circa 6 BC – AD 30
The Life of Jesus
The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Mattiyu 21:19kusan 33 M.
Ganin itacen ɓaure kusa da hanya, sai ya je wajensa amma bai sami kome a kansa ba sai ganye. Sai ya ce masa, “Kada ka ƙara yin ’ya’ya!” Nan da nan itacen ya yanƙwane.
- Mattiyu 21:20kusan 33 M.
Sa’ad da almajiran suka ga haka, sai suka yi mamaki suna tambaya, “Yaya itacen ɓauren ya yanƙwane nan da nan haka?”
- Mattiyu 21:21kusan 33 M.
Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiya, ba kuwa da wata shakka ba, ba kawai za ku iya yin abin da aka yi wa itacen ɓauren nan ba, amma za ku ma iya ce wa dutsen nan, ‘Je ka, ka jefa kanka cikin teku,’ sai yă faru.
- Mattiyu 21:22kusan 33 M.
In kun gaskata, za ku karɓi duk abin da kuka roƙa a cikin addu’a.”
- Mattiyu 21:23kusan 33 M.
Sai Yesu ya shiga filin haikali, yayinda yake koyarwa, sai manyan firistoci da dattawan mutane suka zo wurinsa suka yi tambaya, “Da wane iko kake yin waɗannan abubuwa? Kuma wa ya ba ka wannan iko?”
- Mattiyu 21:24kusan 33 M.
Yesu ya amsa ya ce, “Ni ma zan yi muku tambaya guda. In kuka ba ni amsa, ni ma zan gaya muku ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa.
- Mattiyu 21:25kusan 33 M.
Baftismar Yohanna, daga ina ta fito? Daga sama ce, ko daga mutane?” Sai suka tattauna a junansu suka ce, “In muka ce, ‘Daga sama,’ zai ce, ‘To, me ya sa ba mu gaskata shi ba?’
- Mattiyu 21:26kusan 33 M.
In kuma muka ce, ‘Daga mutane,’ muna tsoron mutane, gama duk sun ɗauka Yohanna annabi ne.”
- Mattiyu 21:27kusan 33 M.
Saboda haka suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.” Sai ya ce, “Ni ma ba zan gaya muku ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa ba.”
- Mattiyu 21:28kusan 33 M.
“Me kuka gani? An yi wani mutum wanda yake da ’ya’ya biyu maza. Sai ya je wajen ɗan farin ya ce, ‘Ɗana, yau tafi gonar inabi ka yi aiki.’
- Mattiyu 21:29kusan 33 M.
“Ya amsa ya ce, ‘Ba zan tafi ba,’ amma daga baya ya sāke tunani, ya tafi.
- Mattiyu 21:30kusan 33 M.
“Sai mahaifin ya tafi waje na biyun ya faɗa masa iri magana guda. Sai ya amsa ya ce, ‘Zan tafi, ranka yă daɗe,’ amma bai tafi ba.
- Mattiyu 21:31kusan 33 M.
“Wanne cikin yaran nan biyu ya yi abin da mahaifinsa yake so?” Suka amsa, “Na farin.” Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, masu karɓar haraji da karuwai suna riga ku shiga mulkin Allah.
- Mattiyu 21:32kusan 33 M.
Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo wurinku don yă nuna muku hanyar adalci, ba ku gaskata shi ba, amma masu karɓar haraji da karuwai sun gaskata. Har ma bayan kun ga wannan, ba ku tuba kun gaskata shi ba.”
- Mattiyu 21:33kusan 33 M.
“Ku saurari wani misali. An yi wani mai gona wanda ya yi gonar inabi. Ya kewaye ta da katanga, ya haƙa wurin matsin inabi a ciki, ya kuma gina hasumiyar gadi. Sa’an nan ya ba wa waɗansu manoma hayar gonar inabin, ya kuma yi tafiya.
- Mattiyu 21:34kusan 33 M.
Da lokacin girbi ya yi kusa, sai ya aiki bayinsa wajen ’yan hayan, su karɓo masa ’ya’yan inabi.
- Mattiyu 21:35kusan 33 M.
“Amma ’yan hayan suka kama bayinsa; suka dūke ɗaya, suka kashe ɗaya, suka kuma jajjefi na ukun.
- Mattiyu 21:36kusan 33 M.
Sai ya sāke aiken waɗansu bayi wurinsu, fiye da na dā yawa, amma ’yan hayan suka yi musu kamar yadda suka yi wa na farin.
- Mattiyu 21:37kusan 33 M.
A ƙarshe, sai ya aiki ɗansa a wurinsu. Ya ce, ‘Za su girmama ɗana.’
- Mattiyu 21:38kusan 33 M.
“Amma da ’yan hayan suka hangi ɗan, sai suka ce wa juna, ‘Wannan shi ne magājin. Ku zo, mu kashe shi, mu ci gādonsa.’
- Mattiyu 21:39kusan 33 M.
Saboda haka suka kama shi, suka jefar da shi bayan katangar gonar inabin, suka kashe shi.
- Mattiyu 21:40kusan 33 M.
“To, idan mai gonar inabin ya zo, me zai yi da ’yan hayan nan?”
- Mattiyu 21:41kusan 33 M.
Suka amsa suka ce, “Zai yi wa banzan mutanen nan mugun kisa, yă ba da hayar gonar inabin ga waɗansu ’yan haya, waɗanda za su ba shi rabonsa na amfanin gona a lokacin girbi.”
- Mattiyu 21:42kusan 33 M.
Yesu ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karanta a cikin Nassi cewa, “ ‘Dutsen da magina suka ƙi shi ne ya zama dutsen kusurwar gini. Ubangiji ne ya aikata wannan, kuma abin mamaki ne a idanunmu’?
- Mattiyu 21:43kusan 33 M.
“Saboda haka, ina gaya muku cewa za a karɓe mulkin Allah daga gare ku, a ba wa mutanen da za su ba da amfani.