Tsallake zuwa abun ciki

circa 6 BC – AD 30

The Life of Jesus

The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.

3,779 ayoyi · 4 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Mattiyu 21:44kusan 33 M.

    Duk wanda ya fāɗi a kan dutsen nan, zai kakkarye. Amma duk wanda dutsen nan ya fāɗi a kansa, za a murƙushe shi.”

  2. Mattiyu 21:45kusan 33 M.

    Da manyan firistoci da Farisiyawa suka ji misalan Yesu, sai suka gane cewa da su yake.

  3. Mattiyu 21:46kusan 33 M.

    Suka nemi hanyar kama shi, amma suka ji tsoron taron, don mutane sun ɗauka shi annabi ne.

  4. Mattiyu 22:1kusan 33 M.

    Yesu ya sāke yin musu magana da misalai, yana cewa,

  5. Mattiyu 22:2kusan 33 M.

    “Mulkin sama yana kama da wani sarki wanda ya shirya bikin auren ɗansa.

  6. Mattiyu 22:3kusan 33 M.

    Sai ya aiki bayinsa su kira waɗanda aka gayyata zuwa bikin, amma waɗanda aka ce su zo bikin, suka ƙi zuwa.

  7. Mattiyu 22:4kusan 33 M.

    “Sai ya sāke aiken waɗansu bayi ya ce, ‘Ku ce wa waɗanda aka gayyata cewa na shirya abinci. An yanka bijimai da shanun da aka yi kiwo, kome a shirye yake. Ku zo bikin auren mana.’

  8. Mattiyu 22:5kusan 33 M.

    “Amma ba su kula ba, suka kama gabansu, ɗaya ya tafi gonarsa, ɗaya kuma ya tafi kasuwancinsa.

  9. Mattiyu 22:6kusan 33 M.

    Sauran suka kama bayinsa suka wulaƙanta su, suka kuma kashe su.

  10. Mattiyu 22:7kusan 33 M.

    Sai sarkin ya yi fushi. Ya aiki mayaƙansa suka karkashe masu kisankan nan, aka kuma ƙone birninsu.

  11. Mattiyu 22:8kusan 33 M.

    “Sa’an nan ya ce wa bayinsa, ‘Bikin aure fa ya shiryu, sai dai mutanen da na gayyata ba su dace ba.

  12. Mattiyu 22:9kusan 33 M.

    Ku bi titi-titi ku gayyato duk waɗanda kuka gani, su zo bikin.’

  13. Mattiyu 22:10kusan 33 M.

    Saboda haka bayin suka bi titi-titi, suka tattaro duk mutanen da suka samu, masu kirki da marasa kirki, zauren bikin ya cika makil da baƙi.

  14. Mattiyu 22:11kusan 33 M.

    “Amma da sarkin ya shigo don yă ga baƙin, sai ya ga wani can da ba ya sanye da kayan auren.

  15. Mattiyu 22:12kusan 33 M.

    Ya yi tambaya ya ce, ‘Aboki, yaya ka shigo nan ba tare da rigar aure ba?’ Mutumin ya rasa ta cewa.

  16. Mattiyu 22:13kusan 33 M.

    “Sai sarkin ya ce wa fadawa, ‘Ku daure shi hannu da ƙafa, ku jefar da shi waje, cikin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.’

  17. Mattiyu 22:14kusan 33 M.

    “Gama kirayayu da yawa, amma zaɓaɓɓu kaɗan ne zaɓaɓɓu.”

  18. Mattiyu 22:15kusan 33 M.

    Sai Farisiyawa suka yi waje, suka ƙulla yadda za su yi masa tarko cikin maganarsa.

  19. Mattiyu 22:16kusan 33 M.

    Suka aiki almajiransu tare da mutanen Hiridus wurinsa. Suka ce, “Malam, mun san kai mutum ne mai mutunci, kuma kana koyar da maganar Allah bisa gaskiya. Mutane ba sa ɗaukan hankalinka, domin ba ka kula ko su wane ne ba.

  20. Mattiyu 22:17kusan 33 M.

    To, ka gaya mana, a ra’ayinka? Ya dace a biya Kaisar haraji ko a’a?”

  21. Mattiyu 22:18kusan 33 M.

    Amma Yesu da yake ya san mugun nufinsu, sai ya ce, “Ku munafukai, don me kuke ƙoƙarin sa mini tarko?

  22. Mattiyu 22:19kusan 33 M.

    Ku nuna mini kuɗin da ake biyan haraji da shi.” Sai suka kawo masa dinari,

  23. Mattiyu 22:20kusan 33 M.

    sai ya tambaye su ya ce, “Hoton wane ne wannan? Kuma rubutun wane ne?”

  24. Mattiyu 22:21kusan 33 M.

    Suka amsa, “Na Kaisar ne.” Sai ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba wa Allah abin da yake na Allah.”

  25. Mattiyu 22:22kusan 33 M.

    Da suka ji haka, sai suka yi mamaki. Saboda haka suka ƙyale shi, suka yi tafiyarsu.