Tsallake zuwa abun ciki

circa 6 BC – AD 30

The Life of Jesus

The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.

3,779 ayoyi · 4 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Mattiyu 20:28kusan 33 M.

    kamar yadda Ɗan Mutum bai zo don a bauta masa ba, sai dai don yă yi bauta, yă kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”

  2. Mattiyu 20:29kusan 33 M.

    Sa’ad da Yesu da almajiransa suke barin Yeriko, sai wani babban taro ya bi shi.

  3. Mattiyu 20:30kusan 33 M.

    Makafi biyu kuwa suna zaune a bakin hanya, da suka ji cewa Yesu yana wucewa, sai suka ɗaga murya suka ce, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu!”

  4. Mattiyu 20:31kusan 33 M.

    Mutane suka tsawata musu, suka ce musu su yi shiru. Sai suka ƙara ɗaga murya suna cewa, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu!”

  5. Mattiyu 20:32kusan 33 M.

    Yesu ya tsaya ya kira su. Ya tambaye su, “Me kuke so in yi muku?”

  6. Mattiyu 20:33kusan 33 M.

    Suka amsa suka ce, “Ubangiji, muna so mu sami ganin gari.”

  7. Mattiyu 20:34kusan 33 M.

    Sai Yesu ya ji tausayinsu, ya taɓa idanunsu. Nan da nan kuwa suka sami ganin gari, suka kuma bi shi.

  8. Mattiyu 21:1kusan 33 M.

    Da suka yi kusa da Urushalima suka kuma kai Betfaji da yake kan Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki almajirai biyu,

  9. Mattiyu 21:2kusan 33 M.

    yana ce musu, “Ku je ƙauyen da yake gabanku, nan take za ku ga wata jaka a daure tare da ɗanta kusa da ita, a can. Ku kunce su ku kawo mini.

  10. Mattiyu 21:3kusan 33 M.

    In wani ya yi muku wata magana, ku ce masa Ubangiji yana bukatarsu, zai kuwa mai da su nan da nan.”

  11. Mattiyu 21:4kusan 33 M.

    Wannan ya faru ne don a cika abin da aka faɗa ta bakin annabin cewa,

  12. Mattiyu 21:5kusan 33 M.

    “Ku ce wa Diyar Sihiyona, ‘Duba, sarkinki yana zuwa gare ki, mai tawali’u yana a kan jaki, a kan aholaki, ɗan jaki.’ ”

  13. Mattiyu 21:6kusan 33 M.

    Almajiran suka tafi suka yi kamar yadda Yesu ya umarce su.

  14. Mattiyu 21:7kusan 33 M.

    Suka kawo jakar da ɗanta, suka shimfiɗa mayafansu a kansu, Yesu kuma ya zauna a kansu.

  15. Mattiyu 21:8kusan 33 M.

    Wani babban taron mutane suka shimfiɗa mayafansu a kan hanya, yayinda waɗansu suka sassari rassan itatuwa suka shisshimfiɗa a kan hanya.

  16. Mattiyu 21:9kusan 33 M.

    Taron mutanen da suke gabansa da kuma waɗanda suke binsa a baya suka yi ihu suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda!” “Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!” “Hosanna a cikin sama!”

  17. Mattiyu 21:10kusan 33 M.

    Sa’ad da Yesu ya shiga Urushalima, dukan birnin ya ruɗe, ana ta tambaya, “Wane ne wannan?”

  18. Mattiyu 21:11kusan 33 M.

    Taron mutane suka amsa, “Wannan shi ne Yesu, annabin nan daga Nazaret a Galili.”

  19. Mattiyu 21:12kusan 33 M.

    Yesu ya shiga filin haikali, ya kuma kori duk masu saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur masu canjin kuɗi da kuma kujerun masu sayar da tattabarai.

  20. Mattiyu 21:13kusan 33 M.

    Ya ce musu, “A rubuce yake, ‘Za a ce da gidana, gidan addu’a,’amma kuna mai da shi ‘kogon ’yan fashi.’ ”

  21. Mattiyu 21:14kusan 33 M.

    Makafi da guragu suka zo wurinsa a haikali, ya kuwa warkar da su.

  22. Mattiyu 21:15kusan 33 M.

    Amma da manyan firistoci da malaman dokoki suka ga abubuwan banmamakin da ya yi, yara kuma suna ihu a filin haikali suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda,” sai fushi ya kama su.

  23. Mattiyu 21:16kusan 33 M.

    Suka tambaye shi suka ce, “Kana jin abin da waɗannan suke faɗa?” Yesu ya amsa ya ce, “I, ba ku taɓa karanta ba cewa, “ ‘Daga leɓunan yara da jarirai kai, Ubangiji, ka shirya wa kanka yabo’?”

  24. Mattiyu 21:17kusan 33 M.

    Sai ya bar su, ya fita daga birnin ya tafi Betani, inda ya kwana.

  25. Mattiyu 21:18kusan 33 M.

    Kashegari da sassafe, yayinda yake kan hanyarsa ta komawa cikin birni, sai ya ji yunwa.