circa 6 BC – AD 30
The Life of Jesus
The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Mattiyu 15:12kusan 32 M.
Sai almajiran suka zo wurinsa suka ce, “Ka san cewa Farisiyawa ba su ji daɗi sa’ad da suka ji wannan ba?”
- Mattiyu 15:13kusan 32 M.
Ya amsa ya ce, “Duk tsiron da Ubana na sama bai shuka ba, za a tumɓuke shi daga saiwoyi.
- Mattiyu 15:14kusan 32 M.
Ku ƙyale su, ai, makafin jagorai ne.In makaho ya yi wa makaho jagora, dukansu za su fāɗa a rami.”
- Mattiyu 15:15kusan 32 M.
Bitrus ya ce, “Ka bayyana mana wannan misali.”
- Mattiyu 15:16kusan 32 M.
Yesu ya tambaye su ya ce, “Har yanzu ba ku gane ba ne?
- Mattiyu 15:17kusan 32 M.
Ba ku gane cewa duk abin da ya shiga baki yakan wuce ciki ne daga nan kuma yă fita daga jiki ba?
- Mattiyu 15:18kusan 32 M.
Amma abubuwan da suke fitowa ta baki suna fitowa ne daga zuciya, su ne kuma suke ƙazantar da mutum.
- Mattiyu 15:19kusan 32 M.
Gama daga zuciya ne mugayen tunani, kisankai, zina, fasikanci, sata, shaidar ƙarya, ɓatan suna, suka fitowa.
- Mattiyu 15:20kusan 32 M.
Waɗannan su ne suke ƙazantar da mutum; amma cin abinci ba tare da wanke hannuwa ba, ba ya ƙazantar da mutum.”
- Mattiyu 15:21kusan 32 M.
Barin wurin ke nan, sai Yesu ya janye zuwa yankin Taya da Sidon.
- Mattiyu 15:22kusan 32 M.
Wata mutuniyar Kan’ana daga wajajen ta zo wurinsa, tana ihu tana cewa, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai! ’Yata tana shan wahala ƙwarai daga aljanin da yake cikinta.”
- Mattiyu 15:23kusan 32 M.
Yesu bai ce mata uffam ba. Saboda haka almajiransa suka zo wurinsa suka roƙe shi suka ce, “Ka kore ta tă tafi, tana ta binmu tana damunmu da ihu.”
- Mattiyu 15:24kusan 32 M.
Ya amsa ya ce, “An aiko ni wurin ɓatattun tumakin Isra’ila ne kaɗai.”
- Mattiyu 15:25kusan 32 M.
Sai macen ta zo ta durƙusa a gabansa ta ce, “Ubangiji, ka taimake ni!”
- Mattiyu 15:26kusan 32 M.
Ya amsa ya ce, “Ba daidai ba ne a ɗauki abincin yara a jefa wa karnukansu.”
- Mattiyu 15:27kusan 32 M.
Ta amsa, ta ce, “I, Ubangiji, amma karnuka ma sukan ci gutsattsarin da sukan fāɗi daga teburin maigidansu.”
- Mattiyu 15:28kusan 32 M.
Sa’an nan Yesu ya amsa ya ce, “Mace, kina da bangaskiya mai yawa! An biya miki bukatarki.” ’Yarta kuwa ta warke nan take.
- Mattiyu 15:29kusan 32 M.
Yesu ya tashi daga nan ya bi ta gefen Tekun Galili. Sa’an nan ya haura gefen wani dutse ya zauna.
- Mattiyu 15:30kusan 32 M.
Taron mutane mai girma kuwa suka zo wurinsa, suna kawo masa guragu, makafi, shanyayyu, kurame da dai waɗansu da yawa, suka kuwa kwantar da su a gabansa; ya kuma warkar da su.
- Mattiyu 15:31kusan 32 M.
Mutanen kuwa suka yi mamaki sa’ad da suka ga kurame suna magana, shanyayyu suna samun lafiya, guragu suna takawa, makafi kuma suna ganin gari. Sai suka yabi Allah na Isra’ila.
- Mattiyu 15:32kusan 32 M.
Yesu ya kira almajiransa wurinsa ya ce, “Ina jin tausayin mutanen nan; gama kwana uku ke nan suke tare da ni ba abin da za su ci. Ba na so in sallame su da yunwa, don kada su kāsa a hanya.”
- Mattiyu 15:33kusan 32 M.
Sai almajiransa suka amsa suka ce, “Ina za mu sami isashen burodi a wannan wurin da babu kowa mu ciyar da irin taron nan?”
- Mattiyu 15:34kusan 32 M.
Yesu ya tambaye su, “Burodi guda nawa kuke da shi?” Suka amsa suka ce, “Guda bakwai da ’yan ƙananan kifaye.”
- Mattiyu 15:35kusan 32 M.
Ya sa taron su zazzauna a ƙasa.
- Mattiyu 15:36kusan 32 M.
Sa’an nan ya ɗauki burodi guda bakwai da kuma kifayen nan, da ya yi godiya, sai ya kakkarya su ya ba wa almajiran, su kuma suka ba wa mutane.