Tsallake zuwa abun ciki

circa 970–930 BC

Solomon & The Temple

Solomon builds the great Temple in Jerusalem and rules with unprecedented wisdom and wealth before foreign gods divide his heart.

635 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. 2 Tarihi 7:12kusan 1004 K.H.

    sai Ubangiji ya bayyana gare shi a daren ya ce, “Na ji addu’arka na kuma zaɓi wannan wuri don kaina, a matsayin haikali don hadayu.

  2. 2 Tarihi 7:13kusan 1004 K.H.

    “Sa’ad da na kulle sammai don kada a yi ruwan sama ko na umarci fāri su cinye amfanin ƙasar ko kuwa na aika da annoba a cikin mutanena,

  3. 2 Tarihi 7:14kusan 1004 K.H.

    in mutanena, waɗanda ake kira da sunana, sun ƙasƙantar da kansu, suka kuma yi addu’a, suka nemi fuskata, suka kuma juye daga mugayen hanyoyinsu, zan ji daga sama in kuma gafarta zunubinsu in kuwa warkar da ƙasarsu.

  4. 2 Tarihi 7:15kusan 1004 K.H.

    Yanzu, idanuna za su buɗu, kunnuwata kuma za su saurara ga addu’o’in da aka miƙa a wannan wuri.

  5. 2 Tarihi 7:16kusan 1004 K.H.

    Na zaɓi na kuma tsarkake wannan haikali saboda Sunana yă kasance a can har abada. Idanuna da kuma zuciyata kullum za su kasance a can.

  6. 2 Tarihi 7:17kusan 1004 K.H.

    “Game da kai kuwa, in ka yi tafiya a gabana kamar yadda Dawuda mahaifinka ya yi, ka kuma yi dukan abin da na umarta, ka kiyaye ƙa’idodina da dokokina,

  7. 2 Tarihi 7:18kusan 1004 K.H.

    zan kafa kujerar sarautarka, yadda na alkawarta wa Dawuda mahaifinka sa’ad da na ce, ‘Ba za ka taɓa rasa wani mutumin da zai yi mulki a bisa Isra’ila ba.’

  8. 2 Tarihi 7:19kusan 1004 K.H.

    “Amma in ka juya daga gare ni ka yashe ƙa’idodi da umarnan da na ba ka, ka yi gaban kanka don ka bauta wa waɗansu alloli ka kuma yi musu sujada,

  9. 2 Tarihi 7:20kusan 1004 K.H.

    zan tumɓuke Isra’ila daga ƙasata, wadda na ba su, zan kuma ƙi wannan haikalin da na tsarkake domin Sunana. Zan mai da shi abin karin magana da abin ba’a cikin dukan mutane.

  10. 2 Tarihi 7:21kusan 1004 K.H.

    Ko da yake wannan haikali yanzu mai girma ne, dukan wanda ya wuce zai kaɗa kai yă ce, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi irin wannan abu ga wannan ƙasa da kuma ga wannan haikali?’

  11. 2 Tarihi 7:22kusan 1004 K.H.

    Mutane za su amsa, ‘Domin sun yashe Ubangiji Allah na kakanninsu, wanda ya fitar da su daga Masar, suka rungumi waɗansu alloli, suna musu sujada, suna bauta musu, shi ya sa ya kawo dukan wannan masifa a kansu.’ ”

  12. 2 Tarihi 8:1kusan 1004 K.H.

    A ƙarshen shekaru ashirin, a lokacin da Solomon ya gina haikalin Ubangiji da nasa fadan,

  13. 2 Tarihi 8:2kusan 1004 K.H.

    Solomon ya sāke gina ƙauyukan da Hiram ya ba shi, ya kuma zaunar da Isra’ilawa a cikinsu.

  14. 2 Tarihi 8:3kusan 1004 K.H.

    Sa’an nan Solomon ya tafi Hamat-Zoba ya ci ta da yaƙi.

  15. 2 Tarihi 8:4kusan 1004 K.H.

    Ya kuma gina Tadmor a hamada da kuma dukan biranen ajiyar da ya gina a Hamat.

  16. 2 Tarihi 8:5kusan 1004 K.H.

    Ya sāke gina Bet-Horon na Bisa da kuma Bet-Horon na Ƙasa a matsayin birane masu katanga, da bangaye da ƙofofi da kuma ƙyamare,

  17. 2 Tarihi 8:6kusan 1004 K.H.

    haka kuma Ba’alat da dukan biranen ajiyarsa, da kuma dukan birane domin keken yaƙinsa da dawakansa, duk abin da ya so yă gina a Urushalima, a Lebanon da kuma dukan yankin da ya yi mulki, ya gina shi.

  18. 2 Tarihi 8:7kusan 1004 K.H.

    Dukan mutanen da suka rage daga Hittiyawa, Amoriyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa (waɗannan mutane ba Isra’ilawa ba ne),

  19. 2 Tarihi 8:8kusan 1004 K.H.

    wato, zuriyarsu da suka ragu a ƙasar, wadda Isra’ilawa ba su hallaka ba, waɗannan ne Solomon ya mai da su bayinsa na aikin dole, kamar yadda yake har wa yau.

  20. 2 Tarihi 8:9kusan 1004 K.H.

    Amma Solomon bai mai da Isra’ilawa bayi don aikinsa ba; su ne mayaƙansa, shugabannin hafsoshinsa, da shugabannin keken yaƙinsa da kuma mahayan keken yaƙinsa.

  21. 2 Tarihi 8:10kusan 1004 K.H.

    Su ne kuma manyan ma’aikatan Sarki Solomon, manyan mutane ɗari biyu da hamsin masu lura da mutane.

  22. 2 Tarihi 8:11kusan 1004 K.H.

    Solomon ya kawo ’yar Fir’auna daga Birnin Dawuda zuwa fadan da ya gina mata, gama ya ce, “Matata ba za tă zauna a fadan Dawuda sarkin Isra’ila ba, domin wuraren da akwatin alkawarin Ubangiji ya shiga masu tsarki ne.”

  23. 2 Tarihi 8:12kusan 1004 K.H.

    A kan bagaden Ubangiji da ya gina a gaban shirayi, Solomon ya miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji,

  24. 2 Tarihi 8:13kusan 1004 K.H.

    bisa ga bukace-bukace na kullum don hadayun da Musa ya umarta don Asabbatai, Sabon Wata da kuma bukukkuwa uku na shekara, Bikin Burodi Marar Yisti, Bikin Makoni da Bikin Tabanakul.

  25. 2 Tarihi 8:14kusan 1004 K.H.

    Bisa ga farillar mahaifinsa Dawuda, ya naɗa ɓangarori na firistoci don ayyukansu da Lawiyawa don su jagoranci yabo su kuma taimaki firistoci bisa ga bukace-bukacen kowace rana. Ya kuma naɗa matsara ƙofofi ɓangarori, ɓangarori don ƙofofi dabam-dabam domin abin da Dawuda mutumin Allah ya umarta ke nan.