Tsallake zuwa abun ciki

Joseph

199 ayoyi · 17 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Joseph

Tace bisa littafi
  1. Sa’ad da kwanakin makoki suka wuce, sai Yusuf ya ce wa iyalin gidan Fir’auna, “In na sami tagomashi a idanunku, ku yi magana da Fir’auna domina. Ku faɗa masa,

  2. Saboda haka Yusuf ya haura don yă binne mahaifinsa. Dukan hafsoshin Fir’auna suka yi masa rakiya tare da manyan mutanen gidan Fir’auna, da kuma dukan manyan mutanen Masar

  3. da kuma dukan membobin gidan Yusuf, da ’yan’uwansa da kuma waɗanda suke na gidan mahaifinsa. Yara kaɗai da garkunansu da kuma shanunsu ne aka bari a Goshen.

  4. Bayan ya binne mahaifinsa, sai Yusuf ya koma Masar, tare da ’yan’uwansa da kuma dukan waɗanda suka tafi tare da shi don binne mahaifinsa.

  5. Sa’ad da ’yan’uwan Yusuf suka ga cewa mahaifinsu ya mutu, sai suka ce, “Mai yiwuwa Yusuf yana riƙe da mu a zuciya, wataƙila zai rama dukan abubuwa marasa kyau da muka yi masa?”

  6. Saboda haka suka aika wa Yusuf suna cewa, “Mahaifinka ya bar waɗannan umarnai kafin yă rasu.

  7. Ga abin da za ku ce wa Yusuf, ‘Na roƙe ka, ka gafarta wa ’yan’uwanka zunubai da laifofin da suka aikata na abubuwa marasa kyau da suka yi maka.’ Yanzu muna roƙonka ka gafarta zunuban bayin Allah na mahaifinka.” Sa’ad da saƙonsu ya zo masa, sai Yusuf ya yi kuka.

  8. Amma Yusuf ya ce musu, “Kada ku ji tsoro. Ni Allah ne?

  9. Yusuf ya zauna a Masar tare da dukan iyalin mahaifinsa. Ya rayu shekara ɗari da goma.

  10. Ya kuma ga tsara ta uku ta ’ya’yan Efraim. Haka ma ’ya’yan Makir ɗan Manasse, an haife su aka sa a gwiwoyin Yusuf.

  11. Sai Yusuf ya ce wa ’yan’uwansa, “Ina gab da mutuwa. Amma tabbatacce Allah zai taimake ku, yă fid da ku daga wannan ƙasa zuwa ƙasar da ya alkawarta da rantsuwa wa Ibrahim, Ishaku da kuma Yaƙub.”

  12. Yusuf kuwa ya sa ’ya’yan Isra’ila maza suka yi rantsuwa, ya kuma ce, “Tabbatacce Allah zai taimake ku, ku kuma dole ku ɗauki ƙasusuwana, ku haura da su daga wannan wuri.”

  13. Yusuf kuwa ya rasu yana da shekara ɗari da goma. Bayan an shafe shi da maganin hana ruɓa, sai aka sa shi a akwatin gawa a Masar.

  14. Zuriyar Yaƙub duka sun kai mutum saba’in. Yusuf ya riga ya kasance a Masar.

  15. Yanzu Yusuf da dukan ’yan’uwansa da kuma dukan tsaran nan da suka tafi Masar, sun mutu,

  16. Sai wani sabon sarki wanda bai san Yusuf ba, ya hau sarautar Masar.

  17. Musa ya ɗauki ƙasusuwan Yusuf tare da shi, gama Yusuf ya sa Isra’ilawa su rantse masa. Ya ce, “Tabbatacce Allah zai taimake ku, sai ku ɗibi ƙasusuwana tare da ku daga wannan wuri.”

  18. daga kabilar ’ya’yan Yusuf, daga Efraim, Elishama ɗan Ammihud; daga Manasse, Gamaliyel ɗan Fedazur;

  19. Daga ’ya’yan Yusuf. Daga zuriyar Efraim. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.

  20. Gaddi ɗan Susi, daga kabilar Manasse (wata kabilar Yusuf);

  21. Zuriyar Yusuf bisa ga kabilansu ta wurin Manasse da Efraim.

  22. Waɗannan su ne kabilan Efraim; jimillarsu ta kai 32,500. Waɗannan su ne kabilan Yusuf ta wurin kabilansu.

  23. ’Ya’yan nan mata na Zelofehad, ɗan Hefer, ɗan Gileyad, ɗan Makir, ɗan Manasse, suna cikin kabilan Manasse ɗan Yusuf, suka tafi ƙofar shiga Tentin Sujada. Sunayensu kuwa su ne Mala, Nowa, Hogla, Milka da kuma Tirza.

  24. Sai Musa ya ba wa mutanen Gad, mutanen Ruben, da rabin mutanen Manasse ɗan Yusuf, masarautar Sihon, sarkin Amoriyawa, da masarautar Og na Bashan, dukan ƙasar, tare da biranenta da kuma yankunan da suke kewaye.

  25. Hanniyel ɗan Efod, shugaba daga kabilar Manasse ɗan Yusuf;