Tsallake zuwa abun ciki

circa 6 BC – AD 30

The Life of Jesus

The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.

3,779 ayoyi · 4 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Mattiyu 23:27kusan 33 M.

    “Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kuna kama da kaburburan da aka shafa musu farin fenti, waɗanda suna da kyan gani a waje, amma a ciki, cike suke da ƙasusuwan matattu da kuma kowane irin abu mai ƙazanta.

  2. Mattiyu 23:28kusan 33 M.

    Haka ku ma, a waje, a idon mutane, ku masu adalci ne, amma a ciki, cike kuke da munafunci da mugunta.

  3. Mattiyu 23:29kusan 33 M.

    “Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan gina kaburbura don annabawa, ku kuma yi wa kaburburan mutane masu adalci ado.

  4. Mattiyu 23:30kusan 33 M.

    Kuna cewa, ‘Da mun kasance a zamanin kakanninmu, ai, da ba mu haɗa hannu da su muka karkashe annabawa ba.’

  5. Mattiyu 23:31kusan 33 M.

    Ta haka kuna ba da shaida a kanku cewa ku zuriyar waɗanda suka karkashe annabawa ne.

  6. Mattiyu 23:32kusan 33 M.

    To, sai ku ci gaba ku cikasa ayyukan da kakanninku suka fara!

  7. Mattiyu 23:33kusan 33 M.

    “Ku macizai! ’Ya’yan macizai! Ta yaya za ku tsere wa hukuncin jahannama ta wuta?

  8. Mattiyu 23:34kusan 33 M.

    Saboda haka ina aika muku da annabawa, da masu hikima da malamai. Waɗansunsu za ku kashe ku kuma gicciye; waɗansu kuma za ku yi musu bulala a majami’unku kuna kuma binsu gari-gari.

  9. Mattiyu 23:35kusan 33 M.

    Ta haka alhakin jinin masu adalcin da aka zubar a duniya, tun daga jinin Habila mai adalci, zuwa jinin Zakariya ɗan Berekiya, wanda kuka kashe tsakanin haikali da bagade zai koma kanku.

  10. Mattiyu 23:36kusan 33 M.

    Gaskiya nake gaya muku, duk wannan zai auko wa wannan zamani.

  11. Mattiyu 23:37kusan 33 M.

    “Urushalima, ayya Urushalima, ke da kike kashe annabawa, kike kuma jifan waɗanda aka aiko gare ki, sau da sau na so in tattara ’ya’yanki wuri ɗaya, yadda kaza takan tattara ’ya’yanta cikin fikafikanta, amma kuka ƙi.

  12. Mattiyu 23:38kusan 33 M.

    Ga shi, an bar muku gidanku a yashe.

  13. Mattiyu 23:39kusan 33 M.

    Gama ina gaya muku, ba za ku sāke ganina ba sai kun ce, ‘Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji.’ ”

  14. Mattiyu 24:1kusan 33 M.

    Yesu ya bar haikali ke nan, yana cikin tafiya sai almajiransa suka zo wurinsa don su ja hankalinsa ga gine-ginen haikali.

  15. Mattiyu 24:2kusan 33 M.

    Sai Yesu ya ce, “Kun ga duk waɗannan abubuwa? Gaskiya nake gaya muku, ba wani dutse a nan da za a bari a kan wani; duk za a rushe.”

  16. Mattiyu 24:3kusan 33 M.

    Da Yesu yana zaune a Dutsen Zaitun, almajiran suka zo wurinsa a ɓoye. Suka ce, “Gaya mana, yaushe ne wannan zai faru, mece ce alamar zuwanka da kuma ta ƙarshen zamani?”

  17. Mattiyu 24:4kusan 33 M.

    Yesu ya amsa, “Ku lura fa, kada wani yă ruɗe ku.

  18. Mattiyu 24:5kusan 33 M.

    Gama mutane da yawa za su zo cikin sunana, suna cewa, ‘Ni ne Kiristi,’ za su kuwa ruɗi mutane da yawa.

  19. Mattiyu 24:6kusan 33 M.

    Za ku ji labarin yaƙe-yaƙe da kuma jita-jitarsu, sai dai ku lura kada hankalinku yă tashi. Dole irin waɗannan abubuwa su faru, amma ƙarshen tukuna.

  20. Mattiyu 24:7kusan 33 M.

    Al’umma za tă tasar wa al’umma, mulki yă tasar wa mulki. Za a yi yunwa da girgizar ƙasa a wurare dabam-dabam.

  21. Mattiyu 24:8kusan 33 M.

    Dukan waɗannan fa, mafarin azabar naƙudar haihuwa ne.

  22. Mattiyu 24:9kusan 33 M.

    “Sa’an nan za a bashe ku don a tsananta muku a kuma kashe ku, dukan al’ummai za su ƙi ku saboda ni.

  23. Mattiyu 24:10kusan 33 M.

    A wannan lokaci, da yawa za su juya daga bangaskiya, su ci amana su kuma ƙi juna,

  24. Mattiyu 24:11kusan 33 M.

    annabawan ƙarya da yawa za su firfito su kuma ruɗi mutane da yawa.

  25. Mattiyu 24:12kusan 33 M.

    Saboda ƙaruwar mugunta, ƙaunar yawanci za tă yi sanyi,