Tsallake zuwa abun ciki

circa 6 BC – AD 30

The Life of Jesus

The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.

3,779 ayoyi · 4 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Mattiyu 13:31kusan 31 M.

    Ya ba su wani misali ya ce, “Mulkin sama yana kama da ƙwayar mustad, wadda mutum ya ɗauka ya shuka a gonarsa.

  2. Mattiyu 13:32kusan 31 M.

    Ko da yake ita ce mafi ƙanƙanta cikin ƙwayoyinku, duk da haka sa’ad da ta yi girma, takan zama mafi girma cikin tsire-tsiren lambu ta kuma zama itace, har tsuntsayen sararin sama su zo su yi sheƙa a rassansa.”

  3. Mattiyu 13:33kusan 31 M.

    Har yanzu ya ba su wani misali ya ce, “Mulkin sama yana kama da yisti wanda mace ta ɗauka ta kwaɓa garin alkama mai yawa, har sai da yistin ya gauraye yistin duka.”

  4. Mattiyu 13:34kusan 31 M.

    Yesu ya faɗa wa taron dukan waɗannan abubuwa cikin misalai; bai faɗa musu kome ba, sai tare da yin amfani da misalai.

  5. Mattiyu 13:35kusan 31 M.

    Ta haka aka cika abin da aka faɗa ta wurin annabi cewa, “Zan buɗe bakina da misalai, zan faɗi abubuwan da suke ɓoye tun halittar duniya.”

  6. Mattiyu 13:36kusan 31 M.

    Sa’an nan ya bar taron ya shiga gida. Almajiransa kuwa suka zo wurinsa suka ce, “Bayyana mana misalin ciyayin nan a gona.”

  7. Mattiyu 13:37kusan 31 M.

    Ya amsa ya ce, “Mai yafa irin mai kyan nan, shi ne Ɗan Mutum.

  8. Mattiyu 13:38kusan 31 M.

    Gonar kuwa ita ce duniya, irin nan mai kyau kuwa suna a matsayin ’ya’yan mulkin. Ciyayin nan kuma su ne ’ya’yan mugun nan,

  9. Mattiyu 13:39kusan 31 M.

    abokin gāban da yake shuka su kuwa, Iblis ne. Lokacin girbi kuma shi ne ƙarshen zamani, masu girbin kuwa su ne mala’iku.

  10. Mattiyu 13:40kusan 31 M.

    “Kamar yadda aka tattara ciyayin aka kuma ƙone a wuta, haka zai zama a ƙarshen zamani.

  11. Mattiyu 13:41kusan 31 M.

    Ɗan Mutum zai aiki mala’ikunsa, su kuwa cire daga mulkinsa kome da yake jawo zunubi da kuma duk masu aikata mugunta.

  12. Mattiyu 13:42kusan 31 M.

    Za su jefa su cikin wuta mai zafi, inda za a yi kuka da cizon haƙora.

  13. Mattiyu 13:43kusan 31 M.

    Sa’an nan masu adalci za su haskaka kamar rana a mulkin Ubansu. Duk mai kunnen ji, yă ji.”

  14. Mattiyu 13:44kusan 31 M.

    “Mulkin sama yana kama da dukiyar da aka ɓoye a gona. Da wani ya same ta, sai yă sāke ɓoye ta, sa’an nan cikin farin cikinsa yă je yă sayar da duk abin da yake da shi yă sayi gonar.

  15. Mattiyu 13:45kusan 31 M.

    “Har wa yau dai, mulkin sama yana kama da ɗan kasuwa mai neman lu’ulu’ai masu kyau.

  16. Mattiyu 13:46kusan 31 M.

    Da ya sami dutse guda mai daraja sosai, sai ya tafi ya sayar da dukan abin da yake da shi ya saye shi.

  17. Mattiyu 13:47kusan 31 M.

    “Har yanzu, mulkin sama yana kama da abin kamun kifin da aka jefa cikin tafki yă kamo kifi iri-iri.

  18. Mattiyu 13:48kusan 31 M.

    Da abin kamun kifi ya cika, masuntan suka jawo shi gaci. Sai suka zauna suka tattara kifi masu kyau a kwanduna, amma suka zubar da marasa kyau.

  19. Mattiyu 13:49kusan 31 M.

    Haka zai kasance a ƙarshen zamani. Mala’iku za su zo su ware masu mugunta daga masu adalci

  20. Mattiyu 13:50kusan 31 M.

    su kuma jefa su cikin wuta mai zafi, inda za a yi kuka da cizon haƙora.”

  21. Mattiyu 13:51kusan 31 M.

    Yesu ya tambaye su ya ce, “Kun gane dukan waɗannan abubuwa?” Suka amsa, “I.”

  22. Mattiyu 13:52kusan 31 M.

    Sa’an nan ya ce musu, “Saboda haka duk malamin dokokin da ya horu game da koyarwar mulkin sama, yana kama da maigida wanda yakan fitar daga ɗakin ajiyarsa sababbin dukiya da kuma tsofaffi.”

  23. Mattiyu 13:53kusan 31 M.

    Sa’ad da Yesu ya gama ba da waɗannan misalai, sai ya ci gaba daga can.

  24. Mattiyu 13:54kusan 31 M.

    Yana isowa garinsa, sai ya fara koya wa mutane a cikin majami’arsu, suka kuwa yi mamaki. Suka yi ta tambaya suna cewa, “Ina wannan mutum ya sami irin wannan hikima da kuma ayyukan banmamaki haka?

  25. Mattiyu 13:55kusan 31 M.

    Wannan ba shi ne ɗan kafinta nan ba? Ba mahaifiyarsa ba ce Maryamu, ’yan’uwansa kuma Yaƙub, Yusuf, Siman da Yahuda ba?