Tsallake zuwa abun ciki

circa 6 BC – AD 30

The Life of Jesus

The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.

3,779 ayoyi · 4 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Mattiyu 15:37kusan 32 M.

    Duk kuwa suka ci, suka ƙoshi. Daga baya almajiran suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna bakwai.

  2. Mattiyu 15:38kusan 32 M.

    Yawan waɗanda suka ci kuwa, maza dubu huɗu ne, ban da mata da yara.

  3. Mattiyu 15:39kusan 32 M.

    Bayan Yesu ya sallami taron, sai ya shiga jirgin ruwa ya tafi wajajen Magadan.

  4. Mattiyu 16:1kusan 32 M.

    Farisiyawa da Sadukiyawa suka zo don su gwada Yesu ta wurin neman yă nuna musu wata alama daga sama.

  5. Mattiyu 16:2kusan 32 M.

    Ya amsa ya ce,“Sa’ad da yamma ta yi, kukan ce, ‘Yanayi zai yi kyau, gama sararin sama ya yi ja,’

  6. Mattiyu 16:3kusan 32 M.

    da safe kuma, ku ce, ‘Yau kam za a yi hadari, gama sararin sama ya yi ja, ya kuma ɓata fuska.’ Kun san yadda za ku fassara yanayin sararin sama, amma ba kwa iya fassarar alamun lokuta.

  7. Mattiyu 16:4kusan 32 M.

    Wannan mugu da mazinacin zamani yana neman wani abin banmamaki, amma ba wata alamar da za a nuna wa wannan zamani sai dai ta Yunana.” Sai Yesu ya bar su ya tafi abinsa.

  8. Mattiyu 16:5kusan 32 M.

    Da suka ƙetare tafkin, almajiran sun manta su riƙe burodi.

  9. Mattiyu 16:6kusan 32 M.

    Yesu ya ce musu, “Ku yi hankali, ku yi taka zallan da yistin Farisiyawa da Sadukiyawa.”

  10. Mattiyu 16:7kusan 32 M.

    Sai suka fara tattaunawa da junansu suna cewa, “Ko don ba mu kawo burodi ba ne.”

  11. Mattiyu 16:8kusan 32 M.

    Sane da abin da suke zance, sai Yesu ya ce, “Ku masu ƙarancin bangaskiya, don me kuke magana da junanku a kan ba ku zo da burodi ba?

  12. Mattiyu 16:9kusan 32 M.

    Har yanzu ba ku gane ba ne? Ba ku tuna da gurasa biyar ɗin nan na mutum dubu biyar ba? Kwando nawa kuka tattara cike?

  13. Mattiyu 16:10kusan 32 M.

    Ko kuma burodi bakwai nan na mutum dubu huɗu, cikakku manyan kwanduna nawa kuka ɗauka?

  14. Mattiyu 16:11kusan 32 M.

    Yaya kuka kāsa gane cewa ba zancen burodi nake yi ba? Sai dai ku yi hankali da yistin Farisiyawa da Sadukiyawa.”

  15. Mattiyu 16:12kusan 32 M.

    Sa’an nan suka gane ba cewa yake musu su yi hankali da yistin da ake amfani da shi a burodi ba ne, sai dai su yi hankali da koyarwar Farisiyawa da Sadukiyawa ne.

  16. Mattiyu 16:13kusan 32 M.

    Sa’ad da Yesu ya zo yankin Kaisariya Filibbi, sai ya tambayi almajiransa ya ce, “Wa mutane suke ce da Ɗan Mutum?”

  17. Mattiyu 16:14kusan 32 M.

    Suka amsa, “Waɗansu suna ce Yohanna Mai Baftisma; waɗansu kuma suna ce annabi Iliya; har wa yau waɗansu suna ce Irmiya ne ko kuma ɗaya daga cikin annabawa.”

  18. Mattiyu 16:15kusan 32 M.

    Ya tambaye su, “Amma ku fa, wane ne ni a ganinku?”

  19. Mattiyu 16:16kusan 32 M.

    Siman Bitrus ya amsa ya ce, “Kai ne Kiristi, Ɗan Allah mai rai.”

  20. Mattiyu 16:17kusan 32 M.

    Yesu ya amsa ya ce, “Mai albarka ne kai Siman ɗan Yunana, gama ba mutum ne ya bayyana maka wannan ba, sai dai Ubana da yake cikin sama.

  21. Mattiyu 16:18kusan 32 M.

    Ina kuwa gaya maka, kai ne Bitrus,a kan wannan dutse zan gina ikkilisiyata, kuma ƙofofin Hadesba za su rinjaye ta ba.

  22. Mattiyu 16:19kusan 32 M.

    Zan ba ka mabuɗan mulkin sama; kome ka daure a duniya zai zama a daure a sama, kome kuma ka kunce a duniya zai zama a kunce a sama.”

  23. Mattiyu 16:20kusan 32 M.

    Sa’an nan ya gargaɗe almajiransa cewa kada su faɗa wa kowa shi ne Kiristi.

  24. Mattiyu 16:21kusan 32 M.

    Tun daga wannan lokaci Yesu ya fara bayyana wa almajiransa cewa dole yă tafi Urushalima yă sha wahaloli da yawa a hannun dattawa, manyan firistoci da kuma malaman dokoki, dole a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.

  25. Mattiyu 16:22kusan 32 M.

    Bitrus ya ja shi gefe ya fara tsawata masa yana cewa, “Sam, Ubangiji! Wannan ba zai taɓa faruwa da kai ba!”