Tsallake zuwa abun ciki

Joseph

199 ayoyi · 17 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Joseph

Tace bisa littafi
  1. A iyakokin Manasse akwai Bet-Sheyan, Ta’anak, Megiddo da Dor, tare da ƙauyukansu. Zuriyar Yusuf ɗan Isra’ila ta zauna a waɗannan garuruwa.

  2. Da hannunka mai ƙarfi ka fanshi mutanenka, zuriyar Yaƙub da Yusuf. Sela

  3. Sa’an nan ya ƙi tentunan Yusuf, bai zaɓi kabilar Efraim ba;

  4. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Mai muryar “Lilin Alkawari.” Na Asaf. Zabura ce. Ka ji mu, ya Makiyayin Isra’ila, kai da ka bishe Yusuf kamar garke. Kai da kake zaune a kursiyi tsakanin kerubobi, ka haskaka

  5. Ya kafa shi a matsayin ƙa’ida domin Yusuf sa’ad da ya fito daga Masar. Muka ji yaren da ba mu fahimta ba.

  6. ya kuma aiki mutum a gabansu, Yusuf, da aka sayar a matsayin bawa.

  7. “Ɗan mutum, ka ɗauki sanda ka rubuta a kansa, ‘Na Yahuda da Isra’ilawan da suke tare da shi.’ Sa’an nan ka ɗauki wani sanda, ka rubuta a kansa, ‘Sandan Efraim, na Yusuf da dukan gidan Isra’ilan da suke tare da shi.’

  8. Ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, Zan ɗauki sandan Yusuf, wanda yake a hannun Efraim, da na kabilan Isra’ilawan da suke tare da shi, in haɗa shi da sandan Yahuda, in mai da su sanda guda, za su kuwa zama ɗaya a hannuna.’

  9. Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “Waɗannan su ne iyakokin da za ku raba ƙasar gādo cikin kabilan Isra’ila goma sha biyu, da rabo biyu don Yusuf.

  10. A gefen gabas, wanda yake da tsawon kamu 4,500 zai kasance da ƙofofi uku, ƙofar Yusuf, ƙofar Benyamin da ƙofar Dan.

  11. Ku nemi Ubangiji ku kuma rayu, ko kuwa zai ratsa yă share gidan Yusuf kamar wuta; zai cinye Betel kuwa ba zai sami wanda zai kashe ta ba.

  12. Ku ƙi mugunta, ku ƙaunaci nagarta; ku dinga yin shari’ar gaskiya a ɗakunan shari’a. Mai yiwuwa Ubangiji Allah Maɗaukaki zai ji tausayin raguwar Yusuf.

  13. Da manyan kwanoni kuke shan ruwan inabi kuna kuma shafa mai mafi kyau, amma ba kwa baƙin ciki game da kangon da Yusuf ya zama.

  14. Gidan Yaƙub zai zama kamar wuta, gidan Yusuf kuma kamar harshen wuta; gidan Isuwa zai zama kamar tattaka, za a kuma sa masa wuta yă ƙone. Babu wanda zai tsira daga gidan Isuwa.” Ni Ubangiji na faɗa.

  15. “Zan ƙarfafa gidan Yahuda in kuma ceci gidan Yusuf. Zan maido da su domin ina jin tausayinsu. Za su zama kamar ban taɓa ƙinsu ba, gama ni ne Ubangiji Allahnsu zan kuma amsa musu.

  16. Duk suka yabe shi, suka yi mamakin kalmomin alheri da suke fitowa daga bakinsa. Suka yi tambaya, suna cewa, “Anya, wannan ba ɗan Yusuf ba ne?”

  17. Sai ya zo wani gari a Samariya da ake ce da shi Saikar, kurkusa da filin da Yaƙub ya ba wa ɗansa Yusuf.

  18. “Domin kakanninmu sun ji kishin Yusuf, sai suka sayar da shi bawa zuwa Masar. Amma Allah ya kasance tare da shi

  19. A ziyararsu ta biyu, Yusuf ya faɗa wa ’yan’uwansa wane ne shi, Fir’auna kuwa ya sami sani game da iyalin Yusuf.

  20. Bayan wannan, Yusuf ya aika a zo da mahaifinsa Yaƙub da dukan iyalinsa, gaba ɗaya dai mutum saba’in da biyar ne.

  21. Sa’an nan wani sarki, wanda bai san kome game da Yusuf ba, ya zama mai mulkin Masar.

  22. Ta wurin bangaskiya ne Yaƙub, sa’ad da yake bakin mutuwa, ya albarkaci kowane ɗan Yusuf, ya kuma yi sujada yayinda yake jingine a kan sandansa.

  23. Ta wurin bangaskiya ne Yusuf, sa’ad da kwanakinsa suka yi kusan ƙarewa, ya yi magana game da fitowar Isra’ilawa daga Masar ya kuma ba da umarni game da ƙasusuwansa.

  24. daga kabilar Zebulun mutum 12,000, daga kabilar Yusuf mutum 12,000, daga kabilar Benyamin mutum 12,000.