circa 6 BC – AD 30
The Life of Jesus
The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Mattiyu 18:18kusan 32 M.
“Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka daure a duniya, za a daure a sama, duk kuma abin da kuka kunce a duniya, za a kunce shi a sama.
- Mattiyu 18:19kusan 32 M.
“Har wa yau, ina gaya muku cewa in mutum biyu a cikinku a duniya suka yarda su roƙi wani abu, Ubana da yake cikin sama zai yi muku.
- Mattiyu 18:20kusan 32 M.
Gama inda mutum biyu ko uku suka taru cikin sunana, a can ma ina tare da su.”
- Mattiyu 18:21kusan 32 M.
Sai Bitrus ya zo wurin Yesu ya yi masa tambaya ya ce, “Ubangiji, sau nawa zan yafe wa ɗan’uwana sa’ad da ya yi mini zunubi? Har sau bakwai?”
- Mattiyu 18:22kusan 32 M.
Yesu amsa ya ce, “Ina gaya maka, ba sau bakwai ba, amma sau saba’in da bakwai.
- Mattiyu 18:23kusan 32 M.
“Saboda haka, mulkin sama yana kama da wani sarki wanda ya so yă yi ƙididdigar dukiyarsa da take a hannun bayinsa.
- Mattiyu 18:24kusan 32 M.
Da ya fara ƙididdigar, sai aka kawo masa wani wanda yake bin bashin talenti dubu goma.
- Mattiyu 18:25kusan 32 M.
Da yake bai iya biya ba, sai maigida ya umarta a sayar da shi da matarsa da yaransa da kuma duk abin da yake da shi, a biya bashin.
- Mattiyu 18:26kusan 32 M.
“Bawan ya durƙusa a gabansa. Ya yi roƙo ya ce, ‘Ka yi mini haƙuri, zan biya ka ƙaf.’
- Mattiyu 18:27kusan 32 M.
Maigidan bawan ya ji tausayinsa, ya yafe masa bashin, ya kuma sake shi.
- Mattiyu 18:28kusan 32 M.
“Amma da wannan bawa ya fita, sai ya gamu da wani abokin bautarsa wanda yake binsa bashin dinari ɗari. Sai ya cafke shi, ya shaƙe shi a wuya yana cewa, ‘Biya ni abin da nake binka!’
- Mattiyu 18:29kusan 32 M.
“Wannan abokin bautarsa ya durƙusa ya roƙe shi, ‘Ka yi mini haƙuri, zan biya ka.’
- Mattiyu 18:30kusan 32 M.
“Amma ya ƙi. A maimako, sai ya je ya sa aka jefa shi a kurkuku, har yă biya bashin.
- Mattiyu 18:31kusan 32 M.
Sa’ad da sauran bayin suka ga abin da ya faru, abin ya ɓata musu rai ƙwarai, sai suka tafi suka faɗa wa maigidansu dukan abin da ya faru.
- Mattiyu 18:32kusan 32 M.
“Sai maigidan ya kira wannan bawa. Ya ce, ‘Kai mugun bawa, na yafe duk bashin da nake binka domin ka roƙe ni.
- Mattiyu 18:33kusan 32 M.
Ashe, bai kamata kai ma ka ji tausayin abokin bautarka yadda na yi maka ba?’
- Mattiyu 18:34kusan 32 M.
Cikin fushi, maigidan ya miƙa shi ga ma’aikatan kurkuku su gwada masa azaba, har yă biya dukan bashin da ake binsa.
- Mattiyu 18:35kusan 32 M.
“Haka Ubana da yake cikin sama zai yi da kowannenku, in ba ku yafe wa ’yan’uwanku daga zuciyarku ba.”
- Mattiyu 19:1kusan 33 M.
Sa’ad da Yesu ya gama faɗin waɗannan abubuwa, sai ya bar Galili, ya tafi yankin Yahudiya a ɗaya gefen Urdun.
- Mattiyu 19:2kusan 33 M.
Taron mutane mai yawa suka bi shi, ya kuwa warkar da su a can.
- Mattiyu 19:3kusan 33 M.
Waɗansu Farisiyawa suka zo wurinsa don su gwada shi. Suka yi tambaya suka ce, “Daidai ne mutum yă saki matarsa saboda wani dalili da kuma a kan kowane dalili?”
- Mattiyu 19:4kusan 33 M.
Ya amsa ya ce, “Ba ku taɓa karantawa ba ne cewa, a farkon halitta, Mahalicci ‘ya yi su namiji da ta mace,’
- Mattiyu 19:5kusan 33 M.
ya kuma ce, ‘Saboda wannan dalili, namiji zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa yă manne wa matarsa, biyun kuwa su zama jiki guda’?
- Mattiyu 19:6kusan 33 M.
Ta haka, ba sa ƙara zama biyu, sai dai ɗaya. Saboda haka abin da Allah ya haɗa fa, kada mutum yă raba.”
- Mattiyu 19:7kusan 33 M.
Suka yi tambaya, suka ce, “To, me ya sa Musa ya umarta cewa mutum yă ba wa matarsa takardar saki, yă kuma kore ta?”