- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 930–586 BC
The Divided Kingdom
The kingdom splits into Israel and Judah; prophets warn of judgment as both nations slowly drift into idolatry and exile.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 2 Sarakuna 10:34kusan 884 K.H.
Game da sauran ayyukan mulkin Yehu, da dukan abin da ya yi, a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.
- 2 Sarakuna 10:35kusan 856 K.H.
Yehu ya huta tare da kakanninsa, aka binne shi a Samariya. Yehoyahaz kuma ya ci sarauta bayansa.
- 2 Sarakuna 10:36kusan 856 K.H.
Yehu ya yi sarautar Isra’ila a Samariya shekara ashirin da takwas.
- 2 Sarakuna 11:1kusan 884 K.H.
Da Ataliya mahaifiyar Ahaziya ta ga ɗanta ya mutu, sai ta shiga hallaka dukan iyalin gidan sarauta.
- 2 Sarakuna 11:2kusan 884 K.H.
Amma Yehosheba, ’yar Sarki Yoram, ’yar’uwar Ahaziya, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya daga cikin ’ya’yan sarkin da ake shiri a kashe, ta ɓoye. Ta ɓoye shi daga Ataliya a wurin mai lura da shi a ɗakin kwana; don kada a kashe shi.
- 2 Sarakuna 11:3kusan 884 K.H.
Ya kasance a ɓoye, shi da mai lura da shi, a haikalin Ubangiji shekara shida yayinda Ataliya take mulkin ƙasar.
- 2 Sarakuna 11:4kusan 878 K.H.
A shekara ta bakwai sai Yehohiyada ya aika a kira komandodin sojoji ɗari-ɗari, da Keretawa, da matsara, ya sa aka kawo masa su a haikalin Ubangiji. Ya ƙulla yarjejjeniya da rantsuwa da su a haikalin Ubangiji, sa’an nan ya nuna musu ɗan sarki.
- 2 Sarakuna 11:5kusan 878 K.H.
Ya umarce su cewa, “Ga abin da za ku yi sa’ad da kuka zo aiki a Asabbaci, ku raba kanku kashi uku. Kashi ɗaya za su yi gadin gidan sarki,
- 2 Sarakuna 11:6kusan 878 K.H.
kashi ɗaya za su yi gadin Ƙofar Sur, kashi ɗaya kuma za su yi gadin ƙofar da take bayan ’yan gadin fada. Dukan waɗannan ƙungiyoyi uku za su yi gadin fadan,
- 2 Sarakuna 11:7kusan 878 K.H.
ku kuma da kuke a sauran ƙungiyoyi biyu da kun saba hutu a Asabbaci, duk za ku yi gadin haikali don sarki.
- 2 Sarakuna 11:8kusan 878 K.H.
Ku tsaya kewaye da sarki, kowane mutum da makaminsa a hannu. Duk wanda ya kusace ku, ku kashe shi. Ku manne wa sarki duk inda ya tafi.”
- 2 Sarakuna 11:9kusan 878 K.H.
Komandodin sojoji suka yi yadda Yehohiyada firist ya umarta. Kowa ya ɗauki mutanensa, waɗanda za su kama aiki Asabbaci da waɗanda za su kama hutun Asabbaci, suka zo wurin Yehohiyada firist.
- 2 Sarakuna 11:10kusan 878 K.H.
Sai ya ba komandodin māsu da garkuwoyi da dā suke na Dawuda, waɗanda suke a cikin haikalin Ubangiji.
- 2 Sarakuna 11:11kusan 878 K.H.
Matsaran kuma kowa da makaminsa a hannu, suka tsaya kewaye da sarki, kusa da bagade da kuma haikali, daga gefen kudu zuwa gefen arewa na haikalin.
- 2 Sarakuna 11:12kusan 878 K.H.
Sai Yehohiyada ya fito da ɗan sarki ya sa masa rawani a kā; ya ba shi shafin alkawari, ya kuma furta shi sarki. Suka shafe shi da mai, mutane kuma suka yi ta tafi suka ihu, suna cewa, “Ran sarki yă daɗe.”
- 2 Sarakuna 11:13kusan 878 K.H.
Sa’ad da Ataliya ta ji surutun matsara da na mutane, sai ta tafi wurin mutanen a haikalin Ubangiji.
- 2 Sarakuna 11:14kusan 878 K.H.
Da ta duba sai ga sarki, tsaye kusa da ginshiƙi, bisa ga al’ada. Hafsoshi da masu busa suna tsaye kusa da sarki, dukan mutanen ƙasar kuma suna farin ciki suna busa ƙahoni. Sai Ataliya ta keta tufafinta ta tā da murya tana cewa, “Kai! Wannan cin amana ne! Ai, wannan cin amana ne!”
- 2 Sarakuna 11:15kusan 878 K.H.
Yehohiyada ya umarci komandodin sojoji waɗanda suke lura da mayaƙa, ya ce, “Ku fitar da ita daga cikinku, ku kuma kashe duk wanda ya bi ta.” Gama firist ɗin ya ce, “Kada a kashe ta a cikin haikalin Ubangiji.”
- 2 Sarakuna 11:16kusan 878 K.H.
Saboda haka suka kama ta yayinda ta kai inda dawakai sukan shiga filin fada, a can kuwa aka kashe ta.
- 2 Sarakuna 11:17kusan 878 K.H.
Sa’an nan Yehohiyada ya yi alkawari tsakanin Ubangiji da sarki da kuma mutane cewa za su zama mutanen Ubangiji. Ya kuma yi alkawari tsakanin sarki da mutane.
- 2 Sarakuna 11:18kusan 878 K.H.
Sai dukan mutanen ƙasar suka tafi haikalin Ba’al suka rushe shi. Suka farfasa bagadai da kuma gumaka, suka kuma kashe Mattan wanda yake firist na Ba’al a gaban bagade. Sa’an nan Yehohiyada firist ya sa matsara a haikalin Ubangiji.
- 2 Sarakuna 11:19kusan 878 K.H.
Ya tafi tare da komandodin sojoji, Keretawa, matsara da kuma dukan mutanen ƙasar, tare kuwa suka kawo sarki daga haikalin Ubangiji zuwa cikin fada, ta ƙofar matsara. Sarki kuwa ya ɗauki mazauninsa a bisa kursiyin sarauta,
- 2 Sarakuna 11:20kusan 878 K.H.
dukan mutanen ƙasar suka yi murna. Birnin ya sami salama don an kashe Ataliya da takobi a fada.
- 2 Sarakuna 11:21kusan 878 K.H.
Yowash yana da shekara bakwai sa’ad da ya fara mulki.
A shekara ta bakwai ta Yehu, Yowash ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima na tsawon shekaru arba’in. Sunan mahaifiyarsa Zibiya ce; daga Beyersheba.