Tsallake zuwa abun ciki

circa 6 BC – AD 30

The Life of Jesus

The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.

3,779 ayoyi · 4 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Mattiyu 24:38kusan 33 M.

    Gama a kwanaki kafin ruwan tsufana, mutane sun yi ta ci, sun kuma yi ta sha, suna aure, suna kuma aurarwa, har zuwa ranar da Nuhu ya shiga jirgi;

  2. Mattiyu 24:39kusan 33 M.

    ba su kuwa san abin da yake faruwa ba sai da ruwan tsufana ya zo ya share su tas. Haka zai zama a dawowar Ɗan Mutum.

  3. Mattiyu 24:40kusan 33 M.

    Maza biyu za su kasance a gona; za a ɗau ɗaya a bar ɗaya.

  4. Mattiyu 24:41kusan 33 M.

    Mata biyu za su kasance suna niƙa; za a ɗau ɗaya a bar ɗaya.

  5. Mattiyu 24:42kusan 33 M.

    “Saboda haka sai ku zauna a faɗake, gama ba ku san a wace rana ce Ubangijinku zai zo ba.

  6. Mattiyu 24:43kusan 33 M.

    Ku dai gane wannan, da maigida ya san ko a wane lokaci ne da dare, ɓarawo zai zo, da sai yă zauna a faɗake yă kuma hana a shiga masa gida.

  7. Mattiyu 24:44kusan 33 M.

    Saboda haka ku ma, sai ku zauna a faɗake, domin Ɗan Mutum zai zo a sa’ar da ba ku za tă ba.

  8. Mattiyu 24:45kusan 33 M.

    “Wane ne bawan nan mai aminci da kuma mai hikima, wanda maigida ya sa yă lura da bayi a cikin gidansa, yă riƙa ba su abinci a daidai lokaci?

  9. Mattiyu 24:46kusan 33 M.

    Zai zama wa bawan nan da kyau in maigidan ya dawo ya same shi yana yin haka.

  10. Mattiyu 24:47kusan 33 M.

    Gaskiya nake gaya muku, zai sa shi yă lura da dukan dukiyarsa.

  11. Mattiyu 24:48kusan 33 M.

    Amma in wannan bawa mugu ne, ya kuma ce a ransa, ‘Maigidana ba zai dawo da wuri ba.’

  12. Mattiyu 24:49kusan 33 M.

    Sa’an nan yă fara dūkan ’yan’uwansa bayi, yana ci yana kuma sha tare da mashaya.

  13. Mattiyu 24:50kusan 33 M.

    Maigidan wannan bawa zai dawo a ranar da bai yi tsammani ba, a sa’ar kuma da bai sani ba.

  14. Mattiyu 24:51kusan 33 M.

    Maigidan zai farfasa masa jiki da bulala, yă kuma ba shi wuri tare da munafukai, inda za a yi kuka da cizon haƙora.

  15. Mattiyu 25:1kusan 33 M.

    “A lokacin mulkin sama zai zama kamar budurwai goma waɗanda suka ɗauki fitilunsu suka fita don su taryi ango.

  16. Mattiyu 25:2kusan 33 M.

    Biyar daga cikinsu wawaye ne, biyar kuma masu hikima.

  17. Mattiyu 25:3kusan 33 M.

    Wawayen sun ɗauki fitilunsu, sai dai ba su riƙe mai ba.

  18. Mattiyu 25:4kusan 33 M.

    Masu hikimar kuwa suka riƙo tulunan mai da fitilunsu.

  19. Mattiyu 25:5kusan 33 M.

    Ango ya yi jinkirin zuwa, sai duk suka shiga gyangyaɗi har barci ya kwashe su.

  20. Mattiyu 25:6kusan 33 M.

    “Can tsakar dare, sai aka ji kira, ana cewa, ‘Ga ango nan! Ku fito, ku tarye shi!’

  21. Mattiyu 25:7kusan 33 M.

    “Sai dukan budurwan nan suka farka suka kuna fitilunsu.

  22. Mattiyu 25:8kusan 33 M.

    Sai wawayen suka ce wa masu hikimar, ‘Ku ɗan sassam mana manku; fitilunmu suna mutuwa.’

  23. Mattiyu 25:9kusan 33 M.

    “Su kuwa suka amsa, suka ce, ‘A’a, wataƙila ba zai ishe mu da ku ba. Gara ku je wurin masu sayarwa ku sayo.’

  24. Mattiyu 25:10kusan 33 M.

    “Amma yayinda suke kan tafiya garin sayen mai, sai ango ya iso. Budurwai da suke a shirye, suka shiga wajen bikin auren tare da shi. Aka kuma kulle ƙofa.

  25. Mattiyu 25:11kusan 33 M.

    “An jima can, sai ga sauran sun iso. Suka ce, ‘Ranka yă daɗe! Ranka yă daɗe! Ka buɗe mana ƙofa!’