circa 6 BC – AD 30
The Life of Jesus
The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Mattiyu 13:56kusan 31 M.
Duk ’yan’uwansa mata kuma ba tare da mu suke ba? To, a ina wannan mutum ya sami dukan waɗannan abubuwa?”
- Mattiyu 13:57kusan 31 M.
Sai suka ji haushinsa. Amma Yesu ya ce musu, “Sai a garinsa da kuma a gidansa na kaɗai annabi ba ya samun girma.”
- Mattiyu 13:58kusan 31 M.
Bai kuwa yi abubuwan banmamaki da yawa a can ba saboda rashin bangaskiyarsu.
- Mattiyu 14:1kusan 32 M.
A lokacin nan sarki Hiridus ya ji labarin Yesu,
- Mattiyu 14:2kusan 32 M.
sai ya ce wa fadawansa, “Wannan Yohanna Mai Baftisma ne; ya tashi daga matattu! Shi ya sa abubuwan banmamakin nan suke faruwa ta wurinsa.”
- Mattiyu 14:3kusan 32 M.
To, dā Hiridus ya kama Yohanna ya daure, ya kuma sa shi cikin kurkuku saboda Hiridiyas, matar ɗan’uwansa Filibus,
- Mattiyu 14:4kusan 32 M.
gama Yohanna ya dinga ce masa, “Ba daidai ba ne ka aure ta.”
- Mattiyu 14:5kusan 32 M.
Hiridus ya so yă kashe Yohanna, amma yana jin tsoron mutane, don sun ɗauka shi annabi ne.
- Mattiyu 14:6kusan 32 M.
A bikin tuna da ranar haihuwar Hiridus, diyar Hiridiyas ta yi musu rawa ta kuma gamsar da Hiridus ƙwarai,
- Mattiyu 14:7kusan 32 M.
har ya yi alkawari da rantsuwa cewa zai ba ta duk abin da ta roƙa.
- Mattiyu 14:8kusan 32 M.
Da mahaifiyarta ta zuga ta, sai ta ce, “Ba ni a cikin kwanon nan, kan Yohanna Mai Baftisma.”
- Mattiyu 14:9kusan 32 M.
Sarki ya yi baƙin ciki, amma saboda rantsuwarsa da kuma baƙinsa, sai ya ba da umarni a ba ta abin da ta roƙa
- Mattiyu 14:10kusan 32 M.
ya kuma sa aka yanke kan Yohanna a kurkuku.
- Mattiyu 14:11kusan 32 M.
Aka kawo kansa cikin kwano aka ba yarinyar, ita kuma ta kai wa mahaifiyarta.
- Mattiyu 14:12kusan 32 M.
Almajiran Yohanna suka zo suka ɗauki gawarsa suka binne. Sa’an nan suka je suka gaya wa Yesu.
- Mattiyu 14:13kusan 32 M.
Sa’ad da Yesu ya ji abin da ya faru, sai ya shiga jirgin ruwa ya janye shi kaɗai zuwa wani wuri inda ba kowa. Da jin haka, taron mutane suka bi shi da ƙafa daga garuruwa.
- Mattiyu 14:14kusan 32 M.
Da Yesu ya sauka ya kuma ga taro mai yawa, sai ya ji tausayinsu ya kuma warkar da marasa lafiyarsu.
- Mattiyu 14:15kusan 32 M.
Da yamma ta yi, sai almajiransa suka zo wurinsa suka ce, “Wurin nan fa ba kowa, ga shi kuma rana ta kusa fāɗuwa. Ka sallami taron don su shiga ƙauyuka su nemi wa kansu abinci.”
- Mattiyu 14:16kusan 32 M.
Yesu ya amsa, “Ba su bukata su tafi. Ku ku ba su wani abu su ci.”
- Mattiyu 14:17kusan 32 M.
Suka ce, “Burodi biyar da kifi biyu ne kawai muke da su a nan.”
- Mattiyu 14:18kusan 32 M.
Ya ce, “Ku kawo mini su a nan.”
- Mattiyu 14:19kusan 32 M.
Sai ya umarci mutanen su zazzauna a kan ciyawa. Da ya ɗauki burodi biyar da kifin biyun nan ya dubi sama, ya yi godiya ya kuma kakkarya burodin. Sa’an nan ya ba wa almajiransa, almajiran kuwa suka ba wa mutane.
- Mattiyu 14:20kusan 32 M.
Duk suka ci suka ƙoshi, almajiran kuwa suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna goma sha biyu.
- Mattiyu 14:21kusan 32 M.
Yawan waɗanda suka ci, sun yi wajen maza dubu biyar, ban da mata da yara.
- Mattiyu 14:22kusan 32 M.
Nan da nan Yesu ya sa almajiran su shiga jirgin ruwa su sha gabansa, su haye zuwa ɗayan hayin, yayinda shi kuma yă sallami taron.