Tsallake zuwa abun ciki

circa 6 BC – AD 30

The Life of Jesus

The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.

3,779 ayoyi · 4 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Mattiyu 22:23kusan 33 M.

    A ranan nan Sadukiyawa, waɗanda suke cewa babu tashin matattu, suka zo wurinsa da tambaya.

  2. Mattiyu 22:24kusan 33 M.

    Suka ce “Malam, Musa ya faɗa mana cewa in mutum ya mutu ba shi da ’ya’ya, dole ɗan’uwansa yă auri gwauruwar yă kuma haifar wa ɗan’uwan ’ya’ya.

  3. Mattiyu 22:25kusan 33 M.

    A cikinmu an yi ’yan’uwa guda bakwai. Na fari ya yi aure, ya mutu, da yake bai sami ’ya’ya ba, sai ya bar matarsa wa ɗan’uwansa.

  4. Mattiyu 22:26kusan 33 M.

    Haka ya faru da ɗan’uwa na biyu da na uku, har zuwa na bakwai.

  5. Mattiyu 22:27kusan 33 M.

    A ƙarshe, macen ta mutu.

  6. Mattiyu 22:28kusan 33 M.

    To, a tashin matattu, matar wa a cikinsu bakwai ɗin nan za tă zama, da yake dukansu sun aure ta?”

  7. Mattiyu 22:29kusan 33 M.

    Yesu ya amsa ya ce, “Kun ɓata, domin ba ku san Nassi ko ikon Allah ba.

  8. Mattiyu 22:30kusan 33 M.

    Ai, a tashin matattu, mutane ba za su yi aure ko su ba da aure ba; za su zama kamar mala’iku a sama.

  9. Mattiyu 22:31kusan 33 M.

    Amma game da tashi daga matattu na waɗanda suka mutu ba ku karanta abin da Allah ya ce muku ba ne,

  10. Mattiyu 22:32kusan 33 M.

    ‘Ni ne Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub’? Ai, shi ba Allah na matattu ba ne, shi Allah na masu rai ne.”

  11. Mattiyu 22:33kusan 33 M.

    Da taro suka ji haka, sai suka yi mamakin koyarwarsa.

  12. Mattiyu 22:34kusan 33 M.

    Da jin Yesu ya ƙure Sadukiyawa, sai Farisiyawa suka tattaru.

  13. Mattiyu 22:35kusan 33 M.

    Ɗaya daga cikinsu, wani masanin Doka, ya gwada shi da wannan tambaya.

  14. Mattiyu 22:36kusan 33 M.

    “Malam, wace doka ce mafi girma a cikin dokoki?”

  15. Mattiyu 22:37kusan 33 M.

    Yesu ya amsa ya ce, “ ‘Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka da dukan ranka da kuma dukan hankalinka.’

  16. Mattiyu 22:38kusan 33 M.

    Wannan, ita ce doka ta fari da kuma mafi girma.

  17. Mattiyu 22:39kusan 33 M.

    Ta biye kuma kamar ta farkon take. ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’

  18. Mattiyu 22:40kusan 33 M.

    Dukan Doka da Annabawa suna rataya ne a kan waɗannan dokoki biyu.”

  19. Mattiyu 22:41kusan 33 M.

    Yayinda Farisiyawa suke a tattare wuri ɗaya, sai Yesu ya tambaye su,

  20. Mattiyu 22:42kusan 33 M.

    “Me kuke tsammani game da Kiristi? Ɗan wane ne shi?” Suka amsa suka ce, “Ɗan Dawuda.”

  21. Mattiyu 22:43kusan 33 M.

    Ya ce musu, “To, ta yaya Dawuda ya yi magana ta wurin Ruhu Mai Tsarki, ya kira shi ‘Ubangiji’? Gama ya ce,

  22. Mattiyu 22:44kusan 33 M.

    “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana, sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka.” ’

  23. Mattiyu 22:45kusan 33 M.

    To, in Dawuda ya kira shi ‘Ubangiji,’ yaya zai zama ɗansa?”

  24. Mattiyu 22:46kusan 33 M.

    Ba wanda ya iya tanka masa, daga wannan rana kuwa ba wanda ya sāke yin karambanin yin masa wata tambaya.

  25. Mattiyu 23:1kusan 33 M.

    Sa’an nan Yesu ya ce wa taron mutane da kuma almajiransa,