amma masu adalci kuwa za su shiga rai madawwami.”

  11. Mattiyu 26:1kusan 33 M.

    Sa’ad da Yesu ya gama faɗin dukan waɗannan abubuwa, sai ya ce wa almajiransa,

  12. Mattiyu 26:2kusan 33 M.

    “Kamar yadda kuka sani, Bikin Ƙetarewa sauran kwana biyu, za a kuma ba da Ɗan Mutum don a gicciye shi.”

  13. Mattiyu 26:3kusan 33 M.

    Sai manyan firistoci da dattawan mutane, suka taru a fadan babban firist, mai suna Kayifas,

  14. Mattiyu 26:4kusan 33 M.

    suka ƙulla shawara su kama Yesu da makirci, su kuma kashe shi.

  15. Mattiyu 26:5kusan 33 M.

    Suka ce, “Amma ba a lokacin Biki ba, don kada mutane su tā da rikici.”

  16. Mattiyu 26:6kusan 33 M.

    Yayinda Yesu yake a Betani, a gidan wani mutumin da ake kira Siman Kuturu,

  17. Mattiyu 26:7kusan 33 M.

    wata mace ta zo wurinsa da wani ɗan tulun alabasta na turaren mai tsada sosai, wanda ta zuba a kansa a lokacin da yake cin abinci.

  18. Mattiyu 26:8kusan 33 M.

    Sa’ad da almajiransa suka ga wannan, sai suka yi fushi. Suka ce, “Wannan almubazzaranci fa!

  19. Mattiyu 26:9kusan 33 M.

    Wannan turare ai, da an sayar da shi da kuɗi mai yawa a ba matalauta kuɗin.”

  20. Mattiyu 26:10kusan 33 M.

    Sane da wannan, Yesu ya ce musu, “Me ya sa kuke damun macen nan? Ta yi mini abu mai kyau ne.

  21. Mattiyu 26:11kusan 33 M.

    Matalauta za su kasance tare da ku kullum, amma ni ba zan kasance tare da ku kullum ba.

  22. Mattiyu 26:12kusan 33 M.

    Sa’ad da ta zuba turaren nan a jikina, ta shirya ni ne don jana’izata.

  23. Mattiyu 26:13kusan 33 M.

    Gaskiya nake gaya muku, duk inda aka yi wa’azin bisharan nan a duniya duka, abin da matan nan ta yi, za a riƙa faɗarsa don tunawa da ita.”

  24. Mattiyu 26:14kusan 33 M.

    Sai ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, wanda ake kira Yahuda Iskariyot, ya je wurin manyan firistoci

  25. Mattiyu 26:15kusan 33 M.

    ya ce, “Me za ku ba ni, in na bashe shi gare ku?” Sai suka ƙirga masa kuɗi azurfa talatin.