Tsallake zuwa abun ciki

Jerusalem

753 verses · 2 known names

An kuma san shi da: Jerusalem's

31.7700, 35.2300 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Jerusalem

Tace bisa littafi
  1. A rana ta goma sha biyu ga watan farko, muka tashi daga bakin rafin Ahawa don mu tafi Urushalima. Alherin Allahnmu yana tare da mu, ya kuma kāre mu daga magabta da ’yan fashi.

  2. Muka iso Urushalima, inda muka huta kwana uku.

  3. Ko da yake mu bayi ne, Allahnmu bai yashe mu cikin daurin talala da muke ciki ba, ya sa sarakunan Farisa suka yi mana kirki. Ya ba mu sabuwar dama don mu sāke gina haikalin Allahnmu, mu kuma gyara katangar, ya kuma ba mu kāriya a Yahuda da Urushalima.

  4. Aka yi shela a duk fāɗin Yahuda da Urushalima cewa dukan waɗanda suka dawo daga bauta su tattaru a Urushalima.

  5. A cikin kwana uku duk mutanen Yahuda da na Benyamin suka taru a Urushalima. A ranar ashirin ga watan tara, dukan mutanen suka zauna a dandali a gaban gidan Allah cike da ɓacin rai saboda abin da ya faru da kuma ruwan da aka yi.

  6. Hanani, ɗaya daga cikin ’yan’uwana, ya zo daga Yahuda tare da waɗansu mutane. Na kuwa tambaye shi game da raguwar Yahudawan da suka tsira daga kwasan zuwa zaman bauta, da kuma game da Urushalima.

  7. Suka ce mini, “Waɗanda suka tsira daga kwasan zuwa zaman bauta da kuma suka komo cikin yankin suna cikin babban damuwa da wulaƙanci. An rushe katangar Urushalima aka kuma ƙone ƙofofin da wuta.”

  8. Sai na je Urushalima, bayan na zauna a can na kwanaki uku,

  9. sai na fita da dare tare da mutane kalila. Ban faɗa wa wani abin da Allahna ya sa a zuciyata in yi don Urushalima ba. Ba waɗansu dabbobi kuma tare da ni, sai dai dabbar da na hau.

  10. Da dare na fita ta Ƙofar Kwari wajen Rijiyar Dila da Ƙofar Juji, ina dudduba katangar Urushalima waɗanda aka rushe da kuma ƙofofinta waɗanda aka ƙone da wuta.

  11. Sai na ce musu, “Kun ga matsalar da muke ciki, yadda Urushalima ta zama kango, an kuma ƙone ƙofofinta da wuta. Ku zo mu sāke gina katangar Urushalima, ba za mu ƙara shan kunya ba.”

  12. Na amsa musu na ce, “Allah na sama zai ba mu nasara. Mu bayinsa za mu tashi mu fara gini, amma game da ku kam, ba ku da rabo cikin Urushalima, ba ku da wani hakki ko wani abin tunawa.”

  13. Uzziyel ɗan Harhahiya, ɗaya daga cikin masu ƙeran zinariya ne ya yi gyare-gyaren sashe na biye; sai Hananiya, ɗaya daga cikin masu yin turare, ya yi gyare-gyaren biye da wannan. Suka gyara Urushalima har zuwa Katanga Mai Faɗi.

  14. Refahiya ɗan Hur, mai mulkin rabin yankin Urushalima, ya yi gyare-gyaren sashe na biye.

  15. Shallum ɗan Hallohesh, mai mulkin ɗayan rabin yankin Urushalima ya yi gyare-gyaren sashe na biye tare da taimakon ’ya’yansa mata.

  16. Amma da Sanballat, da Tobiya, da Larabawa, da Ammonawa, da kuma mutanen Ashdod suka ji cewa gyare-gyaren katangar Urushalima yana cin gaba, ana kuma tattoshe wuraren da suka tsattsaga, sai suka husata ƙwarai.

  17. Dukansu suka ƙulla su zo, su yi yaƙi da Urushalima, su tā da hankali a cikinta.

  18. A wannan lokaci na kuma ce wa mutane, “A sa kowane mutum da mataimakinsa su zauna a Urushalima da dare, domin a yi tsaro da dare, da safe kuma a kama aiki.”

  19. har ma ka naɗa annabawa su yi wannan shela game da kai a Urushalima, su ce, ‘Akwai sarki a Yahuda!’ To, wannan rahoto zai koma wurin sarki; saboda haka ka zo, mu tattauna wannan batu.”

  20. Na sa ɗan’uwana Hanani tare da Hananiya shugaban fada aikin riƙon Urushalima, domin shi Hananiya mutum mai mutunci ne, mai tsoron Allah fiye da yawancin mutane.

  21. Na ce musu, “Kada a buɗe ƙofofin Urushalima da sassafe sai rana ta fito sosai. Yayinda matsaran ƙofofi suna aiki, a kulle ƙofofin a sa musu sakata kafin matsaran su tashi, wajen fāɗuwar rana. Ku kuma naɗa mazaunan Urushalima a matsayin masu tsaro, waɗansunsu a wuraren aiki, waɗansun kuma kusa da gidajensu.”

  22. Waɗannan su ne mutanen yankin da suka dawo daga zaman bautar da Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kame (sun dawo Urushalima da Yahuda, kowanne zuwa garinsa.

  23. kuma cewa ya kamata su yi shelar wannan magana, su kuma yaɗa ta a duk garuruwansu da kuma cikin Urushalima cewa, “Ku fita zuwa cikin ƙasar tudu ku kawo rassa daga itatuwan zaitun da na zaitun jeji, da kuma daga dargaza, da dabino da itatuwa masu ganye, don yin bukkoki”, kamar yadda yake a rubuce.

  24. To, fa, shugabannin mutane suka zauna a Urushalima, sauran mutanen kuma suka jefa ƙuri’a don su kawo mutum ɗaya daga kowane mutum goma don su zauna a Urushalima, birni mai tsarki, yayinda sauran tara suka zauna a garuruwansu.

  25. Sai mutane suka yaba wa dukan mutanen da suka ba da kansu da yardar rai su zauna a Urushalima.