Tsallake zuwa abun ciki

circa 6 BC – AD 30

The Life of Jesus

The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.

3,779 ayoyi · 4 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Mattiyu 16:23kusan 32 M.

    Yesu ya juya ya ce wa Bitrus, “Rabu da ni, Shaiɗan! Kai abin sa tuntuɓe ne a gare ni; ba ka tunanin al’amuran Allah, sai dai al’amuran mutane.”

  2. Mattiyu 16:24kusan 32 M.

    Sa’an nan Yesu ya ce wa almajiransa, “Duk mai son bina, dole yă ƙi kansa, yă ɗauki gicciyensa, yă bi ni.

  3. Mattiyu 16:25kusan 32 M.

    Gama duk mai son ceton ransa zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni, zai same shi.

  4. Mattiyu 16:26kusan 32 M.

    Me mutum zai amfana in ya sami duniya duka, amma ya rasa ransa? Ko kuwa me mutum zai bayar a bakin ransa?

  5. Mattiyu 16:27kusan 32 M.

    Gama Ɗan Mutum zai zo cikin ɗaukakar Ubansa, tare da mala’ikunsa, sa’an nan zai ba wa kowane mutum lada gwargwadon abin da ya yi.

  6. Mattiyu 16:28kusan 32 M.

    “Gaskiya nake gaya muku, akwai waɗansu da suke tsaitsaye a nan da ba za su mutu ba sai sun ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin mulkinsa.”

  7. Mattiyu 17:1kusan 32 M.

    Bayan kwana shida, sai Yesu ya ɗauki Bitrus, Yaƙub da Yohanna ɗan’uwan Yaƙub, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, su kaɗai.

  8. Mattiyu 17:2kusan 32 M.

    A can aka sāke kamanninsa a gabansu. Fuskarsa ta haskaka kamar rana, tufafinsa kuwa suka zama fari fat suna walƙiya.

  9. Mattiyu 17:3kusan 32 M.

    Nan take sai ga Musa da Iliya suka bayyana a gabansu, suna magana da Yesu.

  10. Mattiyu 17:4kusan 32 M.

    Sai Bitrus ya ce wa Yesu, “Ubangiji, ya yi kyau da muke nan. In kana so, sai in kafa bukkoki uku, ɗaya dominka, ɗaya domin Musa, ɗaya kuma domin Iliya.”

  11. Mattiyu 17:5kusan 32 M.

    Yayinda yake cikin magana, sai wani girgije mai haske ya rufe su, sai wata murya daga cikin girgijen ta ce, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna; wanda kuma nake jin daɗinsa ƙwarai. Ku saurare shi!”

  12. Mattiyu 17:6kusan 32 M.

    Sa’ad da almajiran suka ji haka, sai suka fāɗi ƙasa rubda ciki, a firgice.

  13. Mattiyu 17:7kusan 32 M.

    Amma Yesu ya zo ya taɓa su ya ce, “Ku tashi, kada ku ji tsoro.”

  14. Mattiyu 17:8kusan 32 M.

    Da suka ɗaga kai, ba su ga kowa ba sai Yesu kaɗai.

  15. Mattiyu 17:9kusan 32 M.

    Suna cikin gangarowa daga dutsen ke nan, sai Yesu ya umarce su cewa, “Kada ku faɗa wa kowa abin da kuka gani, sai bayan an tā da Ɗan Mutum daga matattu.”

  16. Mattiyu 17:10kusan 32 M.

    Almajiran suka tambaye shi suka ce, “To, me ya sa malaman dokoki suke cewa, dole sai Iliya ya fara zuwa?”

  17. Mattiyu 17:11kusan 32 M.

    Yesu ya amsa ya ce, “Tabbatacce, Iliya zai zo, zai kuma gyara dukan abubuwa.

  18. Mattiyu 17:12kusan 32 M.

    Amma ina faɗa muku, Iliya ya riga ya zo, ba su kuwa gane shi ba, amma suka yi masa duk abin da suka ga dama. Haka ma Ɗan Mutum zai sha wahala a hannunsu.”

  19. Mattiyu 17:13kusan 32 M.

    Sa’an nan almajiran suka gane cewa yana musu zancen Yohanna Mai Baftisma ne.

  20. Mattiyu 17:14kusan 32 M.

    Da suka isa wajen taron, sai wani mutum ya zo ya durƙusa a gabansa.

  21. Mattiyu 17:15kusan 32 M.

    Ya ce, “Ubangiji, ka yi wa ɗana jinƙai. Yana da farfaɗiya yana kuma shan wahala ƙwarai. Ya sha fāɗuwa cikin wuta ko ruwa.

  22. Mattiyu 17:16kusan 32 M.

    Na kuma kawo shi wurin almajiranka, amma ba su iya warkar da shi ba.”

  23. Mattiyu 17:17kusan 32 M.

    Yesu ya amsa ya ce, “Ya ku zamani marasa bangaskiya da kuma masu taurinkai, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe kuma zan yi haƙuri da ku? Kawo mini yaron a nan.”

  24. Mattiyu 17:18kusan 32 M.

    Yesu ya tsawata wa aljanin, ya kuwa rabu da yaron, nan take yaron ya warke.

  25. Mattiyu 17:19kusan 32 M.

    Sa’an nan almajiran suka zo wurin Yesu a ɓoye suka tambaye shi suka ce, “Me ya sa ba mu iya fitar da aljanin ba?”