- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 930–586 BC
The Divided Kingdom
The kingdom splits into Israel and Judah; prophets warn of judgment as both nations slowly drift into idolatry and exile.
Ayoyi daga wannan lokacin
Yowash ya aikata abin da yake daidai a idon Ubangiji domin Yehohiyada firist ya koya masa.
Amma fa ba a kawar da masujadan kan tuddai ba; mutane suka ci gaba da miƙa hadayu da kuma ƙona turare a kan tuddai.
- 2 Sarakuna 12:4kusan 856 K.H.
Yowash ya ce wa firistoci, “Ku tattara dukan kuɗin da ake kawo a matsayin hadayu masu tsarki na haikalin Ubangiji, kuɗin da aka tattara a ƙidaya, kuɗin da aka tattara daga wa’adin da mutum ya yi, da kuma kuɗin da aka kawo na yardan rai a haikali.
- 2 Sarakuna 12:5kusan 856 K.H.
Bari kowane firist yă karɓi kuɗi daga masu ajiya, sa’an nan a yi amfani da su a gyara duk wani abin da ya lalace a haikali.”
- 2 Sarakuna 12:6kusan 856 K.H.
Amma har zuwa shekara ta ashirin da uku ta mulkin Yowash, firistocin ba su yi gyara haikalin ba.
- 2 Sarakuna 12:7kusan 856 K.H.
Saboda haka Sarki Yowash ya kira Yehohiyada firist da sauran firistoci ya tambaye su ya ce, “Me ya sa ba kwa gyaran abubuwan da suka lalace a haikali? Kada ku sāke karɓan kuɗi daga masu ajiya, amma a miƙa su domin gyaran haikali.”
- 2 Sarakuna 12:8kusan 856 K.H.
Firistoci suka yarda cewa ba za su sāke karɓan kuɗi daga mutane ba, kuma ba za su yi gyaran haikalin da kansu ba.
- 2 Sarakuna 12:9kusan 856 K.H.
Yehohiyada firist ya ɗauki akwatin ya huda rami a murfinsa. Ya ajiye shi kusa da bagade a hannun dama na haikalin Ubangiji. Firistocin da suke tsaron ƙofar suka zuba dukan kuɗin da aka kawo a haikalin Ubangiji a cikin akwatin.
- 2 Sarakuna 12:10kusan 856 K.H.
Duk sa’ad da suka ga kuɗin sun ƙaru a akwatin, sai marubucin fada da babban firist, su ƙirga kuɗin da aka kawo a haikalin Ubangiji su sa a jakankuna.
- 2 Sarakuna 12:11kusan 856 K.H.
Sa’ad da suka ga kuɗin ya yi yawa, sai su ba wa waɗanda aka zaɓa su lura da aikin haikalin. Da shi suka biya waɗanda suka yi aiki a haikalin Ubangiji, su kafintoci, da magina,
- 2 Sarakuna 12:12kusan 856 K.H.
masu gini, da masu fasa duwatsu. Suka sayi katakai da sassaƙaƙƙun duwatsu domin gyaran haikalin Ubangiji, suka kuma biya duk waɗansu kuɗin gyaran haikalin.
- 2 Sarakuna 12:13kusan 856 K.H.
Ba a yi amfani da kuɗin da aka kawo a haikali don yin manyan kwanonin azurfa, lagwani, abin yayyafa ruwa, kakaki ko wani abu na zinariya, ko na azurfa domin haikalin Ubangiji ba;
- 2 Sarakuna 12:14kusan 856 K.H.
an ba ma’aikatan da suka gyara haikalin ne.
- 2 Sarakuna 12:15kusan 856 K.H.
Ba su bukaci wani bayani daga waɗanda aka ba wa kuɗin don su biya ma’aikatan ba, domin sun yi aikinsu da aminci.
- 2 Sarakuna 12:16kusan 856 K.H.
Ba a kawo kuɗi daga hadayun laifi da na hadayun zunubi a haikalin Ubangiji ba, waɗannan na firistoci ne.
- 2 Sarakuna 12:17kusan 840 K.H.
A wannan lokaci, Hazayel sarkin Aram ya haura, ya kai wa Gat hari, ya kuma ci ta da yaƙi. Sa’an nan ya juya don yă yaƙi Urushalima.
- 2 Sarakuna 12:18kusan 840 K.H.
Amma Yowash sarkin Yahuda ya kwashe tsarkakan kayan da kakanninsa, Yehoshafat, Yehoram da Ahaziya, sarakunan Yahuda suka keɓe, da kyautai da shi kansa ya keɓe, da kuma dukan azurfan da aka samu a ɗakunan ajiya haikalin Ubangiji da na fada, ya aika da su wa Hazayel sarkin Aram, shi kuma ya janye daga Urushalima.
- 2 Sarakuna 12:19kusan 840 K.H.
Game da sauran ayyukan mulkin Yowash da duk abin da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda.
- 2 Sarakuna 12:20kusan 840 K.H.
Hafsoshinsa suka yi masa maƙarƙashiya suka kashe shi a Bet Millo, a kan hanyar da ta gangara zuwa Silla.
- 2 Sarakuna 12:21kusan 840 K.H.
Hafsoshin da suka kashe shi kuwa su ne Yozabad ɗan Shimeyat da Yehozabad ɗan Shomer. Ya mutu, aka kuma binne shi tare da kakanninsa a Birnin Dawuda. Sai Amaziya ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
A shekara ta ashirin da uku ta Yowash ɗan Ahaziya, sarkin Yahuda, Yehoyahaz ɗan Yehu, ya zama sarkin Isra’ila a Samariya, ya kuwa yi mulki shekaru goma sha bakwai.
- 2 Sarakuna 13:2kusan 856 K.H.
Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji ta wurin bin zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila ta aikata, bai kuwa guje musu ba.
- 2 Sarakuna 13:3kusan 856 K.H.
Saboda haka fushin Ubangiji ya ƙuna a kan Isra’ila, kuma da daɗewa ya sa su a ƙarƙashin ikon Hazayel sarkin Aram da Ben-Hadad ɗansa.
- 2 Sarakuna 13:4kusan 856 K.H.
Sai Yehoyahaz ya nemi tagomashin Ubangiji, Ubangiji kuwa ya saurare shi, domin ya gan irin matsin da sarkin Aram yake yi wa Isra’ila.
- 2 Sarakuna 13:5kusan 856 K.H.
Sai Ubangiji ya tā da mai ceto wa Isra’ila, suka kuma kuɓuta daga ikon Aram. Ta haka Isra’ilawa suka yi zama a gidajensu yadda suka yi a dā.