circa 6 BC – AD 30
The Life of Jesus
The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Mattiyu 24:13kusan 33 M.
amma duk wanda ya tsaya da ƙarfi har ƙarshe, zai sami ceto.
- Mattiyu 24:14kusan 33 M.
Za a kuma yi wa’azin wannan bisharar mulki a cikin dukan duniya, yă zama shaida ga dukan al’ummai, sa’an nan ƙarshen yă zo.
- Mattiyu 24:15kusan 33 M.
“Saboda haka sa’ad da kuka ga ‘abin ƙyama mai kawo hallaka,’wanda annabi Daniyel ya yi magana a kai, yana tsaye a tsattsarkan wuri (mai karatu yă gane),
- Mattiyu 24:16kusan 33 M.
to, sai waɗanda suke cikin Yahudiya, su gudu zuwa cikin duwatsu.
- Mattiyu 24:17kusan 33 M.
Kada wani da yake a kan rufin gidansa, yă sauko don ɗaukar wani abu a gida.
- Mattiyu 24:18kusan 33 M.
Kada wani da yake gona kuma yă komo don ɗaukar rigarsa.
- Mattiyu 24:19kusan 33 M.
Kaiton mata masu ciki da mata masu renon ’ya’ya a waɗancan kwanakin!
- Mattiyu 24:20kusan 33 M.
Ku yi addu’a, kada gudunku yă zama a lokacin sanyi ko a ranar Asabbaci.
- Mattiyu 24:21kusan 33 M.
Gama a lokacin za a yi wata matsananciyar wahala, wadda ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har ya zuwa yanzu ba kuwa za a ƙara yi ba.
- Mattiyu 24:22kusan 33 M.
“Da ba don an taƙaita kwanakin nan ba, da babu wani da zai tsira, amma saboda zaɓaɓɓun nan, za a taƙaita kwanakin.
- Mattiyu 24:23kusan 33 M.
A lokacin in wani ya ce muku, ‘Duba, ga Kiristi nan!’ Ko, ‘Ga shi can!’ Kada ku gaskata.
- Mattiyu 24:24kusan 33 M.
Gama Kiristi masu yawa na ƙarya, da annabawan ƙarya za su firfito, su kuma aikata manyan alamu da ayyukan banmamaki don su ruɗi har da zaɓaɓɓu ma in zai yiwu.
- Mattiyu 24:25kusan 33 M.
Ga shi, na faɗa muku tun da wuri.
- Mattiyu 24:26kusan 33 M.
“Saboda haka in wani ya ce muku, ‘Ga shi can a hamada,’ kada ku fita; ko, ‘Ga shi nan a ɗakunan ciki,’ kada ku gaskata.
- Mattiyu 24:27kusan 33 M.
Gama kamar yadda walƙiya take wulgawa walai daga gabas zuwa yamma, haka dawowar Ɗan Mutum zai kasance.
- Mattiyu 24:28kusan 33 M.
Duk inda mushe yake, can ungulai za su taru.
- Mattiyu 24:29kusan 33 M.
“Nan da nan bayan tsabar wahalan nan “ ‘sai a duhunta rana, wata kuma ba zai ba da haskensa ba; taurari kuma za su fāffāɗi daga sararin sama, za a kuma girgiza abubuwan sararin sama.’
- Mattiyu 24:30kusan 33 M.
“A sa’an nan ne alamar dawowar Ɗan Mutum zai bayyana a sararin sama, dukan al’umman duniya kuwa za su yi kuka. Za su ga Ɗan Mutum yana zuwa kan gizagizan sararin sama, da iko da kuma ɗaukaka mai girma.
- Mattiyu 24:31kusan 33 M.
Zai kuwa aiki mala’ikunsa su busa ƙaho mai ƙara sosai, za su kuwa tattaro zaɓaɓɓunsa daga kusurwoyi huɗun nan, daga wannan bangon duniya zuwa wancan.
- Mattiyu 24:32kusan 33 M.
“Yanzu fa, sai ku koyi wannan darasi daga itacen ɓaure. Da zarar rassansa suka yi taushi ganyayensa kuma suka toho, kun san damina ta kusa.
- Mattiyu 24:33kusan 33 M.
Haka kuma, sa’ad da kun ga dukan waɗannan abubuwa, ku sani ya yi kusan zuwa, yana ma dab da bakin ƙofa.
- Mattiyu 24:34kusan 33 M.
Gaskiya nake gaya muku, wannan zamani ba zai shuɗe ba sai dukan abubuwan nan sun faru.
- Mattiyu 24:35kusan 33 M.
Sama da ƙasa za su shuɗe, amma maganata ba za tă taɓa shuɗe ba.
- Mattiyu 24:36kusan 33 M.
“Babu wanda ya san wannan rana ko sa’a, ko mala’ikun da suke sama ma, ko Ɗan, sai dai Uban kaɗai.
- Mattiyu 24:37kusan 33 M.
Kamar yadda ya faru a zamanin Nuhu, haka zai zama a dawowar Ɗan Mutum.