Tsallake zuwa abun ciki

circa 6 BC – AD 30

The Life of Jesus

The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.

3,779 ayoyi · 4 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Mattiyu 14:23kusan 32 M.

    Bayan ya sallame su, sai ya haura bisan gefen dutse shi kaɗai don yă yi addu’a. Da yamma ta yi, yana can shi kaɗai,

  2. Mattiyu 14:24kusan 32 M.

    jirgin ruwan kuwa ya riga ya yi nesa da gaci, yana fama da raƙuman ruwa domin iska tana gāba da shi.

  3. Mattiyu 14:25kusan 32 M.

    Wajen tsaro na huɗu na dare, sai Yesu ya nufe su, yana takawa a kan tafkin.

  4. Mattiyu 14:26kusan 32 M.

    Sa’ad da almajiran suka gan shi yana takawa a kan tafkin, sai tsoro ya kama su. Suka yi ihu don tsoro suka ce, “Fatalwa ce.”

  5. Mattiyu 14:27kusan 32 M.

    Amma nan da nan Yesu ya ce musu, “Ku yi ƙarfin hali! Ni ne. Kada ku ji tsoro.”

  6. Mattiyu 14:28kusan 32 M.

    Sai Bitrus ya amsa ya ce, “Ubangiji in kai ne ka ce mini in zo wurinka a kan ruwan.”

  7. Mattiyu 14:29kusan 32 M.

    Ya ce, “Zo.” Sai Bitrus ya fita daga jirgin ruwan, ya taka a kan ruwan ya nufe wajen Yesu.

  8. Mattiyu 14:30kusan 32 M.

    Amma da ya ga haukar iskar, sai ya ji tsoro, ya kuma fara nutsewa, sai ya yi ihu ya ce, “Ubangiji, ka cece ni!”

  9. Mattiyu 14:31kusan 32 M.

    Nan da nan Yesu ya miƙa hannu ya kamo shi ya ce, “Kai mai ƙarancin bangaskiya, don me ka yi shakka?”

  10. Mattiyu 14:32kusan 32 M.

    Da suka hau jirgin ruwan, sai iskar ta kwanta.

  11. Mattiyu 14:33kusan 32 M.

    Waɗanda suke cikin jirgin ruwan kuwa suka yi masa sujada, suna cewa, “Gaskiya kai Ɗan Allah ne.”

  12. Mattiyu 14:34kusan 32 M.

    Sa’ad da suka haye, sai suka sauka a Gennesaret.

  13. Mattiyu 14:35kusan 32 M.

    Da mutanen wurin suka gane da Yesu, sai suka kai labari a ko’ina a ƙauyukan da suke kewaye. Mutane suka kawo masa dukan marasa lafiyarsu

  14. Mattiyu 14:36kusan 32 M.

    suka kuwa roƙe shi yă bar marasa lafiya su taɓa ko da gefen rigarsa kawai, duk waɗanda suka taɓa shi kuwa suka warke.

  15. Mattiyu 15:1kusan 32 M.

    Sa’an nan waɗansu Farisiyawa da malaman dokoki suka zo wurin Yesu daga Urushalima suka yi tambaya suka ce,

  16. Mattiyu 15:2kusan 32 M.

    “Me ya sa almajiranka suke karya al’adun dattawa? Ba sa wanke hannuwansu kafin su ci abinci!”

  17. Mattiyu 15:3kusan 32 M.

    Yesu ya amsa ya ce, “Ku ma me ya sa kuke karya dokar Allah saboda al’adarku?

  18. Mattiyu 15:4kusan 32 M.

    Gama Allah ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,kuma duk wanda ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa dole a kashe shi.’

  19. Mattiyu 15:5kusan 32 M.

    Amma ku kukan ce, in wani ya ce wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa, ‘Duk taimakon da dā ya kamata za ku samu daga gare ni an ba wa Allah,’

  20. Mattiyu 15:6kusan 32 M.

    ba zai ‘girmama mahaifinsa’ da shi ba. Ta haka kun yi banza da maganar Allah saboda al’adarku.

  21. Mattiyu 15:7kusan 32 M.

    Ku munafukai! Daidai ne Ishaya ya yi annabci a kanku da ya ce,

  22. Mattiyu 15:8kusan 32 M.

    “ ‘Waɗannan mutane da baki kawai suke girmama ni, amma zukatansu suna nesa da ni.

  23. Mattiyu 15:9kusan 32 M.

    A banza suke mini sujada, koyarwarsu, dokoki ne kawai da mutane suke koyarwa.’ ”

  24. Mattiyu 15:10kusan 32 M.

    Sai Yesu ya kira taron wurinsa ya ce, “Ku saurara ku kuma gane.

  25. Mattiyu 15:11kusan 32 M.

    Abin da yake shiga bakin mutum ba ya ƙazantar da shi, sai dai abin da yake fitowa daga bakinsa, shi ne yake ƙazantar da shi.”