Tsallake zuwa abun ciki

Jerusalem

753 verses · 2 known names

An kuma san shi da: Jerusalem's

31.7700, 35.2300 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Jerusalem

Tace bisa littafi
  1. Waɗannan su ne shugabannin yankuna waɗanda suka zauna a Urushalima (ko da yake waɗansu Isra’ilawa, da firistoci, da Lawiyawa, da ma’aikatan haikali, da zuriyar bayin Solomon, suka yi zama a cikin garuruwan Yahuda, kowanne a mallakarsa cikin garuruwa dabam-dabam,

  2. yayinda sauran mutane daga Yahuda da Benyamin suka zauna a Urushalima). Daga zuriyar Yahuda akwai, Atahiya ɗan Uzziya, ɗan Zakariya, ɗan Amariya, ɗan Shefatiya, ɗan Mahalalel, wani zuriyar Ferez;

  3. Zuriyar Ferez waɗanda suka zauna a Urushalima sun kai ɗari huɗu da sittin da takwas, dukansu kuwa muhimman mutane ne.

  4. Babban shugaban Lawiyawa a Urushalima shi ne Uzzi ɗan Bani, ɗan Hashabiya, ɗan Mattaniya, ɗan Mika. Uzzi yana ɗaya daga zuriyar Asaf, waɗanda suke mawaƙan da suke da nawayar hidima a gidan Allah.

  5. A keɓewar katangar Urushalima, an nemi Lawiyawa daga inda suke zama aka kawo su Urushalima don su yi bikin miƙawa da farin ciki da waƙoƙin godiya da kuma kiɗin kuge, garaya da molo.

  6. Aka kuma tattara mawaƙa su ma daga yankin kewayen Urushalima, daga ƙauyukan Netofawa,

  7. daga Bet-Gilgal, da kuma daga wuraren Geba da Azmawet, gama mawaƙan sun gina wa kansu ƙauyuka kewaye da Urushalima.

  8. A rana ta uku kuma suka miƙa manyan hadayu, suna farin ciki domin Allah ya ba su farin ciki mai girma. Mata da yara suka yi farin ciki su ma. An ji ƙarar farin ciki da ake yi a Urushalima daga nesa.

  9. Amma yayinda dukan wannan yake faruwa, ba ni a Urushalima, gama a shekara ta talatin da biyu na Artazerzes sarkin Babilon na dawo wurin sarki. A wani lokaci daga baya na nemi izininsa

  10. sai na koma zuwa Urushalima. A nan na ji game da mugun abin da Eliyashib ya aikata da ya tanada wa Tobiya ɗaki a filayen gidan Allah.

  11. A waɗannan kwanaki, na ga mutane a Yahuda suna matse ruwan inabi a ranar Asabbaci suna kuma kawo hatsi suna labta su a kan jakuna, tare da ruwan inabi, ’ya’yan inabi, ɓaure da kaya iri-iri. Suna kuma kawowa dukan wannan cikin Urushalima a ranar Asabbaci. Saboda haka na gargaɗe su a kan sayar da abinci a wannan rana.

  12. Mutane daga Taya waɗanda suke zama a Urushalima suna shigar da kifi da kaya iri-iri na ’yan kasuwa suna kuma sayar da su a Urushalima a ranar Asabbaci wa mutanen Yahuda.

  13. Sa’ad da inuwar yamma ya fāɗo a ƙofofin Urushalima kafin Asabbaci, na umarta a rufe ƙofofi kuma kada a buɗe sai Asabbaci ya wuce. Na kafa waɗansu mutanena a ƙofofin don kada a shigo da wani kaya a ranar Asabbaci.

  14. Sau ɗaya ko biyu, ’yan kasuwa da masu sayar da kowane irin kaya suka kwana waje da Urushalima.

  15. wanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya ɗauka tare ’yan zaman bauta cikin waɗanda ya ɗauko daga Urushalima, tare da Yekoniya, sarkin Yahuda.

  16. Cikin jin daɗinka ka sa Sihiyona ta yi nasara; ka gina katangar Urushalima.

  17. Saboda haikalinka a Urushalima sarakuna za su kawo maka kyautai.

  18. Zabura ta Asaf. Ya Allah, al’ummai sun mamaye gādonka; sun ƙazantar da haikalinka mai tsarki, sun bar Urushalima kufai.

  19. Sun zubar da jini kamar ruwa ko’ina a Urushalima, kuma babu wani da zai binne matattu.

  20. Saboda haka za a furta sunan Ubangiji a Sihiyona yabonsa kuma a Urushalima

  21. a filayen gidan Ubangiji, a tsakiyarki, ya Urushalima. Yabi Ubangiji.

  22. Ƙafafunmu suna tsaye a ƙofofinki, ya Urushalima.

  23. An gina Urushalima kamar birnin da aka yi a harhaɗe wuri guda.

  24. Ku yi addu’a don salamar Urushalima, “Bari waɗanda suke ƙaunarki su zauna lafiya.

  25. Kamar duwatsun da sun kewaye Urushalima, haka Ubangiji ya kewaye mutanensa yanzu da har abada kuma.