Tsallake zuwa abun ciki

circa 6 BC – AD 30

The Life of Jesus

The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.

3,779 ayoyi · 4 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Mattiyu 19:8kusan 33 M.

    Yesu ya amsa ya ce, “Musa ya ba ku izini ku saki matanku saboda taurin zuciyarku ne. Amma ba haka yake ba daga farko.

  2. Mattiyu 19:9kusan 33 M.

    Ina faɗa muku cewa duk wanda ya saki matarsa, sai dai a kan rashin aminci a cikin aure, ya kuwa auri wata, ya yi zina ke nan.”

  3. Mattiyu 19:10kusan 33 M.

    Almajiran suka ce masa, “In haka yake tsakanin miji da mata, ashe, ya ma fi kyau kada a yi aure.”

  4. Mattiyu 19:11kusan 33 M.

    Yesu ya ce, “Ba kowa ba ne zai yarda da wannan magana, sai dai waɗanda aka yarda musu.

  5. Mattiyu 19:12kusan 33 M.

    Gama waɗansu bābānni ne domin haka aka haife su; waɗansu kuwa mutane ne suka mai da su haka; waɗansu kuma sun ƙi aure ne saboda mulkin sama. Duk mai iya ɗaukar wannan yă ɗauka.”

  6. Mattiyu 19:13kusan 33 M.

    Sa’an nan aka kawo yara ƙanana wurin Yesu don yă ɗibiya musu hannuwansa, yă kuma yi musu addu’a. Amma almajirai suka tsawata wa waɗanda suka kawo su.

  7. Mattiyu 19:14kusan 33 M.

    Yesu ya ce, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su, gama mulkin sama na irin waɗannan ne.”

  8. Mattiyu 19:15kusan 33 M.

    Sa’ad da ya ɗibiya musu hannuwansa, sai ya tafi abinsa.

  9. Mattiyu 19:16kusan 33 M.

    To, fa, sai ga wani ya zo wurin Yesu ya tambaye shi ya ce, “Malam, wane abu mai kyau ne ya zama mini dole in yi don in sami rai madawwami?”

  10. Mattiyu 19:17kusan 33 M.

    Yesu ya amsa ya ce, “Don me kake tambayata game da abin da yake mai kyau? Akwai Mai kyau Ɗaya kaɗai. In kana so ka sami rai madawwami, ka kiyaye dokokin nan.”

  11. Mattiyu 19:18kusan 33 M.

    Mutumin ya yi tambaya ya ce, “Waɗanne?” Yesu ya amsa ya ce, “ ‘Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka yi shaidar ƙarya,

  12. Mattiyu 19:19kusan 33 M.

    ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’ka kuma ‘ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’”

  13. Mattiyu 19:20kusan 33 M.

    Saurayin ya ce, “Duk waɗannan na kiyaye. Me kuma ya rage mini?”

  14. Mattiyu 19:21kusan 33 M.

    Yesu ya amsa ya ce, “In kana so ka zama cikakke, ka je, ka sayar da dukan dukiyarka ka kuma ba matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Sa’an nan ka zo, ka bi ni.”

  15. Mattiyu 19:22kusan 33 M.

    Da saurayin ya ji haka, sai ya tafi rai a ɓace, don yana da arziki sosai.

  16. Mattiyu 19:23kusan 33 M.

    Sa’an nan Yesu ya ce wa almajiransa, “Gaskiya nake gaya muku, yana da wuya mai arziki yă shiga mulkin sama.

  17. Mattiyu 19:24kusan 33 M.

    Har wa yau ina gaya muku, zai fi sauƙi raƙumi yă shiga ta kafar allura, da mai arziki yă shiga mulkin Allah.”

  18. Mattiyu 19:25kusan 33 M.

    Sa’ad da almajiran suka ji wannan, sai suka yi mamaki ƙwarai. Suka yi tambaya suka ce, “To, wa zai sami ceto ke nan?”

  19. Mattiyu 19:26kusan 33 M.

    Yesu ya kalle su ya ce, “Ga mutum kam, wannan ba ya yiwuwa, amma ga Allah kuwa, dukan abubuwa masu yiwuwa ne.”

  20. Mattiyu 19:27kusan 33 M.

    Sai Bitrus ya amsa masa, “Ga shi mun bar kome don mu bi ka! Me za mu samu ke nan?”

  21. Mattiyu 19:28kusan 33 M.

    Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, a lokacin sabunta dukan kome, sa’ad da Ɗan Mutum ya zauna a kan kursiyinsa mai daraja, ku da kuka bi ni, ku ma za ku zauna a kan kursiyoyi goma sha biyu, kuna yi wa kabilu goma sha biyu na Isra’ila shari’a.

  22. Mattiyu 19:29kusan 33 M.

    Duk kuma wanda ya bar gidaje ko ’yan’uwa maza ko ’yan’uwa mata ko mahaifi ko mahaifiya ko yara ko gonaki, saboda ni, zai sami abin da ya fi haka riɓi ɗari, yă kuma gāji rai madawwami.

  23. Mattiyu 19:30kusan 33 M.

    Amma da yawa da suke na farko, za su zama na ƙarshe, da yawa kuma da suke na ƙarshe, za su zama na farko.

  24. Mattiyu 20:1kusan 33 M.

    “Mulkin sama yana kama da wani mai gona, wanda ya fita da sassafe don yă yi hayar mutane su yi aiki a gonar inabinsa.

  25. Mattiyu 20:2kusan 33 M.

    Ya yarda yă biya su dinari guda a yini, sai ya tura su gonar inabinsa.