circa 6 BC – AD 30
The Life of Jesus
The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Mattiyu 25:12kusan 33 M.
“Amma ya amsa ya ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, ban san ku ba.’
- Mattiyu 25:13kusan 33 M.
“Saboda haka sai ku zauna a faɗake, don ba ku san ranar ko sa’ar ba.
- Mattiyu 25:14kusan 33 M.
“Har wa yau, za a kwatanta shi da mutumin da zai yi tafiya, wanda ya kira bayinsa ya kuma danƙa musu mallakarsa.
- Mattiyu 25:15kusan 33 M.
Ga guda, ya ba shi talenti biyar na kuɗi, ga wani talenti biyu, ga wani kuma talenti ɗaya, kowa bisa ga azancinsa. Sa’an nan ya yi tafiyarsa.
- Mattiyu 25:16kusan 33 M.
Mutumin da ya karɓi talenti biyar, nan da nan ya tafi ya yi kasuwanci da su har ya sami ribar talenti biyar.
- Mattiyu 25:17kusan 33 M.
Haka ma, wannan mai talenti biyu, shi ma ya yi riba biyu.
- Mattiyu 25:18kusan 33 M.
Amma mutumin da ya karɓi talenti ɗaya ɗin, ya tafi, ya tona rami, ya ɓoye kuɗin maigidansa.
- Mattiyu 25:19kusan 33 M.
“Bayan an daɗe, sai maigidan bayin nan ya dawo, ya kuma daidaita lissafi da su.
- Mattiyu 25:20kusan 33 M.
Mutumin da ya karɓi talenti biyar, ya kawo ƙarin talenti biyar. Ya ce, ‘Maigida, ka danƙa mini talenti biyar. Ga shi, na yi ribar biyar.’
- Mattiyu 25:21kusan 33 M.
“Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan abubuwa kaɗan, zan sa ka lura da abubuwa masu yawa. Zo ka yi farin ciki tare da maigidanka!’
- Mattiyu 25:22kusan 33 M.
“Mutumin da yake da talenti biyu, shi ma ya zo ya ce, ‘Maigida, ka danƙa mini talenti biyu; ga shi, na yi ribar biyu.’
- Mattiyu 25:23kusan 33 M.
“Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan abubuwa kaɗan, zan sa ka lura da abubuwa masu yawa. Zo ka yi farin ciki tare da maigidanka!’
- Mattiyu 25:24kusan 33 M.
“Sa’an nan mutumin da ya karɓi talenti ɗaya ya zo. Ya ce, ‘Maigida, na san cewa kai mutum ne mai wuyan sha’ani, kana girbi inda ba ka shuka ba, kana kuma tara inda ba ka yafa iri ba.
- Mattiyu 25:25kusan 33 M.
Saboda haka na ji tsoro, na je na ɓoye talentinka a ƙasa. Ga abinka.’
- Mattiyu 25:26kusan 33 M.
“Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Kai mugun bawa, mai ƙyuya! Ashe, ka san cewa ina girbi inda ban yi shuka ba, ina kuma tarawa inda ban yafa iri ba?
- Mattiyu 25:27kusan 33 M.
To, in haka ne, ai, da ka sa kuɗina a banki, don sa’ad da na dawo da na karɓi abina da riba.
- Mattiyu 25:28kusan 33 M.
“ ‘Karɓi talentin daga hannunsa ku ba wanda yake da talenti goma.
- Mattiyu 25:29kusan 33 M.
Gama duk mai abu za a ƙara masa, zai kuma same shi a yawalce. Duk wanda ba shi da shi kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai an karɓe masa.
- Mattiyu 25:30kusan 33 M.
Ku jefar da banzan bawan nan waje, cikin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.’
- Mattiyu 25:31kusan 33 M.
“Sa’ad da Ɗan Mutum ya zo cikin ɗaukakarsa, tare da dukan mala’iku, zai zauna a kursiyinsa cikin ɗaukakar sama.
- Mattiyu 25:32kusan 33 M.
Za a tara dukan al’ummai a gabansa, zai kuma raba mutane dabam-dabam yadda makiyayi yakan ware tumaki daga awaki.
- Mattiyu 25:33kusan 33 M.
Zai sa tumaki a damansa, awaki kuma a hagunsa.
- Mattiyu 25:34kusan 33 M.
“Sa’an nan Sarki zai ce wa waɗanda suke damansa, ‘Ku zo, ku da Ubana ya yi wa albarka; ku karɓi gādonku, mulkin da aka shirya muku tun halittar duniya.
- Mattiyu 25:35kusan 33 M.
Gama da nake jin yunwa, kun ciyar da ni, da nake jin ƙishirwa, kun ba ni abin sha, da nake baƙunci, kun karɓe ni,
- Mattiyu 25:36kusan 33 M.
da nake bukatar tufafi, kun yi mini sutura, da na yi rashin lafiya, kun lura da ni, da nake kurkuku, kun ziyarce ni.’